Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na kai-tsaye. Sai kuma gobe da safe da za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 22 ga watan Mayun, 2024.
Abdullahi Bello Diginza, Usman Minjibir, Umar Mikail and Haruna Kakangi
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na kai-tsaye. Sai kuma gobe da safe da za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Fadar White House ta nuna adawarta a fili ta amince da yankin Falasdinawa a matsayin kasa mai 'yanci da wasu kasashen Turai uku suka yi.
Wakiliyar BBC ta ce fadar ta White House ta ce Shugaba Biden ya daɗe yana son a samar da ƙasa biyu a duk tsawon mulkinsa, sai dai ya fi so a ƙyale ƙasashen biyu su amince a tsakaninsu bayan sun tattauna.
Falasdinawa sun yi farin ciki da matakin da Norway, da Ireland, da Sifaniya suka ɗauka, kuma suna yi masa kallon abu mai cike da tarihi.
Ita kuma Isra'ila ta yi Allah-wadai da matakin wanda ta kira "kyauta ce ga ta'addanci".
Ta ƙara da cewa wannan rashin nuna girmamawa ne ga mutanen da aka kashe a ranar 7 ga watan Oktoba.
Yayin da ake shirye-shryen gudanar da zaɓen babban zaɓe a kasar Ghana, mafi yawan 'yan takarar shugabancin kasa sun zaɓi abokan takarar da za su yi musu mataimaka.
Sai dai har yanzu Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahmudu Bawumiya, wanda ke cikin 'yan takarar, bai zaɓi nasa mataimakin ba.
Wasu na yi wa lamarin kallon abu mai sarƙaƙiya, yayin da wasu suke ganin jan ƙafa yake yi.
Hakan ta sa da yawan al`umma ke ci gaba da shaci-faɗi a kan wanda mataimakin shugaban kasar zai zaɓa.
Tuni babban abokin hamayyarsa tsohon Shugaban Ƙasa John Mahama na babbar jam'iyyar adawa ta NDC ya zaɓi mace a matsayin mataimakiyarsa.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton da wakilinmu Fahd Adam ya aiko mana daga Accra.

Jagoran adawa a Birtaniya kuma shugaban jam'iyyar Labour, Sir Keir Starmer, ya yaba wa sanarwar da gwamnatin jam'iyyar Conservative ta gudanar da babban zaɓe a watan Yuli.
Ya siffanta sanarwar da cewa shi ne abin da ƙasar ke buƙata take ta jira.
Starmer ya ce lokaci ya yi da za a sauya rayuwar al'umma da ƙasa baki ɗaya, kuma ya bayyana lokacin yaƙin neman zaɓe a matsayin wata dama da za a sama wa Birtaniya kyakkyawar makoma.

Asalin hoton, facebook/Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa jihar za ta fara aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi naira 30,000 ga ma'aikatan jihar daga farkon watan Yuni mai zuwa.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin ƙungiyar ƴan ƙwadago reshen jihar.
Tun farko ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa'di zuwa ranar 23 ga watan Mayu ta fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin, tare da barazanar shiga yajin aiki matuƙar aka gaza cimma hakan.
Sai dai a tattaunawar da ta gudana yau Laraba, gwamna Dare ya ce: "Yau ina tabbatar muku cewa daga (watan) June za mu biya mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar Zamfara".

