Fiye da mutum 20 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Neja

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Muna nan tafe da wasu sabbin rahotannin daga sassan duniya gobe da safe.

    Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau.

    Kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Biden ya jinjina wa Tinubu kan shugabancin Ecowas

    d

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yaba wa takwaransa na Najeriya Bola Tinubu kan ƙarfin shugabanci a matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas.

    Mista Biden ya jinjina wa Tinubu a ƙoƙarinsa martaba tare da kare dimokraɗiyya a jamhuriyar Nijar da yankin Afirka ta Yamma.

    Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Shugaban na Amurka ya gana da Tinubu a gefen taron ƙungiyar G-20 ta kasashe masu karfin masana'antu da aka gudanar a birnin Derkhi na kasar Indiya.

    An yi ganarwa ne domin jaddada goyon bayan Amurka ga Najeriya, kamar yadda ofishin jakadancin Amurkan a Najeriya ya bayana.

    “Shugaba Bide ya jinjina wa gwamnatin Tinubu bisa matakan da ta ɗauka na gudanar da sauye-sauyen tatalin arziki, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa jajircewar da ya nuna a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas wajen kare tare da tsare dimokradiyya a Nijar da ma yankin yammacin Afirka," kamar yadda fadar gwamnatin Amurka ta 'White House' ta bayyana .

    Ta kara da cewa ''gayyatar da aka yi wa Najeriya zuwa taron G-20 alama ce irin martabar da ƙasar ke da ita a idon duniya, a matsayinta na giwar dimokraɗiyya da tattalin arziki a duniya".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Tawagar gwamnatin Isra'ila ta isa Saudiyya karon farko cikin tsawon lokaci

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko tawagar gwamnatin Isra'ila ta isa Saudiyya, duk cewa ƙasashen biyu ba su da wata hulɗar diflomasiyya tsakaninsu.

    Tawagar - ƙarƙashin jagorancin shugaban kula da kayan tarihi na Isra'ila - ta shiga Saudiyya ne domin halartar taron hukumar kula da ilimi da al'adu ta MDD wato Unesco.

    Amincewa da shigar wakilin Isra'ila cikin Saudiyya na ɗaga cikin sharuɗɗan da aka gindaya wa ƙasar kafin ba ta damar karɓar baƙuncin taron na Unesco.

    Ana ganin wannan kuma wata dama ce na ƙoƙarin farfaɗo da hulɗa tsakanin ƙasashen biyu

  4. Sojojin mulkin Nijar sun zargi Faransa da yunƙurin afka wa ƙasar

    s

    Asalin hoton, AFP

    Sojojin mulkin Nijar sun zargi Faransa haɗa kai da ƙungiyar Ecowas don shirya ƙaddamar da mamayar soji a ƙasar

    Hakan na zuwa ne, yayin da sojojin suka kasa cimma matsaya da ƙungiyar Ecowas kan rikicin siyasar ƙasar.

    Zargin ka iya tunzura dubban masu goyon bayan mulkin sojin kasar, waɗanda ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan sojojin tare da nuna adawarsu ga ƙasar Faransa.

    Mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojin Kanal Manjo Amadou Abdramane ya ce 'suna zargin gwamnatin Faransa da shirya dakaru, da kayan yaƙi a wasu makwabatn ƙasar da ke Afirka ta yamma domin afka wa ƙasar.

    "Faransa na ci gaba da girke dakarunta a ƙasashe da dama da ke makabtaka da mu, a shirin da take yi na na kawo mana hari tare da mamaye ƙasarmu, wanda shirin haɗin gwiwa ne da kungiyar Ecowas,"kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya karanta a gidan talbijin na ƙasar da maraicen ranar Asabar.

    Sojojin sun yi iƙirarin cewa faransa ta girke jiragen saman yaƙi, da masu saukar ungulu, da motocin sulke 40 a ƙasashen Cote d'Ivoire da Benin.

    Haka kuma sun yi zargin cewa wani ƙaton jirgin ruwa zai kai manyan makamai masu yawa da sauran kayan yaƙi zuwa ƙasshen Senegal da Cote d'Ivoire da kuma Benin.

