An yi sabuwar waƙa da muryar mawaƙin da ya shekara 25 da mutuwa

Bayanan bidiyo, An yi sabuwar waƙa da muryar mawaƙin da ya shekara 25 da mutuwa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani kamfanin fasaha na Koriya Ta Kudu ya ƙirƙiri muryar mawaƙi Kim Kwang-seok da manhajar ƙirƙirar basira ta Artificial Intelligence.

Waɗanda suka shirya waƙar sun yi amfani da tsofaffin waƙoƙin Kim ne da kuma muryarsa da yake magana ta hanyar koya wa manhajar AI yadda za ta kwaikwayi yanayi da shauƙinb da Kim yake shiga idan yana waƙa.

Daga nan sai manhajar ta yi wata sabuwar waƙa da muryar Kim wacce bai taɓa yin irin ta ba a lokacin da yake raye.