Haruna Chizo: Bahaushe dan ci ranin da ya shahara a Jamus

Bayanan bidiyo, Haruna Chizo

Latsa wannan hoton da ke sama domin shan kallon labarin Haruna Chizo:

Wataƙila idan kuka ji ana batun cirani, abin da zai fara zuwa ranku shi ne shiga duniya ba tare da samun nasara ba.

Sai dai wannan tunanin ya saɓa da alherin da Haruna Chizo ya gamu da shi a yawon cirani a ƙasar Jamus.

Chizo wanda fitaccen mawaƙi ne kuma mai barƙwanci na Hausa, ya samu ɗaukaka da yin fice a Jamus, inda saboda tsabar jin daɗin zamansa har Bajamushiya ya aura.

Amma duk da wannan nasara da Haruna ya samu, matashin ya sha baƙar wahala kafin ya isa Turai.

Mai daukar hoto: Abdulsalam Usman

Mai rahoto: Salihu Adamu Usman