    Ita dai Faransa na ci gaba da tsayuka a kan matsayinta na goyon bayan hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, tare da ƙin amincewa da gwamnatin mulkin sojin.

    Gwamnatin Faransa ta ƙi amincewa da buƙatar sojojin na janye dakarunta tare da jakadanta da ke ƙasar, a yayin da sojojin suka ce dakarun na Faransa a yanzu na zaune ne a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    Faransa da Amurka na da sojoji kusan 2,600 a Nijar, a wani ɓangare na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

    A makon da ya gabata ne Amurka ta sanar da sauya wa wasu dakarunta da ke Yamai matsuguni zuwa sansanin sojin samnat da ke Agadez.

    Daruruwan masu goyon bayan juyin mulki a Nijar ne ke taruwa a sansanin sojin Faransa da ke Yamai, suna buƙatar sojojin na Faransa da su fice daga ƙasar.

  5. Girgizar ƙasar Moroko: 'Masu aikin ceto na fuskantar cikas'

  6. Brazil ta karɓi ragamar shugabancin ƙungiyar G-20

    g

    Firaministan Indiya Narendra Modi ya miƙa ragamar shugabancin ƙungiyar G-20 ta ƙasashe masu ƙarfin tatalin arziki, ga ƙasar Brazil bayan kammala taron ƙungiyar da aka gudanar a birnin Delhi a ƙasar Indiya.

    Cikin watan Nuwamba mai zuwa ne Brazil za ta fara shugabancin ƙungiyar a hukumance.

    Mista Modi ya ce "har zuwa watan Nuwamba Indaiya ce za ta jagoranci G-20, don haka har yanzu muna da sauran wata biyu da rabi a jagorancin ƙungiyar".

    A lokacin taron ƙungiyar Mista Modi ya taɓo batun ƙara adadin ƙasashen da ke cikin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

    Yana mai cewa lokaci ya yi da za a gudanar da sauye-sauye a kwamitin.

    Ƙasashe biyar ne ke da kujerar dindindin a kwamtin tsaron, waɗanda suka haɗar da Amurka da Rasha da Faransa da Birtaniya da kuma China.

    Indiya ta daɗe tana kiraye-kirayen ƙara adadin mambobin kwamitin da ke da kujerun na dindindin.

  7. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Haruna Shehu Tangaza tare da Haruna Ibrahim Kakangi ne suka gabatar da shirin na wannan mako.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  8. Amfanin tazargade ga lafiyar ɗan'adam

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Yayin da mutane da dama a Najeriya ke fama da zazzaɓin cutar Maleriya kasancewar lokacin damina, likitocin gargajiya na shawartar mutane wajen amfani da tazargade.

    BBC ta tattauna da Zainab Ujudu Shariff, wata mai haɗa maganin gargajiya a ƙasar inda ta yi bayanin hanyar gargajiya ta amfani da tazargade wajen magance cutar Maleriya.

    Zainab ta ce a kimiyance ana amfani da sinadarin tazargade wajen haɗa maganin Maleriya na Bature.

    "WHO ta ce duk itace da aka saba ana amfani da shi tsawon shekara 200,000 to a yadda yana magani", in ji Zainab.

    Ta ƙara da cewa baya ga Maleriya akwai cututtuka masu yawa da tazargade ke warkarwa.

  9. Amsoshin Takardunku

    Amsoshin Takardunku tare da Ibrahim Yusuf Muhammad

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin auraron shirin
  10. Fiye da mutum 20 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Neja

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 24 galibinsu manoma ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka ɓace a lokacin da wani ƙwale-kwale ɗauke da fasinjoji ya kife a garin Gbajibo, a ƙaramar hukumar Mokwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

    Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.

    Rahotonni na cewa fasinjojin kwale-kwalen sun fito ne daga garuruwan Gbajibo da Ekwa da Yankeiade.

    Jaridar Daily a Najeriya ta ambato shugaban ƙaramar hukumar Mokwa Jibrin Abdullahi Muregi na cewa an kuɓutar da gawarwaki 21.

    Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce suna tattara alƙaluma domin sanin haƙiƙanin adadin mutanen da lamarin ya shafa.

