Matar da ta cillo 'yarta daga saman benen da ya kama da wuta
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wata mata a birnin Durban na Afirka Ta Kudu ta cillo 'yarta daga saman bene bayan an cinna wa benen wuta yayin zanga-zanga ranar Talata.
Ana zargin masu zanga-zanga da wawason kayan shaguna ne suka kunna wa benen wuta.
Mutane da dama ne suka mutu a kasar, yayin da aka kama daruruwan masu zanga-zanga, bayan daurin da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma makon jiya.