Kotu ta yi watsi da ƙarar Atiku da Peter Obi

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Labaran ƙarya da ake yaɗawa a kan alƙalan kotun zaɓen shugaban Najeriya

  2. Sai da safe

    Nan muka kawo ƙarshen labaran namu na yau.

    Buhari Muhammad Fagge ke fatan mu kwana lafiya.

  3. An yi harbe-harbe a iyakar Pakistan da Afghanistan

    BBC

    An samu harbe-harbe tsakanin dakarun da ke aiki kan iyakar Pakistan da Afghanistan.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wata majiya daga dakarun Pakistan na cewa an yi harbe-harben.

    Mutanen yankin sun ce sun ji ƙarar harbi a iyakar Torkham kuma mutane sun yi ta gudu domin tsira da rayuwarsu.

    Jami'an da aka kai yankin aiki da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce an yi harbe-harben amma babu wanda ya mutu a wajen.

  4. 'Yan sandan Isra'ila sun ce an jikkata mutum biyu a wani hari kusa da Ƙudus

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sandan Isra'ila sun ce mutane biyu ne suka jikkata – wani dan Isra'ila da kuma wani dan yawon bude ido - a wani harin wuka da aka kai a kusa da tsohon birnin Kudus.

    Rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ya kai harin wani Bafalasdine ne mai shekaru sha bakwai da haihuwa. An kama shi ne yayin da ya ke neman tsewa ‘yan sanda.

    Wannan dai shi ne lamari na baya-bayan nan a rikicin da ya kara muni cikin shekara daya da rabi da ta gabata.

    Fiye da Falasdinawa dari biyu - wadanda suka hada da masu fafutuka da fararen hula - aka kashe a wannan shekaran; da kuma Isra'ilawa talatin - kusan dukkaninsu fararen hula amma har da sojoji uku.

  5. Kotu ta kori ƙarar Atiku da Peter Obi

    r

    Asalin hoton, gt

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta kori ƙarar Ɗan takarar jam'iyya hamayya ta PDP Atiku Abubakar, da ke ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC.

    Gabanin wannan sai da kotun ta fara watsi da ƙarar Peter Obi ɗan takarar jam'iyyar LP wanda ya zo na uku a zaɓen 2023.

    An shafe yini guda ana sauraren hukunci kan wannan ƙararraki.

    Tuni dai Shugaba Tinubu ya yi maraba da wannan hukunci, cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin 'yaɗa labarai Ajuri Ngelale.

  6. Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Tinubu

  7. Mutum 31 sun mutu a ambaliyar ruwa a Brazil

    g

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla mutane 31 ne aka tabbatar da sun mutu a wata ambaliyar ruwa mafi muni da aka taɓa gani a kudancin Brazil.

    A jihar Rio Grande do Sul, masu aikin ceto sun ce suna ci gaba da kokarin isa ga iyalai da suka makale a saman rufin gidajensu saboda yawan ruwan da aka samu sakamakon saukan Ruwan sama mai nauyi.

    Dubban mutane sun rasa gidajensu. Gwamnan jihar Eduardo Leite ya ce lamarin shi ne bala’I mafi muni da ya shafi yanayi a tarihin yankin.

    Gwamna Leite ya ce Daga abin da mu ke iya hangowa daga jirgin sama wannan lamarin baa bin da aka saba gani ba ne Ba al'ummomin gefen kogi ba ne kadai ne abin ya shafa ba.

  8. Mutum 16 sun mutu a wani hari da Rasha ta kai kasuwa a Ukraine

    H

    Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce wani hari da Rasha ta kai ya kashe mutane goma sha shida a garin Kostiantynivka da ke yankin Donetsk da ke gabashin kasar.

    Ya ce wasu da dama sun jikkata sakamakon harin, wanda aka yi a wata kasuwa, inda ya ce adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

    Mista Zelensky ya bayyana harin a matsayin "rashin Imani".

    A halin da ake ciki, shugaban yankin Zaporizhzhia ya ce wani harin roka da Rasha ta kai a yankin ya jikkata mutane biyu tare da lalata wani abu na more rayuwa mallakan fararen hula, ba tare da ya bayyana ko menene abin ba.

    A wani lamari na daban kuma, Majalisar dokokin Ukraine ta tabbatar da nadin Rustem Umerov a matsayin ministan tsaron kasar.

  9. Fitaccen Malamin addinin Musulunci Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu

    facebook

    Asalin hoton, Facebook

    Fitaccen malamin addinin nan Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu a yau Laraba.

    Malamin ya rasu ne sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita ta garen lokaci.

