BBC Africa Eye: Binciken BBC ya bankaɗo yadda ake ci da gumin dattijai ƴan fansho a Najeriya
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya tona asirin yadda rashawa ta yi katutu a tsarin fansho a Najeriya, wanda ya jefa rayuwar tsofaffi cikin ƙunci na rashin lafiya da rashin kudi, amma kuma ana ware wa wasu ƴan siyasar ƙasar kaso mai tsoka na kuɗaɗen ritaya.
Wakiliyar BBC Yemisi Adagoke ta yi tattaki zuwa jihar Kuros Riba inda ta gano waɗanda suka yi ritaya - tsofaffi wadanda jihar ta ayyana cewa sun mutu kuma an hana su fansho.
Wasu an tilasta musu dogaro da tallafin kudi daga danginsu kuma jami’an gwamnatin jihar suna yi musu wulakanci saboda sun gabatar da koken neman a biyu su haƙƙinsu na fansho.