Bidiyo: Garin da mutanensa ke ɗiban ruwan sha a maƙabarta a Zimbabwe
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mazauna garin Haphley a ƙasar Zimbabwe na ɗaukar wata kasada don ganin cewa sun samu ruwan sha da na amfani.
A yayin da rijiyoyin cikin gari ke ƙafewa, mutanen a yanzu sun koma tona rijiya da hannunsu a cikin wata maƙabarta
Sai dai ruwan da ke ɓulɓulowa daga cikin ƙaburburan matattu da ke haɗewa da na rijiya ba ƙaramar barazana yake yi ga lafiya ba.
Sannan masana sun yi gargaɗi cewa yawan ruwan saman da ake samu a ƙasar zai matuƙar raguwa, kuma wuraren da ake samun ruwa za su ƙafe saboda sauyin yanayi.