'Kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kaiwa naira miliyan biyar'
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge and Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Muna nan tafe da wasu sabbin rahotannin daga sassan duniya gobe da safe.
Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo a yau.
Kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya
Wike ya musanta gayyatar EFCC ko ICPC don bincikar tsohon ministan Abuja
Asalin hoton, RVGH PRESS
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙaryata labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa yana shirin gayyato hukumomin EFCC da ICPC masu yaƙi da rashawa domin bincikar tsohon ministan Abuja Muhammad Bello dangane da wasu kura-kurai a wasu kwangilolin da tsohon ministan ya bayar da wasu abubuwa.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ma'aikatar birnin tarayya Anthony Ogunleye ya fitar, ya ce waɗannan labarai ba su da tushe balle makama.
"A lokacin ziyarar duba ayyuka da minista ya kai wasu sassan birnin, haƙiƙa ya nuna damuwa da fushi kan wasu kura-kurai da ya gani a wasu ayyukan da aka bayar, to amma babu inda ya ambaci cewa zai ɗauki matakin gayyatar EFCC ko ICPC don bincikar wani jami'i ko tsohon a ma'aikatar", in ji sanarwa.
Adadin waɗanda suka mutu a harin Mali ya zarta 100
Asalin hoton, Reuters
Rahotonni daga Mali na cewa adadin waɗanda suka mutu sakamakon harin da aka kai arewa maso gabashin yankin Gao ya zarta 100.
An tsamo wasu ƙarin gawarwaki a kogin Nijar, yayin da fafaren hula da dama suka jikkata inda aka kai su asibitocin Bamba da Gao domin yi musu magani.
A ranar Alhamis ne ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta kai hari kan wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji masu yawa.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa jirgin na ɗauke da fasinjoji kusan 600 waɗanda suka taso daga Gao zuwa Mopti da ke tsakiyar ƙasar.
Da yawa daga cikin waɗanda suka rasun, sun mutu ne sanadiyyar harbi a lokacin harin, ko kuma sanadiyyar nutsewa da suka yi a kogi, lokacin da suka yi yunƙurin tsira da rayukansu.
Firaministan Gabon ya naɗa ministoci
Asalin hoton, Getty Images
Sabon firaministan Raymond NDONG Sima ya sanar da naɗin sabuwar majalisar ministocinsa.
Mambobin jam'iyyun adawa da wasu tsoffin hadiman hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo da sojoji na daga cikin ministocin sabuwar gwamnatin.
Sabuwar majalisar ministocin ne za ta tafiyar da gwamnati har zuwa lokacin da sojojin za su miƙa mulki ga farar hula.
Ba a dai san tsawon lokaci sojojin za su ɗauka kafin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyya ba, to amma firaministan ya shaida wa BBC cewa yana ganin cikin shekara biyu masu zuwa.
A lokacin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Brice Oligui Nguema, ya ce zai kafa kafa gwamnatin da za ta yi aikin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokradiyya, tare da sakin fursunonin da aka ɗauka saboda siyasa ko addini a ƙasar.
Janar Nguema ya kuma sha alwashin sauya kundin tsarin mulkin ƙasar tare da kafa taftataccen tsarin zaɓe dai riƙa gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar.
A cikin mako ne ya saki hamɓararen shugaban ƙasar Ali Bongo, tare da ba shi damar fita ƙasashen waje domin duba lafiyarsa.
Ya kuma saki wasu daga cikin fursunonin siyasa da hamɓararen shugaban ƙasar Ali Bongo ya ɗaure kwanaki bayan rantsar da shi.
A watan da ya gabata ne Sojoji suka hamɓarar da Bongo jim kaɗan bayan hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.
'Ya kamata Birtaniya ta nemi afuwa kan cinikin bayi'
Moroko ta ayyana makokin kwana uku
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Sarki Mohamed VI na Moroko
Fadar masarautar Moroko ta ayyana makokin kwana uku a ƙasar, don nuna alhinin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar da ta afka wa ƙasar cikin daren jira.
