Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba
Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza
Mummunar guguwa ta afka wa Taiwan
Guguwar Haikui na ci gaba da kaɗawa a Taiwan, inda dubban gidaje suka kasance ba lantarki.
Guguwar ta haifar da iska da ruwan sama mai karfi, musamman a kudancin tsibirin.
Ana shirin aika sojoji yankin domin taimakawa wajen shawo kan ambaliyar.
Tuni aka bayar da umarnin rufe makarantu da wuraren kasuwanci a ranar Litinin
Guguwar Haikui ita ce guguwa mafi muni da ta afkawa tsibirin cikin shekaru hudu.
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga bayan yunƙurin ƙona Al Qur'ani a Sweden
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK
'Yan sanda a Sweden sun tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da ƙona al Qur'ani mai tsarki a birnin Malmo na ƙasar.
Ɗaruruwan mutane ne suka haɗa gangami a wani dandali inda wani ɗan iraqi ya fito ya ce zai kona Al Qur'ani mai tsarki.
Kafofin yada labaran ƙasar sun ce nan take aka far masa da jifa da duwatsu, yayin da kuma wasu masu kallo suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin 'yan sanda da ke ƙoƙarin kare shi, ya zuwa yanzu dai an kama mutum biyu.
An sha ƙone Al Qur'ani musamman a 'yan watannin nan a ƙasar Sweden, kuma gwamnatin ƙasar ta ce tana nazarin hanyoyin da za ta bi wajen ganin ta haramta hakan.
Najeriya na nazarin shiga ƙungiyar G-20
Asalin hoton, Twitter/Tinubu
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai halarci taron G-20 a birnin Delhi
Gwamnatin Najeriya ta ce tana nazarin aika buƙatarta ta shiga ƙungiyar ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin duniya, ake yi laƙabi da G-20.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale, ya ce gwamnati na auna alfanu ko kuma kasadar da ke tattare da zama mambar a ƙungiyar.
A ranar litinin ne shugaban ƙasar Bola Tinubu zai tafi birnin Delhi domin halartar taron ƙungiyar bisa gayyata ta musamman da firaministan Indiya Narendra Modi ya yi masa.
Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da matakai na farfado da tattalin arzikin ƙasar da ƙarfafa zuba jari amma kuma ƙasar na fama da hauhawar farashin kayayyaki da basussuka da rashin ingancin kayayyakin more rayuwa.
A halin yanzu Afirka ta Kudu ce kaɗai daga Afirka ta samu zama mamba ƙungiyar ta G20.
Gwamnatin Kaduna ta ɗauki 'yan sa kai 7,000 don magance matsalar tsaro
Asalin hoton, Nig.Army
Gamnatin jihar Kaduna ta ɗauki matasa 7,000 a matsayin 'yan sa kai, domin taimaka wa jami'an tsaro wajen magance matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.
Yayin da yake jawabi a wajen horas da matasan 'yan sa kan, a kwalejin horas da 'yan sanda ta Kaduna, gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata, wajen magance matsalar masu garkuwa da mutane da 'yan fashin daji da sauran laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
An ɗauki dubban matasan ne - waɗanda suka haɗar da maza da mata - daga ƙananan hukumomin jihar 23.
Gwamnan jihar ya ce za a tura masu aikin sa kan zuwa garuruwa da ƙauyukan jihar.
Uba Sani ya ce wannan yunƙuri zai samar da ayyukan yi dubban matasan jihar, baya ga kasancewarsa babban mataki na maido da zaman lafiya da ci gaban jihar.
Arsenal ta caskara Man United a mintunan ƙarshe a Premier
Tinubu zai tafi Indiya taron G-20
Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin masana'antu ta G-20.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Tinubu zai halarci taron ne bisa gayyata ta musamman da firaministan Indiya Narendra Modi ya aika masa.
Mista Ngelale ya ce Tinubu zai bar Najeriya ranar Litinin zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya inda za a gudanar da taron.
Duk da kasancewa Najeriya ba ta cikin ƙungiyar ta G-20, ana sa ran shugaba Tinubu zai yi jawabi a taron.
Sanarwar ta kuma ce a gefen taron shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a wata ganawa da zai yi firaminstan na Indiya, da kuma taron kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu da za a shirya.
