Berekete Family: Binciken Africa Eye kan shirin da ke ƙwato wa ƴan Najeriya ƴanci
Shirin binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya yi duban tsanaki kan shirin Berekete Family na gidan radiyon Human Rights, inda ya gano irin taimakon da shirin yake yi wa jama'a yayin da kuma yake jefa wasu cikin tasku.