Jelani Aliyu ya kaddamar da tashar cajin mota mai amfani da hasken rana a Lagos

Bayanan bidiyo, Jelani Aliyu ya kaddamar da tashar cajin mota mai amfani da hasken rana a Lagos

Shugaban hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya wato NADDC, Jelani Aliyu, ya kaddamar da tashar cajin mota wacce take amfani da hasken rana.

An bude tashar ne a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin kasar ranar Talata.

An kaddamar da tashar ne da zummar rage amfani da fetur, wanda bisa al'ada yake gurbata muhalli.