Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu - za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu - za mu dawo da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo a jihar Kaduna ya kai mutum 17.
An kuma gano mutane 68 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗn jihar zuwa ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin jihar ta Kaduna ta tabbatar.
Daga cikin adadin, an samu rahoton mutuwar mutane 14 a Kafanchan da karamar hukumar Jema’a, yayin da uku kuma suka mutu a karamar hukumar Makarfi.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito babban jami’in kula da cututtuka na ma’aikatar lafiya ta jihar, Dokta Jeremiah Daikwo, na cewa ana dakon sakamakon samfuri guda 20 da ma’aikatar ta tattara kuma ta aika domin a yi gwaji.
Mutane 48 da aka kwantar da su kuma na samu kulawar da ta dace.
Daikwo ya bayyana cewa majinyata 12 suna kwance a babban asibitin Makarfi, 35 kuma a babban asibitin Kafanchan, sai kuma majiyyaci ɗaya a cibiyar lafiya a matakin farko ta Kubau.
Dangane da matakin da ma’aikatar ta ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar, babban jami’in kula da cututtukan ya ce ma’aikatar ta kara kaimi wajen neman waɗanda suka kamu da cutar da kuma kai su zuwa cibiyar kiwon lafiya domin ba su kulawa.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta kara zage damtse wajen sa ido a kananan hukumomin jihar 23, ta hanyar aiki tare da magidanta da kuma shugabannin al’umma.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga birnin Mogadishu na cewa an kashe tsohon ministan noma na jihar Hirshabeelle a yau Lahadi.
Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai ne sun far wa ministan Hassan Ahmed Mudey a gundumar Yaqshid da yake zaune, bayan sallar isha’i, kamar yadda wani ɗan majalisar gudanarwa ta Hirshabeelle ya bayyana.
Minista Mudey na ɗaya daga cikin majalisar ministoci a zamanin Shugaba Mohamed Abdi Waare.
Kungiyar Al-Shabaab ta ɗauki alhakin kashe tsohon ministan.
Kawo yanzu dai hukumomin tsaro na gwamnatin ƙasar ba su ce uffan ba game da kisan da aka yi wa ministan ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan kwallon tawagar Brazil, mai tsaron baya, Alex Telles ya koma taka leda a Al-Nassr daga Manchester United.
Telles, mai shekara 30, zai taka leda tare da tsohon ɗan wasan United, Cristiano Ronaldo, wanda ya koma buga babbar gasar Saudi Pro League a watan Janairu.
Kungiyoyin biyu ba su fayyace kuɗin cinikin ɗan kwallon Brazil ɗin ba.
Telles ya yi wasa 50 a United tun bayan da ta ɗauko shi daga Porto kan fam miliyan 13.6 a 2020, wanda ya yi wasannin aro a Sevilla a kakar da ta wuce.
A kakar bana, babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia ta ɗauki fitattun 'yan kwallo, ciki har da Karim Benzema, wanda kwantiraginsa ya kare a Real Madrid.
Telles shi ne na baya-bayan nan daga Premier League da ya koma zai buga Saudi Pro League da ya haɗa da N'Golo Kante daga Chelsea da ɗan wasan Liverpool Roberto Firmino.
Telles, wanda ya yi wa Brazil wasa 12 da guda biyu a kofin duniya a Qatar a 2022, ya yi takarar buga gurbin lamba uku tare da Luke Shaw a Old Trafford.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan tsaron ƙasar Jamus Boris Pistorius ya soke ziyarar da ya shirya kai wa ƙasashen Iraqi da Jordan.
Jami'ai a ma'aikatar sun ce an soke ziyarar ne saboda dalilai na tsaro.
An yi imanin cewa wani yanayi na damuwa ya mamaye jami'an tsaron Jamus bayan da jama'a a Bagadaza suka ƙona ofishin jakadancin Sweden da ke babban birnin Iraqi bayan kona kur'ani a Stockholm.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi da ma’aikatan kashe gobara a Kamaru, sun ce akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da 21 suka jikkata a ranar Lahadi, bayan da wani gini ya rufta a Douala cibiyar kasuwancin ƙasar.
Ginin mai hawa huɗu ya rufta kan wani ginin da misalin karfe 1:00 na safe agogon GMT a arewacin birnin, kamar yadda wani babban jami'in hukumar kashe gobara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Ɗan majalisar karamar hukumar Douala,Charles Elie Zang Zang, ya ce jami'an ceto na neman waɗanda suka tsira daga ɓaraguzan ginin.
Asibitin Laquintinie da ke Douala ya ce an kai masa waɗanda suka jikkata su 13 kuma ya ce biyu daga cikinsu - da suka haɗa da yarinya 'yar shekara uku da budurwa 'yar shekara 19 - sun mutu.
Ya kara da cewa wasu yara uku na karɓar kulawar gaggawa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan bindiga sun kai hari karamar hukumar Kankia na jihar Katsina tare da kashe mutum ɗaya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ƴan bindigar sun harbi mutumin ne lokacin da suka kai hari wani rukunin gidaje da ke unguwar low-cost kusa da babban asibitin karamar hukumar a daren Asabar.
Wani ganau ya bayyana cewa ƴan bindigar sun zo ne a kan babura, inda suka yi wa rukunin gidajen dirar miƙiya tare da harbi kan mai uwa da wabi, abin da kuma ya janyo mutuwar mutumin mai suna Alhaji Ibrahim Baraya Solo.
Bayan kashe mutumin ne, sai maharan suka tsere tare da barinsa cikin jini.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni ƴan sanda suka fara bincike kan lamarin domin kamo waɗanda ke da hannu a kai harin.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin mulkin sojin Mali ta addamar da sabon kundin tsarin mulki wanda ya bai wa shugaban da rundunonin sojin ƙasar ƙarfin iko mai yawa.
haka kuma sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar samar da majalisar magabata, sannan ya cire Farananci a matsayin harshe gudanar da mulki.
Majalisar koli ta sojoji ce ke jagorantar kasar tun shekarar 2020.
Kungiyoyin adawa sun yi Allah wadai da sauye-sauyen, duk da cewa hukumar zaɓen kasar ta ce kashi 97 ne na 'yan kasar suka amince da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da aka gudanar cikin watan da ya gabata.
Masu sukar sauyen-sayen sun ce sabon kundin tsarin mulkin zai bai wa manyan hafsashin sojin kasar damar fasa alkwarin da suka yi na miƙa mulki hannun farar hula, bayan zaben da ake sa ran gudanarwa cikin watan Fabrairun 2024.
Sabon kundin tsarin mulkin ya bai wa shugaban mulkin sojin ƙasar kanal Assimi Goïta damar gudanar da tsare-tsaren gwamnati ta hanyar rusa majalisar dokoki.
Majalisar koli ta sojojin kasar ta samu gagarumin goyon baya a lokacin da ta ƙace mulkin ƙasar, bayan ɓarkewar zanga-zangar adawa da tsohon hamɓararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta shekaru uku da suka gabata.

