Bambancin sarauta a jiya da yau – Sarkin Zazzau
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar 8 ga watan Fabrairu ne Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya cika shekara 45 a kan mulki.
Sarkin dai ya hau gadon sarauta ne a shekarar 1975 bayan da ya gaji sarkin da ya rasu Alhaji Muhammadu Aminu.
A wannan hirar ta musamman Mai Martaba Sarkin na Zazzau ya bayyana wa BBC yadda mulkin sarauta yake a lokacin da hau da kuma yadda yake a halin yanzu.