Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin ke nan wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne yake muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin ke nan wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne yake muku fatan alheri.
Kakakin sojin Isra'ila, Daniel Hagari, ya zargi Hamas da kashe sojarta mai suna Noa Marciano a Asibitin Al-Shifa.
Rundunar ta tabbatar da mutuwar kofur ɗin 'yar shekara 19 a makon da ya gabata. Ta bayyana a wani bidiyo da Hamas ta fitar.
Ya ce ba ita kaɗai aka kai asibitin ba, har ma ya nuna wani bidiyo da ya ce kyamarar CCTV ce ta ɗauka da ke nuna wasu mutanen da aka yi garkuwa da su lokacin da Hamas take kai su asibitin.
Tun ɗazu mun kawo rahoton cewa ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta kwashe jarirai bakwaini 31 daga Asibitin Al-Shifa saboda ƙarancin kayan kula da su.
An kwashe su ne tare da taimakaon Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce a kai su Asibitin Al-Helal Al-Emairati da ke kudancin Birnin Gaza, inda "suke samun kulawar gaggawa sashen ba da kulawa akai-akai".
Ƙungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran ta sanar da kama jirgin ruwan Isra'ila na dakon kaya a Tekun Maliya.
Sojojin Isra'ila sun ce jirgin ruwan ba na Isra'ila ba ne kuma babu wani ɗan Isra'ila a cikinsa.
Wakilin BBC ya ce "ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kama jirgin a matsayin ɗaya daga cikin ayyukan ta'addancin Iran".
Tun farkon fara rikicin Isra'ila da Hamas, Houthi ta kai wa Isra'ila hare-hare da makamai masu linzami.

Asalin hoton, Reuters
A 'yan mintunan da suka wuce, rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wani bidiyo da ta ce yana nuna "hanyar ƙarƙashin ƙasa mai tsawon mita 55, da faɗin mita 10 a Asibitin Al-Shifa" da ke Zirin Gaza.
A bidiyon, an nuna ƙofar shiga wani rami mai matattakala cikin ɓaraguzai a farfajiyar asibitin.
An ga kuma dakarun na tafiya a gefen wani rami da aka gina shi da kyau da ke kaiwa ga wata ƙofa.
"Hamas na amfani da irin wannan ƙofar don ta hana dakarun Isra'ila shiga hedikwatarta," a cewar rundunar sojin cikin wata sanarwa.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da "bincke don gano hanyar shiga ramin".
Isra'ila ta shafe makonni tana iƙirarin cewa Hamas na amfani da ƙarƙshin asibitin Al-Shifa a matsayin ofishin kitsa hare-hare - zargin da Hamas da kuma ma'aikatan asibitin suka musanta.
A makon da ya gabata, ita ma Amurka ta ce bayanan sirrinta sun nuna cewa Hamas na da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa a asibitin.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Isra'ila ta wallafa saƙo a dandalin X cewa an ba ta damar "ci gaba da kai hare-hare ta ƙasa da kuma yaƙi a Zirin Gaza".
Sai dai babu tabbas ko hakan na nufin faɗaɗa hare-haren har zuwa kudancin Gaza.
A farkon makon nan, dakarun Isra'ila sun watsa wa mazauna yankin Khan Younis da ke kudancin takardu ta sama ɗauke da saƙonnin gargaɗi cewa su bar inda suke saboda za a kawo hare-hare.
Isra'ilar ce ta bai wa mazauna Gaza umarnin su bar arewacin birnin zuwa kudu tun kafin ta fara kai samame ta ƙasa, tana mai cewa "za su tsira a can", amma ta ci gaba da kai hare-hare a can ɗin tun daga lokacin.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Mali ta ce ta gano wani makeken ƙabari a garin Kidal da ke arewa maso yammacin ƙasar wanda kuma ta ƙwace daga hannun 'yan tawayen Abzinawa.
Cikin wata sanarwa ranar Asabar da dare, rundunar ta ce "wannan babban ƙabarin ya nuna irin ƙazamin laifukan da 'yan ta'addan ke aikatawa, waɗanda ba su bin wani addini ko kuma doka".
Ta ce ta gano ƙabarin ne ranar Alhamis yayin wani "aikin tabbatar da tsaron Kidal", amma ba ta bayar da wani ƙarin bayani ba.
Ta ƙara da cewa tana bincike don "gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kotu".
A ranar 14 ga watan Nuwamba ne sojojin suka ƙwace Kidal, garin da 'yan tawayen Abzinawa ke da ƙarfi sosai wanda kuma suka ƙwace daga dakarun gwamnati tun 2014.
Sojojin sun ƙwato garin ne bayan dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya na Minusma sun bar sansaninsu da ke Kidal ranar 31 ga watan Oktoba a wani ɓangare na yarjejeniyar da aka cimma ta ficewarsu daga ƙasar nan da ƙarshen shekara.
Rundunar sojan Mali ta ƙwace mulki a 2020 bayan alaƙa tsakaninta da dakarun Minusma ta yi tsami, inda ta nemi su fice daga ƙasar a watan Yunin da ya gabata.