Asalin hoton, others
Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya karɓi takardar ajiye aikin ministar tsaftar muhalli da albarkatun ruwa ta ƙasar, bayan da aka zargeta da ɓoye dala miliyan ɗaya a gidanta da ke Accra.
Cecilia Abena Dapaah, ta sauka daga muƙaminta sakamakon ce-ce-ku-cen da ya ɓarke a kasar kan gano maƙudan kuɗaɗen a gidanta, da aka yi zargin na sata ne.
'Yan ƙasar da dama da masu rajin yaƙi da rashawa sun yi ta aza ayar tambaya kan hanyoyin samun kuɗin ministar da kuma dalilin da ya sa ta ajiye maƙudan kuɗaɗen a gidanta, duk kuwa da halin matsin tattalin arziki da ƙarancin kuɗin ƙasar waje da ake fama da shi a ƙasar.
A ranar Juma'a ne kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito cewa an gurfanar 'yan aikin gidan ministan biyu da wasu mutum uku a gaban kotu bisa zarginsu da sace dala miliyan ɗaya da Euro 300,000 da kuma miliyoyin sidi na kuɗin ƙasar da wasu abubuwa a gidanta a watan oktoban 2022.
Cikin takardar barin aikinta Cecilia Abena Dapaah, ta ce kuɗin da kafafen yaɗa labaran suka ambata, ba shi ne adadin kudin da ita da mijinta suka gaya wa 'yan sanda ba, a lokacin da suka kai rahoton yi musu satar.
Ta kuma ƙara da cewa a shirye take ta bai wa jami'ai haɗin kai wajen gudanar da bincike domin gano hakiƙanin gaskiyar lamarin.
An zargi masu aikin gidan da kashe kuɗin da suka sata a gidan ministar, ta hanyar sayen kadarori.
Babban ɗan takarar jam'iyyar adawa, kuma tsohon shugaban ƙasa John Mahama ya bayyana matakin da ''badaƙala'.
Cikin wani sakon Tuwita da ya wallafa ya ce ''Ko da ta hanyar halal ta same su, me yasa za ta ajiye miliyoyin kudi a gidanta?''
'Yan majalisar dokokin ƙasar na kira a gudanar da bincike kan hanyar da ministar ta samu kuɗin.
Haruna Shehu Tangaza tare da Umayma Sani Abdulmumin ne suka gabatar da shirin na wannan makon
Goba bishiya ce da ta samo asali daga yankin kudancin da tsakiyar nahiyar Amurka.
‘Yayanta da ganyenta na da amfani da dama ga lafiyar dan’adam.
Mun tattauna da likita, Usman Bashir a kan alfanunta.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Daƙile Cutuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax - da wasu dabbobin ƙasar ke fama da ita - ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba.
gidan Talbijin na ƙasar NTA ya ambato shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed na cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla a ƙasar.
Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma'aikatar lafiyar ƙasar na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.
Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.
Tuni dai gwamnatin ƙasar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ɓulla.
Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.
Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.
Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.
A baya-bayan nan dai hukumomin Najeriya sun bayyana ɓuallar cutar a jihar ta Naija, lamarin da ya sa hukumomin lafiyar ƙasar yin gargaɗi game da cin naman dabbobin da ba su da lafiya.
Shin me ke sa manyan hafsoshin soja a Najeriya ke yin murabus na dole da zarar na ƙasa da su ya zama babban hafsan sojin ƙasar?
Wannan na daga cikin tambayoyin da muka nemo muku amsarsu, cikin shirin namu na wannan makon, wanda Badamasi Abdulkaɗir Muktar ya gabatar.