    Hatsarin na zuwa ne kwana biyu bayan da wani kwale-kwale ya kife ɗauke da fasinjoji ciki har da mata da ƙananan yara ya kife a Yola ta jihar Adamawa, lamarin da ya haddasa asarar rayuka.

  11. Jamus ta kori Hansi Flick bayan kasa taka rawar gani

  12. Tinubu ya wuce Dubai daga Indiya

    d

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai ya da zango a Dubai daga taron G-20 da yake halarta a Indiya, domin ganawa da jagororin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban na Najeriya ta wallafa shafinta na Twitter ta ce ganawar ci gaba ne na tataunawar jakadan ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa ya yi da shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja, domin magance wasu matsaloli na tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Sanarwar ta kuma shugaba Tinubu zai yi ƙoƙarin magance tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Shugaban na Najeriya ya halarci ƙungiyar taron G-20, ta ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki na duniya bisa gayyatar firaministan Indiya, wanda ya jagoranci taron.

    Shugaban zai koma Najeriya da zarar ya kammala ganawa da jagogin na UAE, kamar yadda sanarwar ta bayyana

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Ko kun san alamun kansar mama?

    g

    Mutane suna jin an ce kansa ko cutar Daji, kowa yasan cuta ce da ake shan wuya kuma ba a warkewa idan ana fama da ita.

    Amma tun karshen shekarun 1970, adadin mutanen da ke tsira daga wannan cuta ke ninkawa sau uku, dalili kuma shi ne da yawan marasa lafiyar akan iya cetonsu daga cutar da zarar an gano suna da ita a kan lokaci.

    Matsalar ita ce ba mu fiye bai wa likitoci muhimmanci ba, domin kuwa sukan iya gano alamun cutar tun da wuri matuƙar an tuntube su a kan lokaci.

    A cewar wani bincike da cibiyar binciken kansa ta Birtaniya ta yi, an gwada rabin mutanen Birtaniya an gano wasu na ɗauke da alamun cutar amma kuma kashi biyu ne kacal ake zargin sun kamu da ita.

    Katrina Whittaker, wata mai bincike a Jami'ar Landan, wadda kuma ita ce ta jagoranci wannan binciken, ta ce: "bai kamata mutane su riƙa tsammanin muna son sanya musu fargaba da tsoro ba ne a ransu, ya kamata mutane su riƙa sanin yanayin da suke ciki na lafiya, bai kamata su riƙa jin kunyar zuwa ganin likita ba."

    Ga wasu alamu 8 da an ji su an san cutar kansa ta samu:

    1- Ramewa maras dlili

    2- Yawan Zazzaɓi mara ƙaƙƙautawa

    3- Yawan laulayi

    4- Sauyin launin fata ga masu kansar fata

    5- Yawan ciwon ciki ga masu kansan da ke alka da ciki (Hanji, Tumbi, mahaifa, ƙoda, hanta da sauransu)

    6- Ƙurjin da ke komawa da ke gyambo

    7- Zubar da Jini ga masu kansar jini ko kansar bakin mahaifa

    8-Tari maras warkewa ga masu kansar huhu

  14. Yadda girgizar ƙasa ta lalata wani masallaci mai tarihi a Marrakesh

    Fitaccen babban masallacin nan na birnin Marrakesh Jemaa el-Fna - wani waje na tarihi da muka faɗa a bayananmu na baya da girgizar ƙasar ranar Juma'a ta haifar.

    Akwai wuraren da ke jan hankalin masu yawo buɗe idanu daga gine-gine da kuma wuraren shan shayi da dama a yankin wajen da masallacin yake.

    Za ka iya ganin sauyin da aka samu a masallacin kafin da kuma bayan wannan annoba.

    B
  15. Aƙalla mutum 40 sun mutu a wani harin jirgi da aka kai kasuwa

    f

    Asalin hoton, Sudan M

    Aƙalla mutum 40 ne suka mutu a wani harin jirgin sama da aka kai wata kasuwa da ke kudancin birnin Khartoum, kamar yadda wata sanarwar da hukumomi suka fitar a ranar Lahadi.

    Wannan ne adadin fararen hula mafi yawa da aka kashe a hari guda tun bayan fara yaƙin Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu yayin da rikicin ke ƙara yawa a yankin da mutane ke zaune.

