Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Biden ya nemi ƙara wa Ukraine tallafin dala biliyan 20

    Biden

    Asalin hoton, EVELYN HOCKSTEIN

    Gwamnatin Biden ta buƙaci ƴan majalisar dokokin Amurka su bayar da damar ƙara taimakawa Ukraine da dala biliyan 20.

    Za a yi amfani da mafi yawancin kuɗin ne a kan ayyukan taimakon soji.

    Tun bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraine, Amurka ta bai wa ƙasar fiye da dala biliyan 100 a matsayin tallafi.

    Wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce za a ci gaba da bayar da irin wannan tallafi idan har buƙatar hakan ta taso.

    Ko da yake wasu ƴan majalisar daga jam'iyyar Republican sun ce za a soki matakin ci gaba da bayar da irin wannan taimako.

  2. Ivory Coast za ta tura sojoji Nijar

    Ivory Coast

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ivory Coast ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.

    Alassane Ouattara na jawabi ne bayan kammala taron gaggawa na ECOWAS a Abuja, inda ƙungiyar ta ba da umarnin tanadar dakarun ko-ta-kwana don tura su Nijar a ƙoƙarin dawo da aiki da tsarin mulki.

    Ya ce ƙungiyar na son a dawo da shugaban ƙasar da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa, Mohammed Bazoum a kan mulki.

    Mr Outtara, ya ce sojoji daga Najeriya da Benin da sauran ƙasashe za su haɗu da na Ivory Coast don zama cikin wannan shiri.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa a wannan shafi barkan mu da safiyar Juma'a.

    Badamasi Abdulkadir Mukhtar ke fatan mun wayi gari lafiya.

    Ku ci gaba da bibiyar mu don samun rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.