Cinikin 'yan kwallo: Roma ta mallaki Chris Smalling

Muna kawo muku labaran 'yan wasan da aka saya a kasuwar saye da musayar 'yan ƙwallon ƙafa kai-tsaye, yayin da ake rufe kasuwar a yau Litinin.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu and Umar Mikail

  1. Nan na kawo karshen shirin

    da fatan za ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa don kawo muku labarin wasanni da dumi-duminsu.

    Sunana Mohammed Abdu a madadin Umar Mikail nake cewa sai an jimanku.

  2. Labarai da dumi-dumi,

    An kammala cin kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai a kuma Ingila, yanzu kungiyoyin Premier League za su yi ciniki tsakaninsu da masu buga Championship..

    Muna jiran labari ko cinikin Thomas Partey da na Ruben Loftus sun fada kuwa kan rufe kasuwar?

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Wasu ciniki da aka kammala daf da za a rufe kasuwa

    Transfer

    Asalin hoton, bbc

    Transfer

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. Roma ta mallaki Chris Smalling daga Man United

    Roma ta mallaki dan kwallon Manchester United mai tsaron baya Chris Smalling kan kwantiragin shekara uku kan fam miliyan 15, kudin zai iya kai wa fam miliyan 20 idan aka hada da tsarabe-tsarabe.

    Hukumar kwallon kafar Italiya ce ta kammala dukkan abubuwan da ake bukata na rubutu a lokacin da saura minti daya a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon ta nahiyar Turai. Tun da yammaci aka rufe ta Italiya.

    Smalling mai shekara 30, ya buga wasannin aro a bara a Roma, wacce ta yi ta biyar a kakar da aka karkare a Serie A.

    A baya can United da Roma sun kasa cimma matsaya kan farashin dan kwallon.

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Labarai da dumi-dumi, Manchester United ta kammala daukar Edison Cavani

    Transfer

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayanan hoto, Manchester United ta kammala daukar tsohon dan wasan Paris St-Germain da kuma Napoli, Edinson Cavani a matakin mai cin gashin kansa
  6. Michael Cuisance zai buga wa Marseille wasannin aro daga Bayern Munich

    Michael Cuisance ya koma Marseille domin ya buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana daga Bayern Munich, kwana uku da cinikin zuwa Leeds United ya bi ruwa.

    Mai shekara 21, wanda ya wakilci tawagar Faransa ya kusan komawa kungiyar da Marcelo Bielsa ke jan ragama kan kudin da ake cewar ya kai fam miliyan 20 daga baya hakan bai yi wu ba.

    Wasu rahotannin na cewar bai da koshin lafiyar da ya kamata kungiyar ta dauke shi.

    Cuisance ya buga wa Bayern Munich wasa 10 a kakar 2019-20 ya kuma ci kwallo daya tal.

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Wolverhampton ta dauki aron Rayan Ait-Nouri

    Wolverhampton Wanderers ta kammala daukan aron matashin tawagar Faransa Rayan Ait-Nouri, yayin da mai tsaron bayanta Ruben Vinagre ya koma Olympiakos.

    Ait-Nouri, mai shekara 19 ya je kungiyar ne daga Angers mai buga gasar Lique 1 ta Faransa.

    Shi kuwa dan kwallon Portugal, Vinagre zai buga wasannin aro a Girka da yarjejeniyar sayensa idan ya taka rawar gani.

    Mai shekara 21, wanda ya buga wa Wolves wasa 70 tun lokacin da ya koma Ingila da taka leda daga Monaco a 2017 ya yi godiya ga dukkan wadanda ke Wolves har da magoya baya.

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Southampton na duba koshin lafiyar Walcott daga Everton

    Southampton na duba koshin lafiyar dan kwallon Everton, Theo Walcott wacce zai buga wa wasannin aro zuwa karshen kakar bana.

    Mai shekara 32 baya buga wasanni sosai karkashin Carlo Ancelotti, dalilin da ya sa ya nemi ya koma taka leda aro a tsohuwar kungiyarsa.

    Walcott wanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasa 47 ya fara tamaula a Southampton daga baya ya koma Arsenal a 2016.

    Everton ta dauki dan wasan daga Gunners kan fam miliyan 20 a Janairun 2018

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Masu tsaron bayan Manchester United na yoyo

    Za a dade ba a manta wasannan ba.

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Munich ta sake ɗaukar Douglas Costa

    Bayern Munich ta karɓo aron tsohon ɗan wasanta Douglas Costa daga Juventus kan yarjejeniyar shekara ɗaya.

    Ɗan ƙasar Brazil mai shekara 30, ya buga wa Munich wasa daga shekarar 2015 zuwa 2017, inda ya koma zakarun Serie A na Italiya.

    Ya ci ƙwallo 14 cikin wasa 77 yayin zamansa a birnin Munich.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Juventus ta sayi Federico Chiesa daga Fiorentina

    Juventus ta dauki Federico Chiesa daga Fiorentina kan cinikin da ake cewar zai kai fam miliyan 60.

    Mai shekara 22 zai buga wa Juventus wasannin aro kaka biyu daga baya ya zama mallakinta.

    Chiesa ya fara tamaula a matashin dan kwallo a Fiorentina ya kuma fuskanci Juventus a 2016.

