Bidiyon hira da Suhaila ƴar Sheikh Ibrahim Zakzaky

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Ina cikin ƙuncin tsare mahaifana har kwana 2,000 - Suhaila Zakzaky

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A wata hira da BBC Hausa Suhaila Ibrahim ta ce ba su da wani buri da ya wuce su ga an saki mahaifansu sun sake rayuwa da su.

A ranar Alhamis 3 ga watan Yunin 2021 ne Malam Ibrahim ya cika kwana 2,000 a hannun gwmanatin Najeriya, tun bayan kama shi da aka yi tare da matarsa a Disamban 2015 a gidansa da ke Zaria.

Tun daga wancan lokacin mabiyansa suke ta kira ga gwamnati da ta sake shi, musamman bayan bayar da belinsa da kotu ta yi.