Bidiyo: Makarantar da ke haɗa kan yaran da ƙabilunsu ke rikici da juna
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Akwai wasu ƙabilu da ke faɗa da juna daga ƙasashen Kenya da Uganda da suke kan iyakokin ƙasar.
Rikici tsakaninsu ya yi ƙamari ta yadda zamna lafiya ya ƙi samuwa.
Daga baya an samar da wata makaranta don yaransu su dinga halarta da ke ƙoƙarin haɗa kan yaran don su so juna.