Asalin hoton, Kaduna Police Command
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta kama wani matashi da take zargi "ya ƙware" a satar akuyoyi a ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar.
Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa sun kama mutumin ne a ranar Asabar a ƙauyen Pasali Konu.
A cewarsa, matashin mai shekara 20 ɗan asalin ƙauyen Igwa ne kuma an kama shi "ɗauke da makamai masu haɗari da kuma takunkumi a fuskarsa".
"Wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa su biyu ne suka je ƙuyen don satar akuyoyi," a cewar ASP Hassan.
Ya ƙara da cewa wanda suke tare da matashin da ake zargin ya tsere bayan ya hangi dakarun 'yan sanda, amma suna ci gaba da neman sa.

Asalin hoton, WHO
Ƙungiyar agaji ta Red Crescent reshen Falasɗinu (PCRS) ta ce ta yi nasarar kwashe jarirai bakwaini 31 daga Asibitin Al-Shifa da ke arewacin Gaza ranar Lahadi.
An kwashe su ne tare da taimakon Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da kuma ofishin ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
WHO ta fitar da sanarwa tun da farko cewa akwai masu jinya 291 da har yanzu suke asibitin - cikinsu har da jariran bakwaini 32.
Ba a san dalilin da ya sa adadin jariran suka sha bamban ba tsakanin WHO da kuma PCRS, kuma BBC ba ta iya tabbatar da adadin ba.
Tun a jiya mun bayar da rahoto cewa ɗaruruwan mutane ne suka bar asibitin mafi girma a Gaza tun bayan da dakarun Isr'aila suka kutsa cikinsa don gudanar da abin da suka kira "samame na musamman kan Hamas".

Asalin hoton, Plateau State Government
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Najeriya ta soke nasarar da Gwamnan Filato Caleb Muftwang ya yi a zaɓen watan Maris na 2023.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ambato tawagar alƙalai mai mutum uku ta bayyana a ranar Lahadi cewa ba a bi ƙa'ida ba wajen tsayar Mista Muftwang a matsayin ɗan takarar gwamna a jam'iyyar PDP kamar yadda sashe na 285(2) na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Alƙalan sun ce ƙarar da ɗan takarar APC Nentawe Goshwe ya ɗaukaka ta yi nasara saboda batun tsayar da ɗan takara lamari ne da ya shafi lamurran kafin da kuma bayan zaɓe, saɓanin hukuncin da kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta bayar - inda ta bai wa Mista Muftwang nasara.
Tawagar alƙalan ta amince da mai ƙorafin (Goshwe) cewa gazawar PDP na gudanar da bin umarnin wata kotun Filato da ya ce a gudanar da sahihan tarukan jam'iyya a mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma jiha kafin tsayar da 'yan takara ya saɓa wa doka.
Wannan dalilin ne ya sa kotun ta yi watsi da hukuncin kotun farko a matsayin "wanda bai dace ba kuma ya saɓa da yi wa kowane ɓangare adalci ta hanyar sauraron hujja daga shaidun da aka kora daga shari'ar".
Kotun ta umarci hukumar zaɓe Inec ta ƙwace shaidar cin zaɓe daga hannun gwamnan mai-ci kuma ta bai wa Nentawe Goshwe na APC.

