Rufewa
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu - za mu dawo muku da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu - za mu dawo muku da sabbin labarai.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan tawagar Faransa, Samuel Umtiti ya koma taka-leda a Lille daga Barcelona.
Mai shekara 29, wanda ya buga wa Lyon tamaula kafin ya koma Barcelona, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu da kungiyar da ke buga Ligue 1.
Umtiti - wanda ya taɓa lashe Kofin Duniya - ya sha fama da jinya kusan shekara hudu, hakan ya sa aka bayar da aronsa da Lecce a kakar da ta wuce.
''Tun farko na so komawa Lyon, daga baya na amince na taka-leda a Lille, wadda ita ce ke bukatar na buga mata tamaula,'' in ji dan wasan.
Mai tsaron bayan ya fara taka leda a Lyon tun daga matasan kungiyar, wanda ya lashe babban kofin gasar kwallon kafar Faransa a 2012.
Umtiti shi ne ya ci wa Faransa kwallo a karawa da Belgium a daf da karshe a 2018, sai dai rabon da ya yi wa tawagar wasa tun 2019.

Asalin hoton, Getty Images
Yara biyu sun rasa rayukansu a wani gini da ya rufta a titin Ajao da ke unguwar Ikorodu a jihar Legas.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar.
“Yaran ‘yan shekara tara da kuma bakwai sun maƙale ne a lokacin da katangar gidan da ke makwaɓtaka da su ya faɗa kan gininsu a lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya,” in ji Kodinetan Hukumar NEMA a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, a cikin wata sanarwa.
Hukumar ta ce ba a samu kai agajin gaggawa ba a kan lokaci don ceto rayukan yaran.
Gidan talabijin nan Channels ya ruwaito cewa NEMA ta jajanta wa iyayen yaran da lamarin ya rutsa da su tare da addu'ar Allah ya basu ikon jure rashin.
Hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) ta je wurin da lamarin ya faru domin tantance lamarin.

Asalin hoton, Nigerian Army
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadarin Daji sun samu nasarar kashe wasu ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojin Najeriyar sun ce sun samu nasarar ce a ranar 20 ga watan Yuli bayan kai samame maɓoyar ƴan bindigar wanda hakan na cikin zimmar sabon hafsan sojin ƙasa Manjo Janar T. A Lagbaja na ganin an dawo da zaman lafiya a jihar da kuma yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Sojojin sun kuma samu nasarar tarwatsa sansanonin ƴan bindigar da dama a ƙauyukan Mutuwa da Guda tudu da Kawar da Dantayawa da Gidan Kare da Mahuta da kuma Gyado da ke jihohin Zamfara da Skoto.

Asalin hoton, Nigerian Army
Sai dai an yi ta artabu tsakanin sojojin da kuma ƴan bindigar, inda daga bisani sojojin suka fi karfin ƴan bindigar da kuma samun nasara a kansu.
Sun kuma samu nasarar ƙwato bindiga da harsasai da kuma babura huɗu daga hannun ƴan bindigar.
Haka ma, a irin wannan samame da sojojin suka kai karamar hukumar Maradun, sun samu nasarar kashe ƴan bindiga huɗu da hana su shiga ƙauyen yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga.

Asalin hoton, Getty Images
Aljeriya ta miƙa buƙatar son zama mamba a kungiyar ƙasashen BRICS da kuma ƙasancewa mai hannun jari a bankin na BRICS tare da zuba kuɗi da ya kai dala biliyan 1.5, kamar yadda gidan talabijin na Ennahar ya ruwaito shugaban ƙasar Abdelmajid Tebboune na cewa.
Gidan talabijin ɗin ya kara da cewa shugaba Tebboune ya ce Aljeriya na son zama mamba a kungiyar ne domin ɓuɗe sabbin hanyoyin karfafa tattalin arzikinta.
Ƙasar da ke yankin arewacin Afrika na da albarkatun man fetur da kuma iskar gas na son karfafa tattalin arzikinta da kuma kulla dangantaka da ƙasashe irin China.
Wasu ƙasashen da suka nuna sha'awarsu ta shiga kungiyar BRICS sun haɗa da Argentina da Iran da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Cuba da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Comoro da Gabon da kuma Kazakhstan.
China za ta zuba jarin dala biliyan 36 a Aljeriya a fanonni daban-daban da suka haɗa da masana'antu da fasaha da tattalin arziki da sufuri da kuma aikin gona.

Asalin hoton, Gwamnatin Borno
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya halarci ɗaurin auren ɗa ga gwamnan jihar Borno Mohammed Babagana Zulum.
Ɗaurin auren wanda aka gudanar yau Asabar a Babban Masallacin jihar da ke Maiduguri kusa da fadar Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya samu halartar manyan baki a faɗin ƙasar.
Tsohon shugaban Najeriyar shi ya yi wa ɓangaren ango waliyyi, inda ya karɓa wa ɗan gwamnan na Borno amaryarsa mai suna Ummi Kaltum.
Cikin mutanen da suka halarci ɗaurin auren akwai mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima da gwamnoni masu ci da kuma tsofaffi da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu da ƴan majalisar tarayya da sarakunan gargajiya da ƴan kasuwa a ciki da kuma wajen jihar ta Borno.