  16. Yadda 'yan wasan Moroko ke ba da taimakon jini ga waɗanda girgizar ƙasa ta shafa

    'Yan wasan tawagar kwallon ƙafa ta Moroko sun bayar da agajin jini ga waɗanda girgizar ƙasa ta shafa, kamar yadda tawagar ta wallafa a shafinta na X.

    Wannan ya biyo bayan buƙatar da hukumomin lafiya na ƙasar suka bayyana ta neman agajin jini ga waɗanda suke buƙata.

    Za ka iya kallom wannan bidiyo da ke ƙasa:

    Bayanan bidiyo, Latsa nan domin ganin yadda 'yan wasan kwallon kafar Moroko ke ba da agajin jini ga waɗanda girgizar ƙasa ta shafa.
  17. 'Muna fama da ƙarancin ungozoma 20,000 a Iran'

    G

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'in da Ma'aikatar Lafiya ta Iran ke tuntuɓa ya ce ƙasar baƙatar kimanin ungozoma dubu 12 a sashen aiki da kuma kimanin dubu takwas a sashen lafiya.

    Shahla Khosravi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasar cewa a cewar alƙaluman yawan matasa da iyalai da ake da su, sun nuna akwai buƙatar ungozoma ɗaya a kan masu ciki biyu, don haka a hasashenmu muna buƙatar ƙarin ungozoma 20,0000.

  18. 'Matata da 'ya'yana huɗu sun mutu a girgizar ƙasa, na rasa komai'

    H

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamar yadda muka kawo muku rahotannin abubuwan da suke faruwa a Moroko sakamakon girgizar ƙasa da ta faru a tsaunin Atlas Moutain - da yawa mutane sun rasa masoyansu.

    Lahcen ya shiga ciki mummunan tashin hankali bayan matarsa da 'ya'yansa huɗu sun mutu a wannan musiba.

    Ya shaida wa AFP cewa "Na yi asarar komai. Babu abin da zan iya yi a yanzu, so nake na bar duniyar baki ɗaya saboda baƙin ciki."

    Ana ta gina kabarurruka a saman tsaunukan domin rufe gawarwaki.

    Hasna, wadda itama mazauniyar yankin ce ta ce "duka ƙauyen na makokin 'yan'yansu da suka mutu".

  19. Mummunan faɗa ya ɓarke a yankin Awdheegle da ke kuɗancin Somalia

    b

    Mayaƙan Al-Shabab sun ƙaddamar da wani yaƙi a safiyar nan a yankin Awdheegle da le gundumar Lower Shabelle a kudancin Somaliya.

    Maharan sun kai hare-hare ta fuskoki da yawa na birnin, yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da yunkurin kare su.

    Mutanen da ke yankin Awdheegle sun shaida wa BBC cewa faɗan ya ɓarke ne da misalin ƙarfe huɗu na safiya kuma an shafe awanni ana gwabzawa.

    Mazauna yankin sun ce sun riƙa jin harbin bindiga ta ko wanne bangare da ke yaƙi da juna.

    Gwamnan gundumar Lower Shabelle, Mohamed Ibrahim Barre, ya shaida wa BBC dakarun gwamnati sun durƙusar da gungun maharan, inda ya ce duka ɓangarorin sun yi rashin mayaƙa, amma har yanzu ba su da cikakkun bayanai kan abin da ya faru.

  20. MDD ta yi kira a ɗauki matakin ba sani ba sabo kan matsalar ɗumamar yanayi a duniya

    b

    Wasu bayanan Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce matsalar sauyin yanayi da ɗumamar yanayi na buƙatar ɗaukar matakin gaggawa na ba sani ba sabo kan mutanen duniya, ciki har da yadda muke tafiye-tafiye da yadda muke cin abinci da kuma yadda muke amfani da makamashi.

    Wannan ne bayanan bibiya na farko na duniya daga ƙasashe a wani yunƙuri na rage amfani da makamashi mai bata muhalli tun bayan yarjejeniyar da aka cimma a Paris a 2015.

    Wannan rahoto ya ce duk da dai an samu ci gaba sosai, amma za a iya cimma abin da ya fi haka idan aka sake zage damtse.