Asalin hoton, NG POLICE
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon mataimakin kwamishinan ƴan sanda a Najeriya DCP Abba Kyari na tsawon mako biyu.
Kotun ta ce ta bayar da belin nasa ne domin ba shi damar zuwa gida domin ta'aziyyar mahaifiyarsa wadda ta rasu.
Kotun ta bayar da belin ne kan kuɗi naira miliyan 50 da kuma wani wanda zai tsaya masa.
Haka nan kotun ta ajiye ranar 31 ga wannan wata na Mayu domin sauraron takardar da Abba Kyarin ya shigar na neman beli.
Mahaifiya Abba Kyari ta rasu ne a farkon wannan wata.
Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare Kyari, Barista Hamza Nuhu Ɗantani ya bayyana wa BBC cewa tuni dama suka gabatar da buƙatar belin nasa a kotu.
Ana tuhumar Kyari ne da laifukan da suka jiɓanci safarar ƙwaya bayan kamen da Hukumar yaƙi da safarar ƙwaya ta Najeriya NDLEA ta yi masa shekara biyu da suka gabata.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi balaguro zuwa Chadi ranar Alhamis da zimmar shaida bikin rantsar da Mahamat Déby a matsayin shugaban ƙasar.
A farkon wannan watan na Mayu ne aka ayyana Mahamat a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 6 ga wata.
Sai dai 'yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen.
Wannan ne karon farko da Tinubu zai je Chadi tun bayan zama shugaban ƙasa a watan Mayun 2023.
"Manyan jami'an gwamnati za su yi wa shugaban rakiya kuma za su koma gida bayan kammala bikin," in ji sanarwar.

Asalin hoton, PA Media
Bayan awanni ana raɗe-reɗi Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya tabbatar da cewa za a gudanar da babban zaɓe nan da 'yan makonni.
Bari mu duba manya daga cikin abubuwan da sanarwar tasa ta ƙunsa:

Asalin hoton, Reuters
Mayakan 'yan tawaye a Myanmar sun faɗa wa BBC cewa suna da ƙwarin-gwiwar nasara a yaƙin da suke yi da sojojin gwamnati.
Wakilin BBC ya shafe wata guda tare da ɗaya daga cikin ɓangarorin 'yan tawayen na KNDF da ke jihar Karenni.
Ya shaida yadda suke amfani da lasifika wajen kira ga sojojin da suka yi wa kawanya su mika wuya.
A yankin arewaci na jihar Shan, 'yantawayen sun sha luguden wuta daga dakarun gwamnatin da suka dinga amfani da makaman atilary da sauran makamai wajen murkushe su.
Dubban fararen hula ne suka rasa rayukansu a Myanmar tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula a 2021.

Asalin hoton, PA Media
Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya sanar da cewa zai rushe majalisar zatarwar ƙasar a mako mai zuwa gabanin zaɓen ƙasar da za a gudanar a ranar huɗu ga watan Yuli.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan cece-ku-ce da raɗe-raɗin da aka riƙa yi, bayan hauhawar farashi a ƙasar ta kai wani mataki da ba ta taɓa kaiwa ba cikin shekara uku.
Jam'iyyar da ke mulkin ƙasar ta ƴan mazan jiya za ta shiga zaɓen yayin da take baya a ƙuri'ar jin ra'ayin al'umma, yayin da jam'iyyar Labour take gaba.
Jam'iyyar Conservatives ta kwashe shekara 14 a jere tana jagorancin ƙasar ta Birtaniya.

