Bidiyo: Wadanne labaran karya ake yadawa kan rufe Twitter a Najeriya?

Bayanan bidiyo, Wadanne labaran karya ake yadawa kan rufe Twitter a Najeriya?

Ku latsa hoton d ake sama don kallon bidiyon:

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da amfani da shafin Twitter a ƙasar a makon da ya gabata, ƴan ƙasar ke ta tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.

Haka ma jami'an diflomasiyya da gwamnatocin wasu ƙasashen da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.

Gwamnatin Najeriyar dai ta dakatar da amfani da shafin ne kan abin da ta ce "amfani da shafin wajen gudanar da ayyukan da ka iya yi raba kawunan ƴan ƙasar", kamar yadda sanarwar da ta fitar ta ce.

Kuma dama a makon da ya gabatan dai, shafin Twitter ɗin ya cire wani saƙo da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa inda ya ja kunnen ƴan IPOB masu ƙoƙarin ɓallewa daga Najeriya kan hare-haren da suke kaiwa a Kudu maso gabashin ƙasar.

Twitter ta ce saƙonnin nasa sun saɓa wa dokokinta.

Sai dai wani abu da ya biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da Twitter su ne labaran ƙarya da ake ta ci gaba da yaɗawa a wasu shafukan sada zumunta musamman Whatsapp da Facebook.

Ga dai Madina Maishanu da nazari kan batun.