An sauya wa wani gida mai shekara 139 matsuguni a Amurka
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mazauna birnin San Francisco na Amurka sun ga abin al'ajabi na yadda aka sauya wa wani gida da ya yi shekara 139 matsuguni ta hanyar jan sa a kan titi.
Tsohon matsugunin da gidan yake za a gina rukunin gidaje 48 a gini mai hawa takwas ne.
Mamallakin gidan ya kashe kuɗi kusan dala dubu 200 don samun izini da kuma wajen ɗauke gidan.