Muhimmancin ciyarwa da sada zumunta a watan Ramadan

Bayanan bidiyo, Dr Mustapha Sidi

Latsa alamar hoton da ke sama domin sauraro da kallon Dr Sidi

Dr Mustapha Sidi ya ce ciyarwa a watan Ramadan na daya daga cikin manyan ayyukan da ke kara yawan ladan mai azumi a watan Ramadan.

"Allah Ubangiji ya ce ku tausayawa na kasanku sai na sama ya tausaya muku."

Ya kara da cewa "ba karfi ba ne ke bayar da arziki ba. Allah zai iya karbe baiwar da ya yi ma ya mayar da ita ga wani."

Dangane kuma da zumunci, Dr Sidi ya bukaci Musulmi da su sada zumunci musamman ga 'yan uwansu na jini.

"Ta hakan ne kawai za mu fahimci irin yanayin neman taimako da 'yan uwanmu ke bukata musamman mata."