Tagwayen Asali: Tagwayen da ke amfani da waya ɗaya kuma suke son auren tagwaye
Ku latsa hoton sama ku kalli Tagwayen Asali:
Wasu tagwaye mawaƙa da ake kira Tagwayen Asali sun bayyana wa BBC cewa waya ɗaya suke amfani da ita saboda tsabar shaƙuwa.
"Ai duk wanda ya kira waya cewa yake zai yi magana da tagwayen asali ba guda ɗaya ba, saboda haka ba ma raba waya, da guda ɗaya muke amfani," a cewarsu.
Tagwayen sun ce burinsu shi ne su auri Hasana da Husaina kamarsu kuma sun bayyana dalilansu game da hakan.