Ƙasar ta ɗauki matakin ne bayan Sarki Mohamed VI ya gana da masu ruwa da tsaki a ƙasar kan bala'in.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar MAP ya ruwaito cewa za sassauto da tutocin ƙasar ƙasa a yain makokin.
Girgizar ƙasar ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 1,000.
Rundunar sojin ƙasar za ta aike da tawagar masu ceto zuwa yankunan da lamarin ya faru domin samar da tsaftataccen ruwan sha da abinci da barguna ga mutanen da lamarin ya shafa.
Mutum 15 sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Adamawa
Asalin hoton, fd
Aƙalla mutum 15 ne suka mutu bayan da wani kwale-kale ya kife a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Lamarin ya faru ne da maraicen ranar Juma'a lokacin da kwale-kwalen - ɗauke da fasinjoji 23 ciki har da manoma da 'yan kasuwa da ƙananan yara - ya taso daga ƙauyen Rugange zuwa garin Yola a kogin Njuwa.
Rahotonni sun ambato wani jami'in ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross na cewa an tsamo gawarwaki hudu a wurin da lamarin ya faru, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Ya ce iska mai ƙarfi ce ta tilasta wa ruwa shiga cikin kwale-kwalen, wanda nan take ya kife da fasinjojin da ke cikinsa.
Ya yi kira hukumomin jihar da su samar wa al'ummar ƙauyen Rugange - waɗanda ke fuskantar matsalar ambaliya duk shekara - jirjin ruwa mai amfani da inji.
Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ADSEMA, Muhammad Amin Sulaiman, ya ce an kuɓutar da mutum bakwai yayin ake ci gaba da neman bakwai.
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Girgizar ƙasar Moroko: Tinubu ya jajanta wa Sarki Mohammed VI
Asalin hoton, Nigerian Presidency
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa sakon jaje ga Sarki Mohammed VI na Moroko kan mummunar girgizar ƙasar da ta yi sanadiyyar rayuka da dama a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka jikkata sakamakon bala'in, tare da fatan samun sauƙi a gare su.
Tinubu ya ce al'ummar Najeriya na taya gwamnati da al'ummar Moroko alhinin wannan mummunan abu da ya faru a ƙasar.
Moroko ta gamu da iftila'in girgizar ƙasa ranar Juma'a da daddare, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 1000.
'Kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kaiwa naira miliyan biyar'
Asalin hoton, NAHCON
Hukumar Alhazan Najeriya, ta shawarci maniyyata aikin hajjin shekara mai mai zuwa ta 2024, su ajiye naira miliyan huɗu da rabi a matsayin adashin gata, kafin lokacin da za a fito da hakikanin kuɗin hajjin shekarar.
Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ne ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.
Kwamishinan kuɗi da tsare-tsare na hukumar Alhaji Nura Hassan Yakasai ya shaida wa BBC cewa matakin na zuwa ne bayan da suka yi la'akari da tashin farashin dala.
Ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa hukumar ta yanke shawar ajiye naira miliyan 4.5 a matsayin adashin gata, "idan akwai ciko ma ba zai yi yawa ba".
Ya ƙara da cewa "Kashi 98 na kuɗaɗen da ake buƙata wajen biyan aikin hajji ana yi ne da dala" dan haka ne suka ɗauki matakin shawartar maniyya su biya wannan kuɗi a matsayin adashin gata.
Ya ce dalilin da ya sa hukumar ta yanke wanna shawarar shi ne kada cikon ya yi wa maniyyata yawa a lokacin biyan kudin aikin hajjin.
Ga cikakkiyar hirar a cikin shirinmu na Gane Mini Hanya tare da Usman Minjibir
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Girgizar ƙasar Moroko - Adadin waɗanda suka mutum ya kai 1,037
Har yanzu ana ci gaba da gano gawarwakin da waɗanda suka rasa rayukansu a girgizar ƙasar Moroko.