Manyan 'yan ƙasuwa da jami'an gwamnatin Indiya da na Najeriya ne za su halarci taron tattaunawar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ngelale ya ce shugaban Najeriyar zai yi amfani da wannan taro wajen janyo hankalin masu zuba jari na ƙasashen wajen zuwa Najeriya don samar da ayyukan yi tare da sama wa ƙasar ƙarin kuɗin shiga don haɓaka tattalin arzikinta.
Daga cikin jami'an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya zuwa taron akwai ministan harkokin ƙasashen waje, da ministan kuɗi da na tattalin arziki, da ministar sadarwa, da ministar kasuwanci da masana'antu
Shugaba Tinubu zai koma Najeriya da zarar an kammala taron, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Barcelona za ta buga wasa biyar a watan Satumba
Gwamnati Najeriya ta gargaɗi masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba
Asalin hoton, Twitter/Dele Alake
Gwamnatin Najeriya ta bai wa masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba kwana 30, su dakatar da ayyukansu a faɗin ƙasar.
Ministan ma'adinan ƙasar Dele Alake ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar a Abuja.
Alake ya ce duk yunƙurin da gwamnati ke yi wajen mayar da masu haƙar ma'adinan da ba su da lasisi zuwa halastattu ya ci-tura.
Ya ƙara da cewa ma'aikatarsa za ta sake nazarin lasisin masu haƙar ma'adinai a ƙasar a wani ɓangare na sauye-sauyen da yake yunƙurin yi a ma'aikatar.
Ministan ya ce daga cikin sauye-sauyen da yake shirin yi wa ma'aikatar har da ɓullo da kamfanin ma'ainai na ƙasa, da zai haɗa hannu da kamfanonin ma'adinai na duniya, da kuma samar da 'yan sandan da za su riƙa lura da harkar ma'adinai, tare da samar da bayanan alƙaluman ma'adinai a ƙasar.
A makon da ya gabata ne Ministan ya alƙawarta tsabtace ɓangaren haƙar ma'adinai ta hanyar gabatar da wasu tsare-tsare da ya kira ''masu tsauri'' domin daidaita ɓangaren.
Liverpool ta hada maki uku a kan Aston Villa a Premier
Hatsarin mota ya kashe mutum shida a jihar Osun
Asalin hoton, FRSC
Hukumar kiyaye haɗurra a Najeriya ta ce aƙalla mutum shida ne suka rasu sakamakon hatsarin mota da ya afku a jihar Osun da ke kudancin ƙasar.
Kwamandan shiyya, Henry Benamesia, ya ce ababen hawa biyu ne suka yi karo da juna ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:44 na dare sakamakon shanyewar birki na ɗaya daga cikinsu, wanda hakan ya jawo mutuwar shida daga cikin fasinjojin.
"'Yan sanda sun kai gawar mutum biyar asibitin koyarwa na Osun kafin zuwan jami'an hukumar FRSC," kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ambato Mista Benamesia yana bayyanawa cikin wata sanarwa.
"Ɗaya gawar ta maƙale ne a jikin ɗaya daga cikin motocin, har sai da muka yi amfani da inji kafin mu iya ɓamɓare ta."
Benamesia ya ce gudun wuce kima da ɗaya daga cikin motocin ke yi ne ya haddasa hatsarin.
Yadda ake amfani da fitsari don gane mai ciki fiye da shekara 4,000
Iyalan jagoran Miyetti-Allah a Najeriya na neman taimakon hukuma bayan watanni da ɓatansa
Asalin hoton, Family
Iyalan mataimakin shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti-Allah a Najeriya, Muneer Atiku Lamido, na ci gaba da bayyana damuwa game da rashin jin duriyarsa.
Sama da wata biyu ke nan da ɓacewarsa, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Kaduna daga Katsina ranar 23 ga watan Yuni
Iyalansa sun ce har yanzu babu wani ƙarin bayani da suka samu game da shi walau daga hukumomi ko jami'an tsaro.
"Farko-farkon abin jami'an taro na DSS suna zuwa su tambaye mu mu bayar da abin da muka sani game da shi, amma daga lokacin ba su sake ce mana komai ba," in ji matarsa Asma'u.
Ta ƙara da cewa kwana huɗu da ɓatan nasa aka mayar musu da motarsa da kuma wayoyinsa "amma bayan goge dukkan bayanan da suke ciki".
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton A'isha Salisu Babangida:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton A'isha Salisu Babangida:
Tarihin taken Champions League da yadda ake hasashen ruwan sama
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Amsoshin Takardunku:
Filin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi biyu.