Asalin hoton, Getty Images
Mamallakin kamfanin Twitter Elon Musk ya ce yana duba yiwuwar sauya wa shafin sabon tambari.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Elon Musk ya ce ''Nan ba da jimawa ba za mu sauya wa twitter tambari, ta hanyar musanya hoton tsuntsun da a yanzu ke mazaunin alamar shafin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Ya ƙara da cewa za a sauya hoton tsuntun da alamar harafin 'X'
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Hamshaƙin ɗan kasuwar ya ce ya zaɓi sauya wa shafin tambarin ne domin tabbatar da shafin ya bambanta da kowanne.
Elon Musk ya kuma bayar da samfurin misalin yadda sabon tambarin shafin zai kasance, ta hanyar wallafa bidiyon sabon tambarin a shafinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
A baya-bayan nan dai mai kamfanin Meta da ya mallakin shafin Facebook da Instagram da Whatsapp ya kaddamar da sabon shafin 'Thread' da ake kallo a matsayin kishiya ga shafi Twitter.
Shafin da ya samu miliyoyin mabiya a faɗin duniya.

Asalin hoton, Twitter/Nig.Army
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya ƙaddamar da sabuwar rundunar soji mai suna 'Haƙorin Damisa' da za ta yi yaƙi da rikicin ƙabilanci da na tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Plateau.
Cikin wani sakon Twitter da rundunar sojin ƙasan Najeriya ta wallafa, ta ce an ƙaddamar da rundunar ne domin magance tashe-tashen hankulan da ake yawan samu, a ƙaramar hukumar, lamarin da ke ƙara haifar da taɓarɓarewar tsaro a yankin.
Yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar, a lokacin ƙaddamarwar, babban hafsan soji ƙasa na Najeriyar ya yi kira a gare su da sun kawar da duka wani nau'in barazanar tsaro da yankin ke fuskanta da ma jihar Plateau baki-ɗaya.
Manjo Janar Lagbaja ya ce dakarun su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron lafiyar mazauna yankin, ta hanyar gaggauta kai ɗauki a duk inda aka buƙace su.
Ya kuma sake nanata wa sojojin irin ƙwarin gwiwar da al'umma gari ke da shi a kansu.

Asalin hoton, Twitter/Nig.Army
Haka kuma babban hafsan sojin ƙasar ya gana da masu ruwa-da-tsaki na ƙaramar hukumar, inda ya yi kira a gare su, da su nuna kishi wajen maido da zaman lafiya a ƙaramar hukumar, wani abu da ya kira ''Babban aikin maido da zaman lafiya a Mangu''.
Yana mai cewa babu wanda zai kai al'ummar garin tare da iyalansu jin daɗi, idan aka samu samu zaman lafiya a yankin.
A baya-bayan nan dai an samu rahotonnin tashe-tashen hankula a garin na Mangu.
Jihar Plateau na daga cikin jihohin Najeriya da ke yawan fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci da na manoma da makiyaya.

Asalin hoton, EPA
'Yan sanda a Mexico sun kama wani mutum da ake zargi da kai hari wata mashaya a jihar Sognare da ke arewacin kasar, lamarain da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da jikkata wasu da dama.
Hukumomi a jihar a birnin San Luis Rio Colorado da ke kan iyakar ƙasar da Amurka, sun ce matashin ya jefar da ragowar sigarin da yake sha ne cikin fushi gabanin kaddamar da harin, bayan da aka hana shi shiga saboda cin zarafin wasu mata.
An garzaya da wasu da dama da suka jikkata zuwa asibitoci a Amurka domin yi musu magani.

Asalin hoton, TOM BURRIDGE, BBC
Gwamnan yankin Odesa na Ukraine Oleh Kiper ya ce mutum guda ya mutu, sannan akallan 15 sun jikkata, sakamakon harin da jiragen saman Rasha suka kai a tashar jirgin ruwa da ke yankin.
Ya ƙara da cewa harin ya kuma haifar da lalacewar ababen more rayuwa na fararen hula, da gine-ginen jama'a da kuma wata coci.
Birnin Odesa na fuskantar hare-hare a baya-bayan nan daga dakarun Rasha, tun bayan sanarwar da Moscow ta bayar a makon da ya gabata cewa ba za ta sabunta yarjejeniyar fitar da hatsi ba.
Tashar ruwa ta Odesa, ita ce tasha ra jiragen ruwa mafi girma a Ukraien, kuma an yi jigilar miliyoyin tan na hatsi daga tashar a ƙarƙashin yarjejeniyar da Turkiyya ta jagoranci ƙullawa.
Masu bin mu a wannan shafi, barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasance da ku a wannan yini domin kawo muku irin labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.
Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.
Ku biyo mu....