Musulman da ke yi wa gawarwaki gata a Senegal
A kasar Senegal, duk shekara mutane na mutuwa sanadin hatsari ko kuma wasu dalilai na daban kuma ba a sanin mutanen ko kuma iyalai bas a zuwa domin karbar gawargwakin ‘yan uwansu.
Wata kungiyar Musulmai da ke aiki domin samun lada daga ubangiji tana daukar nauyin yi wa gawarwakin sutura kamar yadda Musulunci ya tanada.