Isma'ila Na'abba Afakallah: Abin da ya sa muka kama mutumin da ake zargi ya yi ridda a Kano

Bayanan bidiyo, 'Abin da ya sa muka kama mutumin da ake zargi ya yi ridda a Kano'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Isma'ila Na'abba Afakalla, ya ce sun kama mutumin da ake zargi da yin kalaman batanci ga Allah (SWT) a cikin wakarsa ne domin hakan ya zama izina ga wasu mutanen.

Ya shaida wa BBC Hausa cewa kamun da aka yi Ahmad Abdul, mai shekara 35, bayan ya fitar da wakar ba tare da hukumar tace fina-finai da dab'i ta Jihar Kano ta tantance ta ba, shi ne mafi alheri.

Ya kara da cewa sun yi hakan ne domin gudun tayar da tarzoma, yana mai cewa mawakin ya nemi afuwa kan kuskuren da ya yi.