Hukumomi sun ce yanayin wajen da aka samu wannan girgizar ƙasa ba zai bari a iya gano mutum nawa ne suka mutu ba har nan da kwanaki.
Amma sun tabbatar da cewa za a samu ƙarin adadin waɗanda abin ya rutsa da su.
Aikin ceto na yuwa saboda wurin cike yake da duwatsu.
Mutane da dama sun baro gidajensu sun komo kan tituna domin gudun abin da zai iya biyo baya.
Ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi wa Moroko cikin hotuna
Asalin hoton, bbc
Asalin hoton, Calara
Asalin hoton, AFP
Asalin hoton, Umar Imzilan
Asalin hoton, Umar Imzilan
Asalin hoton, gv
Taron G-20: Tinubu ya yaba wa Firaministan Indiya
Asalin hoton, Bola Tinubu/Twitter
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya halarci taron ne bisa gayyatar Narendra Modi
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Firaiministan India Nerandra Modi game da karɓar baƙunci taron G20 ya kuma nuna jin daɗinsa game da gayyatarsa da ya yi.
"A matsayina na shugaban ƙasar da tafi shahara tsakanin kasashen baƙaƙen fata, ni ma zan bi sawun sauran shugabannin ƙasashen duniya wajen tabbatar goben ƙasar mu Najeriya ta zama mai haske - tare da duka sauran ƙasashen nahiyar Afrika," in ji Tinubu.
"Kuma a shirye nake wajen mun sake ƙarfafa tsare-tsarenmu kan dimokraɗiyya da ci gaba da yan ƙasarmu mzaune waje da kuma yawan al'umarmu."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Tarihin girgizar ƙasa mafi muni a gwamman shekaru
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasar Morocco ta sha ganin girgizar ƙasar a baya, ciki har da wadda aka yi a 2004.
Girgizar ƙasar da ta faru a hital-Hoceimain da ke arewa maso gabashin Moroko a wannan lokacin ta kashe mutum 628.
A 1960 an samu wata girgizar a Agadire inda ta ƙashe mutum 12,000.
Wannan kan iya bayar da haske kan yawan mutanen da abin ya shafa muke gani a wannan da ta faru a yau.
Wannan bala'in girgizar ƙasar da ta faru a ƙasar ta auku ne a tsakiyar yankin da ke da duwatsu da yawa, inda mafi yawa ƙauye ne kuma yana da wuyar shiga.
Zai ɗauki kwanaki gabanin a iya ganon adadin barnar da girgizar ƙasar da yi.
Gwamnatin Najeriya za ta gina gidaje 1,000 a jihohin arewa bakwai – Shettima
Asalin hoton, FG
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 1,000 a jihohin arewacin Najeriya shida sai kuma Benue a matsayin wani shiri na rage raɗaɗin waɗanda rikici ya shafa a yankin.
Jihohin sun haɗa da Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Naija sai kuma Benue.
Shettima ya bayyana hakan ne a Borno lokacin da ya wakilci Shugaban ƙasar Bola Tinubu yayin buɗe wasu ayyuka 77 cikin kwana 100 farko na wannan lokaci da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi.
Wasu daga cikin ayyukan da Shettima ya buɗe akwai makarantar Shuwari da wata cibiyar lafiya, akwai makarantar Alikaramti da ta Gamboru dukkansu a cikin garin Maiduguri.
Girgizar ƙasa ta yi wa birnin Marrakesh barna mai yawa
Asalin hoton, Reuters
Girgizar ƙasar da aka samu a Moroko da ta kashe masa da mutum 600 ta lalata birnin Marrakesh.
Birnin da na tarihi ne da yake cikin jerin wuraren masu muhimmanci da Unesco.
Wani bidiyo da ba a iya tantancewa ba da aka wallafa a shafin X ya nuna yadda gine-ginen birnin suka lalace, wasu kuma gidajen sun tsattsage.
