Man City ta sharara kwallo biyar a ragar Burnley

Wannan shafi ne kai tsaye kan wasan Premier League tsakanin Manchester City da Burnley da wasu labaran wasanni da ke wakana a rana Litinin

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. A nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a gobe da zan kawo muku wasan Barcelona da Bilbao a gasar La Liga.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw nake cewa ku tara a shirin safe da hantsi a gobe don jin labarin wasanni ta radiyo a bbc Hausa.

  2. Man City 5-0 Burnley

    An tashi wasa kuma Manchester City ta hada maki uku da kwallaye biyar a raga.

    Burnley dai ba ta gurbin da za ta bar buga gasar Premier League ta bana.

  3. Man City 5-0 Burnley

    An kusan tashi wasan ga yadda kungiyoyin ke murza leda.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. Bologna 0-2 Juventus

    Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 43 a gasar Serie A tun lokacin da ya koma Juventus .two years (but not quite two seasons) ago.

  5. Man City 5-0 Burnley

    Wanan ne karon farko da Leroy Sane ya fara buga wa City tamaula tun raunin da ya ji a Community Shield a cikin watan Agusta.

    Ranar Juma'a kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce Sane bai amince ya saka hannu kan kunshin yarjejeniyar da aka gabatar masa ba, ya zabi zai bar Etihad domin gwada nasara a wata kungiyar.

  6. Man City 5-0 Burnley

    Filin Etihad ba kowa kuma wasan kamar na sada zumunta domin ba 'yan kallo kamar yadda aka umarta don gudun yada cutar korona.

    Magoya bayan City sun yi kaurin suna su juya baya suna tsalle da sowa da rera waka idan wasa ya yi musu kyau.

    Sai dai kuma an nada muryar ihu da sowar 'yan kallo ana sawa kaji kamar da mutane na kallon wasa.

    Hakika cutar korona ta dagula abubuwa da dama, kuma sai nan gaba ne komai zai koma daidai.

  7. Man City 5-0 Burnley

    Man City ta fitar da Foden wanda ya ci kwallo biyu a karawar ta maye gurbinda da Leroy Sane, kuma canji na biyu da ta yi bayan Aguero da ya yi rauni,

  8. Bologna 0-2 Juventus

    An yi hutu Juventus ta ci kwallo biyu kuma kawo yanzu ta bayar da tazarar maki hudu kenan.

  9. Bologna 0-2 Juventus

    Paulo Dybala ya ci wa Juventus kwallo na biyu, bayan da Ronaldo ya ci na farko a bugun fenariti.

  10. Man City 5-0 Burnley

    Kwallayen nan ba su isa ba a wajen De Bruyne dobin kwallojn da ya samu daga tsakiya ya kuma gwada sa'a ya nemi ragar Burnley.

    Burnley ta yi da ce kwallon da ya buga ta yi fadi da yawa.

  11. Man City 5-0 Burnley

    Gabriel Jesus ya kusan kara kwallo na shida amma tamaula da ya buga ta i fadi.

  12. Man City 5-0 Burnley, Phil Foden

    Kwallon da aka ci Burnley ta yi kyau domin tun daga gefen fili ta dama aka jawa kwallo inda De Brune ya bai wa Siva shi kuma ya bugo ta zuwa ciki har wajen Gabriel Jesus wanda ya bai wa Foden shi kuma ya buga daf da turke ta fada raga.

  13. Man City 4-0 Burnley

    Foden na nuna kansa tun lokacin da City ta ci gaba da buga gasar Premier League yana kuma nuna cewar kafi ya zo masa da zai iya karbar nauye-nauyen kungiyar.

    Ya samu kwallo ya buga kuma a karo da dama duk wadda ya buga ta kan nufi raga wata a sanyaye wata kuwa mai hatsari.

  14. Man City 4-0 Burnley, David Silva

    Kwallo ce aka yi tun daga kwana aka kai ta gefen fili aka shigo da ita Burnley ta yi kokarin bayar da satar gida amma ina sai kwallo ya je wajen David Silva shi kuwa bai ba ta lokaci ba ya zura a raga kwallo na hudu kenan.

    Burnley dai ta tsare ragarta in ba haka ba za a rubuta mata sunanta da yawan kwallaye a raga a wasan nan.

  15. Bologna 0-1 Juventus, Cristiano Ronaldo

    Ronaldo ne ya hau kan kwallon ya kuma duba wurin da zai yi mai ya buga kwallo ta yi gefe guda mai tsaron raga shima ya yi nasa gefen.

  16. Juventus ta samu bugun fenariti, Bologna 0-0 Juventus

  17. Man City 3-0 Burnley

    Damai mai kyau da wanda ya canji Aguero wato Gabriel Jesus ya samu ya kuma buga kwallon amma ba wani zafi.

  18. An koma zagaye na biyu Man City 3-0 Burnley

    sai a yi wa Burnley addu'a domin kwallayen nan suna da yawa ba su tsaya iya uku ba kamar yadda karawar ke gudana.

  19. Man City 3-0 Burnley

    An yi hutu ko Burnley za ta rage kwallayen da aka zura mata ko kuma za a kara mata nan gaba.

  20. Man City 3-0 Burnley, Riyad Mahrez