Shin za ku iya tura wa mawaƙi kudi don waƙe ɗan siyasa?
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo:
A makon da ya gabata ne fitaccen mawaƙin siyasar nan da ya yi fice a yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya waƙa Dauda Kahutu Rarara ya ce ya daina yi wa shugaban ƙasar waƙa har sai talakawa sun ba shi naira dubu ɗai-ɗai.
Kwanaki kaɗan da faɗar hakan sai ga wasu mawaƙan kamar Adam A Zango da Abubakar Sani sun ce su ma a tara kuɗin za su waƙe masoyansu Atiku Abubakar da Dr Rabi'u Musa Kwankwaso.
Maganganun nasu dai sun jawo tayar da jijiyar wuya daga ƴan ƙasa inda wasu suka dinga sukar su wasu kuma na goyon bayan aniyar tasu.
A wannan bidiyon BBC ta yi wani nazari ne kan wannan batu.
Ma'aikata
Ɗaukar bidiyo: Bashir
Tsarawa da shiryawa: Umar Rayyan
Tace bidiyo: Fatima Othman
Gabatarwa: Umaymah Sani Abdulmumin