    Ya rasu a asibitin tarayya na Medical centre da ke birnin Kebbi a arewacin Najeriya.

    Ya rasu ya bar 'ya'ya 20 da mata hudu da jikoki da dama.

    Shafin Jibwis na Facebook ya ce za a yi jana'izar Malamin gobe a birnin Kebbi sai dai bai bayyana lokaci ba.

  10. An sauya ranar da Arsenal za ta fafata da Everton a Premier

  11. Yadda gwamnatin jihar Nasarawa ta raba tallafin kayan abinci kashi na biyu

    V

    A yau ne gwamnan jihar Nasarawa Eng. A A Sule ya je da kansa wajen rarraba kayan tallafi ga talakawan jihar bayan zarge-zargen cewa jami’an gwamnatin jihar na karkata da akalar kayyakin suna sai da wa.

    Hukumar ‘yan sandan cikin ta DSS ta sanar da cewa ta kama wasu jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar saboda zarginsu da irin wannan halayyar.

    Kan haka ne gwamnan ya halarci wurin da aka kaddamar da zagaye na biyu na rabon kayayyakin dazu a garin Karu.

    h
    n
    k
    B
    h
  12. An kama uwar gidan tsohon shugaban Zambiya kan zargin sata

    H

    'Yan sanda a Zambia sun kuma matar tsohon shuagaban ƙasar Edgar Lungu kan tuhume-tuhume uku, ciki har da zargin satar wata mota, zargin da ta musanta.

    Esther Lungu wanda a yanzu ake tsare da ita a Lusaka babban birnin ƙasar, an kamata ne tare da wasu mutum uku na daban.

    Kakakin 'yan sanda Danny Mwale ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa cewa an kama watar ana kuma tuhumarta da satar wasu takardun fili a Lusaka.

    Dukkansu ana zarginsu ne da mallakar kadarorin da ba bisa ka'ida ba.

    Da yawa daga cikin ministocin ƙasar da suka gabata da wasu manyan jami'ai na tsare ana bincikensu kamar yadda ake tsare da Mrs Lungu.

    Dukkansu sun musa musanta yin ba daidai ba.

  13. Majalisar Wakilan Najeriya za ta fara bincike kan ɓarayin ɗanyen mai a ƙasar

    k

    Asalin hoton, Others

    Wani kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya da ke bincike kan satar ɗanyen mai da ake yi da kuma asarar kuɗin shiga da ake samu na gas ya yi alƙawarin bayyana sunayen mutanen da ka da hannu cikin lamari.

    Ɗan Majalisa Kabiru Rurum wanda shi ne shugaban kwamitin ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nan gabanin fara sauraren binciken ranar 7 ga watan Satumba.

    Ya ce ɓangaren mai shi ne babbar hanyar da Najeriya ke samun kuɗin shiga, inda ya ƙara da alƙawarin cewa wannan binciken zai sha ban-ban da na baya da aka yi.

    A cewarsa, ɓanagern mai da gas sune manyan abubuwan da ƙasa ta dogara a kansu, amma matsalar satar mai na ci gaba da ƙazanta a Najeriya a kullum.

    "Dalilin wannan kwamitin shi ne ya bankaɗo sunan mutanen da ke da hannu cikin wannan satar da ake yi ta ɗanyen mai."

  14. Ten Hag na da muhimmaci a tarihin sana'ar ƙwallona - Amrabat

  15. An shiga yanke hukuncin ƙarar Atiku Abubakar na PDP

    Bayan dogayen bayanai da ka saurara daga Mai Shari'a Haruna tsammani wanda daga ƙarshe ya kori ƙarar jam'iyyar LP wadda Peter Obi ya yi mata takarar shugaban ƙasa.

    Yanzu kuma an shiga yanke hukunci kan ƙarar ɗan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.

    Gabanin nan, ɗaya daga cikin lauyoyin Peter Obi ya tashi ya ƙalubalanci alƙalan da suka yanke hukuncin, inda ya nemi su yi masa ƙarin bayani kan abin da suka yanke.

    Nan take alƙalen suka ce ba shi da wannanb hurumi, sai ya jira a fitar da bayanan bayan yanke hukunci ya gani.

  16. Luis Rubiales: Jenni Hermoso ta shigar da ƙorafi a kan sumbatar kofin duniya

    'Yar ƙwallon ƙasar Sifaniya, Jenni Hermoso ta shigar da ƙorafi a shari'ance game da sumbatar da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Luis Rubiales ya yi mata.