Asalin hoton, Prince Bello/X
Shugaban Najeria, bola Tinubu ya amince da naɗin ACM Mohammed Shehu a matsayin sabon shugaban hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnan tarayyar ƙasar, Sanata Gorge Akume, ta ce shugaban ƙasar ya amince da naɗinsa bisa tanadin dokar hukumar.
Da farko ACM Shehu zai yi wa'adin shekara huɗu, farawa daga ranar 20 ga watan Mayun 2024, kamar yadda dokokin da suka kafa hukumar suka tanadar.
Shugaba Tinubu ya hori sabon shugaban hukumar ta FRSC ya yi amfani da ƙwarewar da yake da ita wajen kawo gagarumin ci gaba a sabon muƙamin nasa.
ACM Shehu ya maye gurbin CM Dauda Biu, wanda wa'adin shugabancinsa ya ƙare.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta dakatar da rabon abinci a kudancin Gaza sakamakon rashin isasshen abincin da kuma matsalar rashin tsaro.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, UNRW ta yi gargaɗin cewa yanzu ba a iya kai wa ga cibiyar raba abinci da gidajen ajiyar abincin saboda yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas a gabashin Rafah.
Aƙalla mutum 815,000 daga cikin fiye da miliyan ɗaya da ke neman mafaka a Rafah sun tsere tun fara yaƙin makonni biyu da suka gabata.
Hukumar ta Unrwa ta ce cibiyoyin lafiya ba su samu magunguna a tsawon kwanaki 10 ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke cewa ba ta amince ƙungiyoyin agaji sun raba dukkannin tallafin da aka kai ta ruwa zuwa Gazar ba.
A ranar Asabar, dandazon Falasɗinawa da ke cikin matsanancin buƙatar abinci suka tare motocin hukumar abinci ta duniya da dama, wani abu da ya tilasta wa hukumar dakatar da raba tallafin.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya da na 'yan sanda a Najeriya sun yi wa harabar zauren majalisar dokokin jihar Cross River ƙawanya, inda suka ƙwace iko da majalisar.
Matakin na zuwa ne bayan majalisar ta sanar da tsige kakakinta, Honarabul Elvert Anyambem a yau Laraba da rana.
Rahotonni daga ƙasar na cewa 'yan majalisar dokokin jihar sun tsige kakakin nasu ne saboda zargin ɓarnatar da kuɗi da suke yi masa.
'Yan majalisar sun kwashe watanni suka yunƙurin tsige kakakin nasu sakamakon abin da suka kira ''rashin gamsuwa da tsarin jagorancinsa''.

Asalin hoton, Olusegun Obasanjo/X
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obansanjo ya shawarci al'ummar Afirka su sake nazarin tsarin dimokraɗiyyar da Turawan Yamma suka gasar musu.
Gidan talbijin na Channel a Najeriya, ya ambato mista Obasanjo na cewa dole ne ƙasashen Afirka su gina tsarin dimokraɗiyyar da zai dace da al'adu da ɗabi'un al'ummar yankin.
Mista Obasanjo ya bayyana hakan ne a wani taro kan dimokradiyyar nahiyar Afirka da aka gudanar a ɗakin taro na Yar’adua Centre da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce lokaci ya yi da al'ummar Afirka za su ajiye tsarin da turawa suka gadar musu, su gina nasu wanda zai dace da ala'dunsu.
Ya kuma ce yana da kyau shugabannin Afirka su nuna kishi da kan ci gaban al'umominsu.
Obasanjo ya ce idan ana son dimokraɗiyya ya yi aiki a Najeriya da ma Afirka baki-ɗaya, dole ne a gina shi kan tsarin shugabanci na gari, ta hanyar bai wa doka ta yi aiki.
Tsohon shugaban ƙasar, ya sha sukar yadda ake gudanar da tsarin dimokraɗiyya a Najeriya da ma ƙasashen Afirka.

Asalin hoton, ..
Majalisar dokokin jihar Cross River ta tsige kakakin majalisar Rt. Hon. Elvert Ekom Ayambem.
A ranar Laraba ne mambobin majalisar 17 daga cikin 25, suka amince da tsige kakakin nata sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗi.
Tun a ranar Talata ne 'yan majalaisar suka fara yaunƙurin tsige kakankin, inda kusan 'yan majalisar 20 suka goyi bayan ƙudirin tsige ɗan majalisar mai wakiltar ƙareamar hukumar Ikom 2.
A watan Yunin 2023 ne aka zaɓi Rt Hon Elvert Ayambem a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar ta 10.

