'Yar Afrikar da mai cutar korona ya tofa mata yawu kuma mutuwarta ta jawo zanga-zanga a Burtaniya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Belly Mujinga, ma'aikaciya ce a filin jirgin kasa kuma 'yar asalin Congo, wadda ta mutu bayan ta kamu da cutar korona sakamakon tofa mata yawu da wani mai dauke da cutar ya yi.
Matasa sun yi ta zanga-zangar mutuwarta, yayin da suka ce dole 'yan sanda su ci gaba da bincike kan abin da ya faru.