Bidiyon yadda ake ƙirga ƙuri'a a zaɓen Ghana
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An soma ƙirga ƙuri'un zaɓen Ghana a wasu rumfunan zaɓen ƙasar.
An dai fara jefa ƙuri'un ne tun da safiyar yau Litinin.
Manyan 'yan takarar da ke fafatawa su ne Shugaban ƙasar Nana Akuffo-Addo da kuma Tsohon Shugaban ƙasar, John Dramani Mahama.
Ƴan takara 11 ke ƙalubalantar shugaba mai-ci Nana Akufo-Addo, wanda ke neman wa'adi na biyu.