Intanet ta durkisar da sana'ata ta sayar da jarida tsawon shekara 51 - Malam Bawa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Malam Bawa wani mutum ne da yake sayar da jaridu a Zaria, a jihar Kadunan Najeriya.
A lokacin da ya cika shekara 51 yana sana'ar, ya shaida wa BBC cewa a yanzu yaduwar intanet ta sa ciniki ba ya tafiya sosai a sana'ar.
"Tun lokacin yakin basasar Najeriya a 1970 nake sana'ar nan kuma ta rufa min asiri sosai, amma a yanzu da kyar nake samun abin da zan ciyar da iyali," in ji shi.
Ga dai cikakkiyar hirarsa a wannan bidiyon.