Ta farko ta nemi sanin tarihin taken gasar zakarun Turai ta Champions League, sai kuma yadda masana kimiyya ke yin hasashen samun ruwan sama ko akasin haka.
Muhammad Annunr Muhammad ne ya gabatar da shirin.
Najeriya za ta kafa cibiyoyin agaji a ƙananan hukumomi 774 don rage talauci
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A watan Oktoba na 2020 aka ɓalle gidajen ajiyar kayan abinci tare da yashe su a jihohin Najeriya da dama - ciki har da wannan da ke Abuja a ranar 26 ga wata
Ministar Harkokin Agaji da Rage Talauci a Najeriya, Betta Edu, ta ce ma'aikatarta za ta gina cibiyoyiin agaji a dukkan ƙananan hukumomin Najeriya 774.
A cewarta, cibiyoyin za su yi aiki ne a matsayin mataki na korar talauci a hankali, kuma za a ajiye kayan abinci ne da aka samar a cikin gida.
"A ƙarƙashin mulkina, ma'aikatar agaji za ta rage talauci ta hanyar ƙirƙirar ayyukan yi, da tura wa masu ƙaramin ƙarfi kuɗi," in ji ministar lokacin da take magana a gidan rediyon tarayya ranar Asabar.
A watan Agusta ne Bola Tinubu ya rantsar da Edu a matsayin minista bayan ta sauka daga muƙamin shugabar mata ta jam'iyyarsu mai mulki ta APC.
Ana ganin ma'aikatar tata za ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin na rage wa 'yan Najeriya raɗaɗin cire tallafin man fetur, wanda ya jawo ninninkawar farashi a faɗin ƙasar.
Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwannin shanu takwas kan sayar da dabbobin sata
Asalin hoton, Facebook/Dauda Lawal
Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta sanar da rufe kasuwannin shanu da aka fi sani da kara saboda zargin sayar da shanun sata da 'yan bindiga ke yi.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya fitar ta ce matakin ya shafi ƙananan hukumomi biyar na jihar, wanda Majalisar Tsaro ta Zamfara ta ɗauka a zamanta na ranar Alhamis da ta wuce.
Kasuwannin da lamarin ya shafa sun haɗa da Danjibga da Kunchin Kalgo, da ke ƙaramar hukumar Tsafe, Bagega da Wuya, a ƙaramar hukumar Anka, da Dangulbi da Dansadau, a Maru.
Sauran kasuwannin su ne Dauran da ke ƙaramar hukumar Zurmi da kuma Nasarawar Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyim.
"An ɗauki matakin ne sakamakon saye da sayar da shanu na sata da wasu 'yan bindiga ke yi," a cewar sanarwar da Kwamashina Mannir Muazu Haidara ya saka wa hannu.
Kwamishinan ya kuma nemi shugabannin ƙananan hukumomin da su tabbatar an bi umarnin.
Jagoran mulkin sojan Gabon ya gana da jam'iyyun siyasar ƙasar
Asalin hoton, Gabon 24
Jagoran mulkin soja a Gabon, Birgediya Janar Brice Oligui Nguema, ya gana da shugabannin jam'iyyun siyasar ƙasar a yunƙurin da yake yi na mayar da mulki ga farar hula.
Gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar ya nuna jagororin siyasar a ranar Asabar suna neman sojan da ya tabbatar sabuwar gwamnatin riƙon-ƙwaryar da za a kafa ta fitar da "tsarin shari'a" da zai ba da damar komawa kan turbar dimokuraɗiyya.
A gobe Litinin ake sa ran za a rantsar da shi a matsayin shugaban gwamnatin riƙon-ƙwaryar.
Janar Nguema ya nemi jam'iyyun su shiga a dama da su a shirin miƙa mulkin ta hanyar bayar da gudummawarsu a zaɓe da kuma tsara kundin mulki "da zai ƙunshi ra'ayin al'ummar Gabon".
"Daga yanzu ba za mu so mu dinga ganin 'yan siyasa uku ko huɗu sun taru ba kuma su sauya wani tsari da gwamnati za ta bi, sannan daga baya mu ji an ce an amince da sauya tsarin zaɓe a taron ƙasa baki ɗaya," in ji shi.
Gwamnatin Ali Bongo da aka hamɓarar ta aiwatar da sauye-sauye masu cike da cecekuce a tsarin zaɓen ƙasar wata ɗaya kafin babban zaɓen na ranar 26 ga watan Agusta, wanda aka ce wasu jam'iyyun adawa ne suka nemi a yi hakan.