Asalin hoton, Nigerian Navy/Facebook
Rundunar sojin ruwan Najeriya da e yaki da masu satar ɗanyen mai, sun ce sun kama tare da lalata tataccen litar gas 15,775 a yankin Igbokoda na ƙaramar hukumar Ilaje da ke jihar Ondo a kudancin ƙasar.
Jaridar Punch a Najeriya ta ce sojojin sun yi kaman ne a ranar Lahadi, inda suka lalata man da suka ce zai kai na miliyoyin naira.
Babban jami'in tawagar sojojin, Commander Humphrey Nnaji ne ya bayyana haka ranar Lahadi.
Ya ce jami'an sojin sun samu bayanan sirri kan masu aikata laifin kafin su kai samamen.
Ya ƙara da cewa rundunar ta kuma samu nasarar ƙwato man da ake tacewa, tare da ƙwato wani kwale-kwale da ɗanyen mai a cikinsa.
Karas na daga cikin nau'ikan kayan marmari, da ke ƙunshe da tarin sinadarai masu yawa da ke taimaka wa lafiyar jikin ɗan'adam.
Daga cikin akwai sinadaran da ke kare ɗan'adam daga kamuwa daga cutar kansa, da inganta garkuwar jiki.
Haka nan kuma masana sun ce karas na ƙunshe da sinadaran da ke kare jiki daga cutar hawan jini da shanyewar ɓarin jiki, da kuma bugun jini ko na zuciya.
Ku kalli wannan bidiyo domin ganin tarin sinadaran da kasar ke ƙunshe da su.
Qatar na taka muhimmiyar rawa a yunƙurin tattaunawar sulhu don sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Kawo yanzu ta shiga tattaunawa da ta kai ga sakin mutum huɗu, ciki har da Amurkawa biyu, 'ya da mahaifiya, da kuma wasu tsofaffi mata 'ya Isra'ila guda biyu.
Qatar - mai ɗimbin arzikin albarkatun iskar Gas da ke yankin Gulf - ta kasance mafakar manyan shugabannin siyasar Hamas, da ke da ofishi a birnin Doha, tun shekarar 2012, da shugabanta Ismail Haniyeh ke jagoranta.
A ofishin ne jami'an ƙungiyar ke zama da jami'an diplomasiyya daga ma'aikatar harkokin wajen Qatar domin tattauna yadda za a saki mutanen.
Tun da farko, firaminstan Qatar, Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, ya shaida wa taron manema labarai cewa "'yan matsaloli ƙalilan ne suka rage a kammala tattaunawar, idan aka kwatanta da manyan, "suna da wahala, sannan suna da saukin sha'ani."
Sai dai har yanzu ba a ga ma'anar abinda yake nufi da 'saukin kai' ba.

Asalin hoton, Oyo State Government
Wani matashi mai suna Prince Adebayo Ayodeji Temitope, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ya yi yunƙurin kafa tarihin mutumin da ya fi daɗewa yana girki a duniya, bayan da ya yi girkin sa'o'i 200.
Mista Temitope ya fara girkin ne da misalin ƙarfe 6:31 na maraicen ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba, inda ya ƙare a ranar 18 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 2:31 na dare.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Oyo ta fitar, ta ce tana taya matashin murnar yin wannan bajinta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A yanzu ana jiran mahukuntan kundin tarihi na 'Guinness World Record' su gama tantance ƙoƙarin matashin domin tabbatar masa da tarihin.
A ranar 7 ga watan Nuwamba ne, Kundin Bajintar ya bayyana cewa wani ɗan Ireland, Alan Fisher ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi daɗewa yana girki a duniya bayan girkin sa'o'i 119 da minti 57.
Alan Fisher ya doke tarihin da Hilda Baci 'yar Najeriya ta kafa cikin watan Yuni, bayan da ta shafe sa'a 93 da mintuna 11 tana girki.

Asalin hoton, X/Hilda Baci

Asalin hoton, WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta ce akwai marasa lafiya 291 da ke cikin tsananin jinya a asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza, bayan a jiya ɗaruruwan Falasɗinawa sun fice daga asibitin a ƙafa.
Kashi biyu cikin uku na marasa lafiyar jarirai ne da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda WHO ɗin ta bayyana.
Daga cikin marasa lafiyar, WHO ta ce suna ɗauke da munanan raunukan karaya, da waɗanda aka yanke musu ƙafa ko hannu, da masu raunuka a kansu da kirji da raunukan da suka danganci cikin jiki.
Likitoci 25 ne suka rage a asibitin na al-Shifa.
A jiya ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce akwai kimanin marasa lafiya 120 da suka rage a asibitin
Sai dai BBC ba ta iya tantance hakiƙanin waɗannan alƙaluma ba.