Bidiyon labaran mazan da aka yi wa fyaɗe a Afirka

Bayanan bidiyo, Bidiyon labaran mazan da aka yi wa fyaɗe a Afirka

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tattauna batun yi wa maza fyaɗe abin kunya ne a sassan duniya daban-daban da suka haɗa da Afirka, inda ake nuna ƙyama sosai ga waɗanda abin ya shafa.

A taƙaice ma mutane da dama na zaton cewa ba za a iya yi wa namiji fyaɗe ba.

Amma a yanzu mazan da aka yi wa fyaɗe a Afirka kan fito su bayar da labarinsu da taimakon junansu da kuma shaida wa al’umma yadda komai ya wakana.

BBC ta zanta da wasu maza biyu a Tanzaniya da Kenya da hakan ya taɓa faruwa da su.

Shiryawa da tacewa Ashley Lime da Anne Okumu.