    Kawo yanzu ya buga wa Fiorentina wasa sama da 150 ya kuma yi wa tawagar Italiya wasa 19.

    Transfers

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Man United ta dauki Telles daga Porto

    Manchester United ta kammala daukar dan kwallon tawagar Brazil, mai tsaron baya daga gefe Alex Telles kan yarjejeniyar shekara hudu daga Porto za kuma a iya tsawaita masa kaka daya.

    Mai shekara 27, wanda ya buga wa kasarsa wasa daya tal, ya koma Old Trafford da taka leda kan fam miliyan 13.6 da karin fam miliyan 1.8 na tsarabe-tsarabe.

    Telles ya ci kwallo 26 ya kuma taiamaka aka zura sama da 50 a raga tun lokacin da ya koma Porto daga Galatasaray a 2016.

    Transfer

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Bayern Munich ta ɗauki Eric Maxim

    Eric Maxim

    Asalin hoton, Bayern Munich

    Eric Maxim Choupo-Moting ya koma Bayern Munich kan yarjejeniyar shekara ɗaya bayan ya bar PSG.

    Ɗan wasan gaban ya bar PSG ne a ƙarshen kakar bara kuma yanzu ya koma Jamus kyauta ba tare da biyan ko ficika ba.

    Mai shekara 31 ɗin ya buga wasan ƙarshe na Champions League tsakanin Bayern da PSG mako shida da suka gabata a birnin Lisbon na Portugal.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Arsenal na fatan sayen Thomas Partey a yau

    Partey

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta nemi sayen Thomas Partey a hukumance daga Atletico Madrid.

    Shafin Goal.com ya ce Gunners ta yi yunƙuri a ƙurarren lokaci domin ta ja hankalin ɗan wasan tsakiyar.

    Sai dai dole ne ta yi dukkanin abin da za ta iya wurin sayensa kafin nan da ƙarfe 11:00 na daren yau ɗin nan.

  15. Man United na neman sayen matasa biyu

    Manchester United na fatan kammala ɗaukar matasan 'yan wasa biyu kafin rufe ƙofa da ƙarfe 11:00 na daren yau.

    United na fatan sayen Amad Traore mai shekara 18 kuma ɗan ƙasar Ivory Coast, wanda ta sha nema tsawon shekaru daga ƙungiyar Atalanta ta Italiya.

    Kazalika tana son ɗaukar Facundo Pellistri daga ƙungiyar Penarol ta ƙasar Uruguay mai shekara 18, amma idan ba ta ssamu dama ba a yau za ta sake nemansa a watan Janairu.

  16. Fortuna Dusseldorf ta ɗauko Peterson daga Swansea City

    Ɗan wasan gaba na Swansea City Kristoffer Peterson ya koma Fortuna Dusseldorf kan kuɗi kusan fan 400,000.

    Peterson, mai shekara 25, wasanni 12 kawai ya buga wa 12 - ya ci ƙwallo ɗaya - tun da ya zo kulub ɗin daga Heracles kan fan 500,000

    Peterson

    Asalin hoton, BBC Sport

  17. Traore zuwa Old Trafford?

    Manchester United na kan tattaunawa domin ɗauko ɗan wasan gaba na Atalanta Amad Traore.

    United ta daɗe tana sa ido kan Traore tsawon shekara uku tun kulub ɗin ya hauro Serie A .

    Ɗan Ivory Coast ana ganin yana cikin matasan da ke lokacinsu a Turai.

    Idan har cinikin ya kankama ana tunanin Traore zai ci gaba da taka leda a kulub dinsa har zuwa Janairu

  18. Moise Kean ya koma PSG daga Everton

    Moise Kean

    Asalin hoton, PSG

    Moise Kean ya koma PSG a matsayin aro daga Everton na tsawon shekara ɗaya.

    Ɗn wasan mai shekara 20 ya koma Everton ne a watan Agustan 2019 kuma bai ci ƙwallo ɗaya ba a gasar Premier.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Guendouzi, Torreira, Kolasinac na kan hanyar barin Arsenal

    Matteo Guendouzi na Arsenal na cikin waɗanda ake sa ran za su motsa a yau zuwa Hertha Berlin ta Jamus.

    Guendouzi na kan hanyarsa ta zuwa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin Marseille ta Faransa da Villarreal ta Sifaniya da Roma ta Italiya amma an fi sa ran zai koma Jamus.

    Kazalika, ana sa ran Lucas Torreira zai koma Atletico Madrid, yayin da ake sa ran Sead Kolasinac zai koma Bayer Leverkusen.

  20. Man United da Cavani sun ƙulla yarjejeniya

    Cavani

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta ƙulla yarjejeniya da Edinson Cavani, inda za ta ba shi albashin fan £210,000 duk mako, a cewar jaridar Daily Mail.

    Zai saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da United kuma hakan zai sa Cavani ya zama ɗan wasa na huɗu da ya fi kowa yawan albashi a Old Trafford.

    Za a yi wa Cavani gwajin lafiya kuma ana sa ran za a bayyana shi a hukumance nan gaba a yau Litinin.

    Cavani ya koma Man United ne bayan PSG ta Faransa ta sallame shi.