Asalin hoton, Reuters
Wasu gine-gine masu cike da tarihi kuma sun zube baki ɗaya, kamar yadda wani mutum ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Mutane da yawa sun ce sun gwammace su koma waje su zauna domin gudun abin da ka iya faruwa bayan girgizar ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Neymar ya karya tahirin Pele na yawan cin kwallo a Brazil
Asalin hoton, Getty Images
Neymar ya karya tahirin Pele na yawan cin kwallo a Brazil, bayan ɗan wasan ya ci kwallo biyu a wasan da suka yi nasara kan Bolivia.
Dan wasan mai shekara 31 wanda ya je wasan share fagen gasar kofin duniya da kwallo 77 kamar, ya kuma zubar da bugun fenariti gabanin ya ci kwallo biyu a minti 45 na biyu a wasansa na 125 a ƙasar.
"Ban taba kawo wa zan iya haɗa wannan tarihi ba. Ban fi Pele ba ko wani ɗan wasa a tawagar Brazil ba," in ji Neymar.
Mata ta ce kwallo 122 a wasa 189 da ta bugawa tawagar Brazil ta mata.
Pele da ya mutu a watan Disamba a shekara 82 ya ci kwallo 77 a wasa 99 da ya buga tsakanin shekarun 1957 zuwa 1971.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin kwallon da ba a taɓa yin irinsu ba a fagen sannan ƙwallon kafa a duniya.
Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutum ya kai 820 a girgizar ƙasar da ta auku a Moroko
Akalla mutum 820 ne suka mutu ya zuwa yanzu a girgizar ƙasar da ta faru a Moroco, kamar yadda gidan talabijin na ƙasar ya ambato ma'aikatar cikin gida na cewa.
Garuruwa da dama ne wannan girgizar ƙasar ta shafa.
Tun da farko mazauna birnin Marrakesh sun ce an samu katsewar lantarki.
Shugabannin ƙasashen Rasha da China ba za su halarci taron G20 ba.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce abubuwa sun yi masa yawa, sai dai ana ganin kawai yana son kaucewa taron ne saboda gudun kada Kotun Duniya ICC ta kama shi, wadda a farkon shekarar ne ta ba da umarnin kama Putin kan zarginsa da aikata laifukan yaƙi a Ukraine.
Ana ganin za a tattauna matsalar wannan yaƙi a yayin taron na G20.
Rasha ta bayyana abin da ake yi a Ukraine wani aikin soji na musamman maimakon mamayar ko kuma yaƙi.
Xi Jinping na zuwa kowanne taron G20 tun da ya fara shugabanci a China, sai wannan karon ne ya gaza halartar wannan, abin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce ka iya zama cin fuska ga India.
China dai babbar ƙawa ce ga Rasha kuma har yau ba ta ce uffan ba game da mamayar da ta yi a Ukraine.
Manyan takunkuman da ƙasashen yamma suka sanya wa Rasha ya ƙara ƙarfin cinikayyar da ke tsakaninta da China da kashi 30.
Kotu ta bai wa Abubakar Kusada kujerar majalisar wakilai a Katsina
Asalin hoton, Facebook
Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen 'yan majalisar tarayya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta soke zaɓen Dalha Ismail Kusada a matsayin ɗan majalisar wakilai.
A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a O. Ogunfowora ta ce Abubakar Yahaya Kusada na APC ne ya lashe zaɓen na watan Fabrairu.
Haka nan, alƙalan sun ayyana Abubakar a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓun Kankia/Ingawa/Kusada.
Kazalika, kotun ta umarci Dalha da hukumar zaɓe ta Inec - waɗanda ake ƙara - su biya Abubakar kuɗi naira 200,000.
Da ma Abubakar ne ke riƙe da kujerar kafin Inec ta sanar da kayen da ya sha jim kaɗan kammala zaɓen, kuma tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina.
Sai dai har yanzu Dalha Kusada na da damar ƙalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.