John Magufuli: Waiwaye kan rayuwar marigayi shugaban Tanzania

Bayanan bidiyo, Bidiyon Waiwaye kan rayuwar marigayi shugaban Tanzania John Magufuli

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

John Pombe Magufuli wanda ɗa ne ga wani tsohon manomi, ya zama shugaban ƙasar Tanazaniya a ranar da ya cika shekara 56 a duniya a shekarar 2015, sannan ya zamo ɗaya daga cikin shugabanni masu jawo ce-ce-ku-ce.

Kafin ya zama shugaban ƙasa ana yi masa laƙabi da bulldozer saboda jagorantar wani shiri na gina tituna a matsayinsa na ministan ayyuka, sannan daga baya an yi ta yabonsa kan tsayin dakan da ya yi wajen daƙile cin hanci da kuma yadda ya ƙi jinin ganin ana almubazzaranci da kuɗi.

Ga dai waiwaye kan wasu abubuwa da suka danganci rayuwarsa.

Amma an sha sukarsa kan wasu abubuwa da ya aiwatar a lokacin da yake kan mulki, inda masu suka suka ce yana yi wa ƴancin albarkacin baki da kuma harkokin kasuwanci barazana.