An ɗage dokar hana fita bayan rikicin ƙabilanci ya kashe mutum uku a Iraƙi
Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum uku aka kashe wasu kuma da dama suka jikkata a arewacin birnin Kirkuk da ke Iraƙi sakamakon rikicin ƙabilanci.
Hukumomi sun ɗage dokar hana fita da suka sanya a birnin bayan ƙura ta lafa.
Dama an ɗauki kwanaki ana zaman doya da manja tsakanin Larabawa da Turkawa da ke zaune a yankin da suke ƙoƙarin hana jam'iyyar Kurdawa komawa tsohuwar hedikwatarta, wadda a baya-bayan nan sojojin Iraƙi suka mayar sansaninsu.
Firaministan Iraƙ Mohamed Shia al-Sudani ya bayar da umarnin bincike tare da kiran bangarorin biyu su kwantar da hankali.
Yankin Kirkuk na da tarin arzikin mai, kuma an jima ana takun-saƙa tsakanin gwamnatin Iraƙin da Kurdawan da suka zargi tsohon shugaban kasar, marigayi Saddam Hussein, da tsugunar da dubban Larabawan Iraƙi a yankin.
Yadda masu zanga-zanga suka yi wa sansanin sojan Faransa ƙawanya
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Kamar yadda ake iya gani a wannan bidioyon na sama da sojojin mulkin Nijar suka aika wa BBC Hausa, dubban masu zanga-zanga ne suka cika sansanin da sojojin Faransa suke a ranar Asabar.
Ana sa ran da yawansu za su sake fitowa a yau Lahadi don cika alƙawarin da suka ɗauka na ci gaba da yin zaman dirshan har sai sojojin sun fita daga Nijar.
Faransa na da dakaru aƙalla 1,500 a sansanoni biyu da ke Nijar ɗin, waɗanda ta jibge don yaƙar 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Akwai dakarun Jamus da na Nijar ɗin a cikin sansanin na Escadrille da ke birnin Yamai.
Masu zanga-zanga sun yanka akuya ɗauke da tutar Faransa
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Faransa - wadda ta yi wa Nijar mulkin mallaka - na faman neman yadda za ta kyautata alaƙa da Nijar yayin da 'yan ƙasar ke ƙumajin yanke alaƙar.
A ranar Asabar, dubun dubatar masu zanga-zanga ne suka kutsa kai cikin sansanin sojan sama na Escadrille da dakarun Faransa ke sansani ɗauke da kwalaye masu rubutu daban-daban.
Wasu sun yanka akuya mai ɗauke da tutar Faransa, sannan wasu suka dinga yawo da makara lulluɓe da tutar ta Faransa. Haka nan an ƙona tutocin Faransar a wurin.
Duk sun yi wannan ne bayan sun shallake shingen da dakarun sojan Nijar ɗin suka kakkafa a ƙofar shiga sansanin da zimmar hana su shiga.
Ita dai Faransa ta ƙi amincewa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum, inda Shugaba Macron ya nanata a ranar Alhamis cewa shugaban suke mara wa baya.
Kazalika, dakarunta na soji da kuma jakadanta a Nijar ba za su fice daga ƙasar ba kamar yadda sojojin mulkin suka ba su wa'adi "saboda su ba halastacciyar gwamnati ba ce" a wajenta.
Tuni sojojin suka cire wa jakadan na Faransa rigar kariya kuma suka umarci 'yan sandan ƙasar su fitar da shi da ƙarfi da yaji.
Zanga-zangar korar dakarun Faransa a Nijar ta shiga rana ta uku
Asalin hoton, Reuters
A jamhuriyar Nijar, ana sa ran ƙarin zanga-zanga a birnin Yamai game da neman dakarun Faransa su fice daga ƙasar ta yammacin Afirka.
A jiya Asabar dubban mutane suka yi gangami a wajen sansanin sojin Faransa da ke Yamai.
Akwai dakarun Faransa aƙalla 1,500 a Nijar waɗanda ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Dangantaka tsakanin Nijar da tsohuwar uwargijiyarta ta ƙara tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli da ya wuce.
A ranar Juma'a shugaban sojin Nijar ya soki matakin ƙin amincewa da gwamnatinsu da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, yana mai cewa kullum suna magana da Bazoum Bazoum ta wayar tarho.