Click Challenge: Tallar 'wulaƙanta' gashin matan Afrika da ya jawo ɓacin rai
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo:
Wani tallan kayan TRESemmé - ya bayyana gashin kan matan Afrika da cewa a cukurkuɗaɗɗe yake yayin da aka nuna na matan Turawa kuma a matsayin mafi kyau - ya jawo cacar baki da zazzafar muhawara kan yadda ake ''wulaƙanta'' gashin baƙaƙen mutane da tarihin nuna wariya a Afrika Ta Kudu.
Da TRESemmé da kamfanin Clicks, waɗanda suka yi tallan sun ba da haƙuri.
Mutane sun yi ta nuna ɓacin ransu a shafukan sada zumunta inda suka yi ta wallafa hotunan kansu da ke nuna gashin kansu na ainihi, ta hanyar amfani da maudu'in #ClicksChallenge da kuma ClicksMustFall.