Asalin hoton, others
Majalisar dokokin jihar Katsina ta buƙaci kamfanin sadarwa na MTN ya daina yawan katse sabis ba tare da yin gamsasshen bayani ga al'umma ba.
Majalisar ta bayyana cewa yawan katse sadarwar na cutar da kasuwanci da zamantakewar al'ummar jihar.
Cikin wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dandume, Hon. Yahaya Nuhu Mahuta ya gabatar a zauren Majalisar ranar Talata, ya ce katse sabis da kamfanin ke yi ya shafi ɓangarori kasuwanci, ilimi da harkokin yau-da-kullum na al'ummar jihar.
Mataimakin kakakin majalisar jihar, Honarabul Hon Abduljalal Haruna Runka ya shaida wa BBC cewa haƙƙin kamfanin ne ya samar da nagartattun ayyuka, domin al'umma kuɗi suka biya don neman biyan buƙata.
Ya bayyana cewa babban takaicin, kamfanin bashi bada wani uzuri ko cikakken bayani akan dalilin ɗaukewar sabis ɗin.
Hon. Mahuta ya ce al'umma suna da hakki a kan kamfanin, kuma gazawar zai baiwa alummar damar chanza tsarin da suke ganin zai taimake su.
Haka kuma majalisar na duba yiwuwar gayyato kamfanin domin yin gamsasshen bayani ga majalisar kan dalilin yin haka.
Mataimakin kakakin majalisar, ya umarci kwamitin sadarwa na majalisar ya aiwatar da bincike a kan koken, tare da kawo rahoto cikin mako biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotu a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya ta yanke wa wani malamin makaranta hukuncin ɗaurin shekara 15 saboda samunsa da laifin yi wa wata ƙaramar yarinya mai shekara takwas fyaɗe.
Ana zargin malamin makarantar da aikata laifin a shekarar 1999 a gidan su yarinyar.
A watan Agustan 2023 aka gurfanar da Oluwagbemi Alabi, mai shekara 45 a gaban kotun.
A lokacin da yarinya ta bayyana agabn kotu, ta ce malamin, wanda makwabcinsu ne kan riƙa tattaɓa jikinta a duk lokacin da ya je gidansu domin koya mata karatu.
''A lokacin ba na gane abin da yake nufi, har sai da wata rana ya haike mini, a falon gidanmu lokacin mahaifiyata ta yi tafiya zuwa Legas, ta bar ni a gida tare da 'yan uwana'', in ji wadda aka yi wa fyaɗe - wadda a yanzu matashiya ce.
Ta ci gaba da faɗa wa kotun cewa Alabi ya cire tufafinta bayan kammala aika-aikar, inda ya yi amfani da shi wajen goge jinin da ya zuba a jikinta, sannan ya jefar da shi.
''Daga nan ne na ruga da gudu zuwa makwabtanmu ina kuka, sun ɗauka tafiyar mahaifiyarmu ce ta sa ni kukan, amma ban gaya musu abin da ya faru ba.''
Ta ce daga nan ba ta sake zuwa makaranta ba, saboda ba za ta iya mayar da hankali kan karatun ba, ''domin kuwa a duk lokacin da na gan shi a aji tsoro ne yake kamani''.
Ta ce ta sake haɗuwa da shi a shekarar 2012 a shafin Facebook, lokacin da ya aike mata da saƙon neman zama abokinta a shafin, amma sai ta ƙi amincewa da shi.
“A shekarar 2023, sai ya ci gaba da damuna, inda ya ci gaba da turo min saƙonni da bidiyoyi na rashin daraja, yana tuna min mummunan lamarin da ya faru a baya tsakaninmu, wanda kuma ba zan iya jurewa ba, daga nan sai na ɗauki matakin shari'a a kansa,'' in ji ta.
A yayin da kotun ta nemi jin bahasin wanda ake zargin, ya amince da laifin da ake tuhumarsa da shi ba tare da wata fargaba ba.
Daga nan ne kuma alƙalin kotun, Mai shari'a Lekan Ogunmoye ya ce laifin da Alabi ya aikata na yin amfani da ƙarfi wajen haike wa ƙaramar yarinya babban laifi ne.
Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 15 domin ya girbi abin da ya shuka.