    Rubiales ya sumbaci Hermoso a leɓɓanta bayan nasarar wasan ƙarshe a Gasar cin Kofin Duniya ta Mata da Sifaniya ta yi, abin da 'yar ƙwallon ta ce ba da yardarta aka yi ba.

    Rubiales ya yi iƙirarin cewa ya sumbace ta ne "da yardarta kuma ita ma ta sumbace shi", amma dai hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta dakatar da jami'in a matakin wucin gadi.

    Ƙorafin na nufin Rubiales mai shekara 46 yana iya fuskantar tuhume-tuhumen aikata babban laifi.

    A ranar 29 ga watan Agusta ne, masu shigar da ƙara suna fara binciken farko a kan ko abin da Rubiales ya aikata daidai yake da laifin cin zarafin lalata.

  17. Shugabannin Afirka na so a ƙara haraji don magance sauyin yanayi

    d

    Asalin hoton, AFP

    Shugabannin ƙasashen Afirka sun ba da shawarar ɓullo da sabbin haraji a duk faɗin duniya domin ɗaukar nauyin matakan magance sauyin yanayi.

    Shawarar na kunshe a wata sanarwar da aka yi mata laƙabi da ‘Nairobi Delaration’ wadda aka fitar a ƙarshen taron sauyin yanayi na kwanaki uku da aka yi a babban birnin ƙasar Kenya.

    Da yake jawabi bayan kammala taron, shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya ce lokaci ya yi da ya kamata lamari ya sauya Mista ruto ya ce mun sami matsaya daya wadda muka gina kan tabbacin cewa nahiyar Afirka na da duk abin da take buƙata wurin taftace tattalin arzikin duniya ta kuma zama jagora a yunkurin inganta yanayin duniya baki daya.

    Shugabannin ƙasashen sun ce sanarwar za ta zama tushen tattaunawarsu a taron koli kan sauyin yanayi na duniya wato COP28 da za a yi a watan Nuwamba a Dubai.

  18. Man United ta bayyana 'yan wasan da za su buga Champions League

  19. Hukumomin Sudan sun buƙaci jiragen sama su koma zirga-zirga a ƙasar

    s

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Sudan ta yi kira ga kamfanonin jiragen sama da su koma zirga-zirga a ƙasar, bayan da kamfanin EgyptAir ya koma jigila a ƙasar karon farko tun bayan ɓarkewar rikici a ƙasar cikin watan Afrilu.

    A ranar Talata da safe ne jirgin saman EgyptAir ɗauke da fasinjoji 100 daga birnin Alƙahira ya sauka a birnin Port Sudan da ke gabashin Sudan, sannan ya koma Masar da rana.

    Gwamnan jihar Red Sea, Fathallah Haj Ahmed, ya shaida wa kafar yaɗa labarai cewa saukar jirgin EgyptAir a ƙasar alama ce da ke nuna cewa an samu kwanciyar hankali a ƙasar ta yadda jiragen ƙasashen duniya za su iya yin jigila a ƙasar.

    “Wannan saƙo ne ga duniya baki-ɗaya yanzu Sudan ta samu lafiya da kwanciyar hankali, don haka muke kira da kamfanonin jiragen sama na duniya da su ci koma zirag-zirgarsu a ƙasar, saboda a yanzu an samu zaman lafiya 100 bisa 100", in ji Ahmed.

    Cikin watan Afrilu ne Sudan ta rufe sararin samaniyarta bayan da aka samu ɓarkewar yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.

    A ranar 15 ga watan Agusta ne hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta ƙasar ta bayyana buɗe sararin samaniyar ƙasar a gabashin ƙasar.

  20. 'Mai ƙorafi bai iya kawo hujjar cewa an taɓa kama Tinubu da laifi ba'

    Game da ƙorafin cewa kotu Amurka ta taɓa ƙwace kuɗi har dala 46,000 daga hannun Bola Tinubu saboda zargin safarar ƙwaya, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a hukuncin da ta yanke, ta ce ana iya ƙwace abin mutum a ƙarar neman haƙƙi, ba tare da an tuhumi mutum da aikata wani babban laifi ba.

    Dangane da haka, a cewar kotun, mai ƙorafin ya gaza gabatar da hujjar cewa, wata kotu ta tuhumi Bola Tinubu, ko kuma ta same shi da laifi.

    Abin da ya sa, kotun ta yanke hukuncin yin watsi da buƙatar masu ƙorafin.

    Kotun ta kuma yanke hukuncin cewa jam'iyyar Labour Party da ɗan takararta, Peter Obi sun gaza gabatar da hujjar cewa kotu ta taɓa kama Bola Ahmed Tinubu na APC, da laifin halasta kuɗin haram a Amurka.