Kofin Duniya: Yadda Croatia ta doke Najeriya

Najeriya ta sha kashi a fafatawarta da Croatia a rukuninsu na D a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Sai wani lokacin, Croatia 2-0 Najeriya

    A nan muka kawo karshen sharhin kai-tsaye da muka kawo ma ku a gasar cin kofin duniya

    Sai wani lokacin.

  2. Najeriya tana kasan teburin rukuni, Croatia 2-0 Najeriya

    Croatia ke jagorantar rukunin D bayan ta doke Najeriya. Argentina da Iceland sun tashi 1-1

    Rukunin D
  3. Croatia ta doke Najeriya, Croatia 2-0 Najeriya

  4. An hure wasa, Croatia 2-0 Najeriya

  5. Kovacic ya yi gaba da gaba da golan Najeriya, Croatia 2-0 Najeriya

    Amma golan ya kame

  6. Yadda Modric ya ci Najeriya a Fanareti, Croatia 2-0 Najeriya

    Modric

    Asalin hoton, Reuters

  7. An kara minti hudu, Croatia 2-0 Najeriya

  8. An fitar da Mikel, Croatia 2-0 Najeriya

    Nwankwo ya karbe shi

  9. Najeriya ta nemi rama kwallo daya, Croatia 2-0 Najeriya

  10. Pjaca ya karbi Mandzukic, Croatia 2-0 Najeriya

    Croatia ta sake canji

  11. Saura minti biyar a hure wasa, Croatia 2-0 Najeriya

  12. An bayar da Fanareti biyar a rana daya, Croatia 2-0 Najeriya

    Messi ya barar da Fanareti a wasan Argentina da Iceland. Fanareti biyar aka bayar a wasannin da aka buga a yau Asabar

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Iheanacho ya kai kora, Croatia 2-0 Najeriya

    Ya nemi ya ba musa ya ci amma Strinic ya kabe wa Croatia kwallon

  14. Kovacic ya karbi Rebic, Croatia 2-0 Najeriya

    Croatia ta yi canji

  15. Saura kiris Croatia ta kara, Croatia 2-0 Najeriya

  16. Iheanacho ya karbi Ighalo, Croatia 2-0 Najeriya

    Najeriya ta sake yin canji

  17. Croatia ta dawo tana matsawa Najeriya, Croatia 2-0 Najeriya

  18. Modric ya ci fanareti, Croatia 2-0 Najeriya

  19. Modric, Croatia 2-0 Najeriya

  20. Croatia ta samu fanareti, Croatia 1-0 Najeriya

    Ekong ya yi wa Mandzukic keta bayan an bugo kwana