Bidiyon yadda Musulman Rohingya suka dinga shan ruwan teku don su rayu
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Malaysia ta umarci wani jirgin ruwa da ke dauke da daruruwan 'yan gudun hijirar Rohingya ya koma inda ya fito, tana ba da hujja da fargabar yaduwar cutar korona.
A lokacin da masu gadin gabar teku na Bangladesh suka ceto jirgin ruwan, an yi kiyasin cewa mutum 20 zuwa 50 ne suka mutu.
Sai dai an yi amanar har yanzu wasu suna can makale a tekun, suna neman wajen fakewa.