Bidiyon yadda aka gurfanar da shugaban IPOB Nnamdi Kanu a kotu

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda aka gurfanar da shugaban IPOB Nnamdi Kanu a kotu

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa an kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da ke son ballewa daga kasar.

Ministan Shari'ar kasar kuma Antoni Janar Abubakar Malami ne ya tabbatar da kama Mr Kanu a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata.

Malami ya kara da cewa an kama shugaban IPOB ne ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman ballewa daga Najeriya.