Sai da safenku
A nan na kawo karshen shiri da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu.
Sai ku tara a shiri na gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasanni a karawar Manchester City da Liverpool da na Real Madrid da Getafe.
Mohammed Abdu
A nan na kawo karshen shiri da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu.
Sai ku tara a shiri na gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, BBC Sport
An tashi wasa Sergio Ramos ya samarwa Real maki ukun da take bukata.
Yanzu Real Madrid ta bai wa Barcelona tazarar maki hudu kenan.
Tsare baya mai kyau da dan wasan Real Madrid Ferland Mendy wanda ya hana Jason ya wuce shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An shiga karin lokaci kuma dai Real ta samu maki ukun da take bukata kam.
Getafe ta saka Faycal Fajr ya maye gurbin David Timor.
Real Madrid ta samu fenariti ne, bayan da Dani Carvajal ya yi gudu da kwallo daga gefen dama nan da nan ya fada da'ira ta 18 ta Getafe.
Daga nan kuma ya yanke Mathías Olivera shi kuma ya sa kafa ya yi masa keta.
Sergio Ramos bai bata tsaya gwalangwaso ba ya buga fenaritin kuma mai tsaron raga David Soria ya bi kwallon amma ta yi zafin da ba zai iya tarewa ba.

Asalin hoton, BBC Sport

Asalin hoton, BBC Sport
Har yanzu Real Madrid ba ta ci Getafe ba wacce ake ganin za ta yagalgala.
Ko a wasan farko da suka buga a Janairu Real ce ta ci 3-0.
Tana kuma bukatar makin nan domin ta bai wa Barcelona tazarar maki hudu, in da haka ba komai zai iya faruwa.
Wasa biyu kacal aka doke Liverpool kawo yanzu.
Man City ta hada maki 100 a kakar 2017-18, Liverpool tana da 86 kawo yanzu saura wasa shida a karkare kakar bana. Wasa shida nan gaba na nufin 18 a kasa idan za ta ci kowanne ko kuma ta hada 15 wato ta ci fafatawa biyar kenan.
An rage tazarar maki ya koma 20 tsakanin Liverpool ta daya da City ta biyu, inda City ta ci kofin 2017-18 da tazarar maki 19.
Sai dai Liverpool ba za ta kamo tarihin da City ta ci wasa 16 a waje ba kamar yadda ta yi a 2017-18, abinda Liverpool za ta iya yi shi ne 15 nan gaba ko da za ta lashe wasannin waje da ke gabanta.
They can't now equal City's record for away wins in a season, though. City got 16 in, wait for it, 2017-18. The most Liverpool can now get is 15.

Asalin hoton, Getty Images
Sai da City ta yi wa Liverpool tarbar girma ashe ta shirya zura mata kwallo har hudu.
Barka dai Liverpool ta riga ta lashe kofin in ba haka ba ai an yaga baraka kenan.

Asalin hoton, PA Media
Yadda kungiyoyin biyu suka murza kwallo.

Asalin hoton, BBC Sport
Manchester City ta samu maki uku kenan a kan Liverpool a Etihad.
An soke kwallon bayan da aka je aka duba a VAR an ga Phil Foden ya taba kwallon a lokacin da zai fadi kasa kuma lokacin ne Mahrez ya zari kwallo aka je aka ci Liverpool.
Wasa ya koma City 4-0 Liverpool.

Asalin hoton, Reuters
Ko yaya Klopp ke ji ace da lashe kofin Premier a wasa na gaba a zura wa Liverpool har kwallo 4-0.
to ko dai shi ya sa Guardiola ya ce za su yi wa Liverpool tarbar girma?

Asalin hoton, Getty Images
Minti 90 ya cika sai karin lokaci ko Liverpool za ta zare ko kwallo daya ne kuwa?