Abin da ya kamata ku sani game da mota mai tashi sama

Bayanan bidiyo, Abin da ya kamata ku sani game da mota mai tashi sama

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wata motar da ake gwajinta ta kammala tafiyarta ta minti 35 a sama tsakanin filin jirgin saman Nitra da Bratislava, da ke Slovakia.

Motar mai tashi sama, wadda ake kira AirCar, tana dauke da injin BMW sannan tana amfani da fetur.

Mutumin da ya kirkiro ta, Farfesa Stefan Klein, ya ce za ta iya tafiyar kilomita 1,000 (600 miles), da nisan kafa 8,200 (2,500m) a sararin samaniya. Kuma tana daukar minti biyu da dakika 15 ta sauya daga mota zuwa jirgin sama.