Me ya jawo fashewar da ta girgiza Najeriya?
Wata gagarumar Fashewar wani abu da ya faru a jihar Legas da ke Najeriya ya girgiza jihar, mutum 23 aka tabbatar da mutuwarsu, inda fashewar ta tarwatsa wata makarantar mata da ke jihar.
Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya ya bayyana cewa fashewar ta faru ne sakamakon wata babbar mota da ta bugi wasu tukwanen gas kusa da ɗaya daga cikin bututun mai na kamfanin na NNPC.
Sai dai wani bincike da sashen binciken ƙwa-ƙwaf na BBC Africa Eye ya gudanar, ya fito da bayanai kan ainahin abin da ya jawo fashewar, inda fashewar ta lalata sama da murabba'in mita 100,000 na birnin na Legas.