Asalin hoton, Gwamnatin Borno

Asalin hoton, Gwamnatin Borno

Asalin hoton, Gwamnatin Borno

Hukumomin Rasha sun sanar da rufe gadar Crimea bayan wani hari da aka kai matatar man fetur da ke kusa da gadar.
Harin ya janyo kwashe fararen hula daga yankin da kuma kawo tsaiko a zirga-zirgar ababen hawa.
Gwamnan yankin Crimea da Rasha ta naɗa, Sergei Aksyonov, ya zargi Ukraine da kai harin, sai dai bai bayar da gamsassun hujjoji kan iƙirarin nasa ba.
Mista Aksyonov ya ce an kwashe mazauna yankin da ba su fi nisan kilomita biyar ba da inda aka kai harin.
An dakatar da zirga-zirgar sufurin jiragen ƙasa a faɗin gadar Kerch.
Tun da safiyar ranar Asabar, hukumomin Rasha suka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a kan gadar, amma daga bisani suka buɗe ta.
Sai daga baya kuma hukumomin yankin da Rasha ta naɗa ta ce an sake dakatar da ababen hawa daga wucewa har sai abin da hali ya yi.

Asalin hoton, Getty Images
Japan da ke rukuni na uku a gasar kofin duniya ta mata ta caskara Zambia 5-0, yayin da Amurka mai rike da kofin ta doke Vietnam 3-0, ita kuwa Ingila ta yi nasara a kan Haiti da ci 1-0.
A gasar cin kofin duniya ta mata da ake yi a Australia da New Zealand, rukuni na huɗu Denmark ta ci China 1-0.
Karon farko da Denmark ta koma buga gasar cin kofin duniya tun bayan shekara 16.

Asalin hoton, Reuters
Jagoran addini na ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya bayyana a yau Asabar cewa ya zama wajibi mutanen da suka wulakanta Al-Kur'ani mai tsarki su fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kuma buƙaci ƙasar Sweden da ta miƙa waɗannan mutanen domin yi musu shari'a a ƙasashen musulmi, kamar yadda kafar yaɗa labaran Iran ta ruwaito.
"Dukkan malaman Musulunci sun yi ittifaqi kan cewa waɗanda suka wulakanta Al-Kur'ani sun cancanci hukunci mafi tsauri...Hakkin da ke kan wannan gwamnati Sweden shi ne miƙa masu laifi zuwa ga ƙasashen musulmi," in ji Khamenei.
Malamai sun bukaci a kashe wata yarinya da ake kyautata zaton ta zagi Annabi Muhammad SAW.

Asalin hoton, Twitter/Nig. Army
Rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar jami'an tsaron farin kaya sun lalata sansanin 'yan ungiyar awaren IPOB da takararta ta ESN a Asaba da ke jihar Delta.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce jami'anta sun kaddamar da samame kan sansanin 'yan awaren da ke takiyar babban dajin Asaba da safiyar ranar Asabar, inda suka samu nasarar kwato makamai.
Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigar a lokacin samamen, inda daga bi-sani 'yan bindigar suna gudu daga maɓoyar tasu.

Asalin hoton, Twitter/Nig.Army
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanarwar ta ce sojojin sun kama daya daga cikin mayaƙan 'yan awaren, tare da ƙwato bindigogi biyar kirar AK-47, da manyan bindigogi masu sarrafa kansu uku. da wata ƙirar G3 da ƙamar bindiga guda.
Sauran abubuwan da dakarun sojin suka ƙwato, sun hadar da kwanson saka alburushi biyar, da gatari da kuma tutar kungiyar IPOB.
Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya yaba da namijin ƙoƙarin da sojojin suka yi tare da sauran jami'an tsaro, a yunƙurinsu na kawar da ayyukan 'yan bindigar da ke addabar yankin, tare da maido da zaman lafiya.

Asalin hoton, WHO
Gwamnatin Gambiya ta kori shugaba da mataimakiyar shugabar hukumar kula da ingancin magunguna na kasar, bayan da kwamitin da gwamnati ta kafa ya gano cewa hukumar ba ta yi wa maganin tarin Indiya da ake alakantawa da kisan akalla yara 70 a kasar rajista ba, kamar yadda doka ta tanada.
Markieu Janneh Kaira tare da Foumata Jah Sowe su ke jagaorantar hukumar kula da ingancin magunguna da sarrafawa da kuma amfani da su ta kasar .
Ana zargin su da yin sakaci a aikinsu, tuni dai aka damƙa su a hannun 'yan sanda domin ci gaba da bincike.
Kwamitin ya kuma alakanta mutuwar yaran da shan magungunan tarin huɗu, da aka yi a Indiya, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna.
Haka kuma gwamnatin ƙasar ta kwace lasisin kamfanin 'Atlantic Pharmacy Company Limited' wanda ya shigar da maganin cikin ƙasar.
To sai dai kamfanin 'Maiden Pharmaceuticals' wanda ke sarrafa maganin a Indiya ya musanta zargin cewa maganin a gurɓatacce ne, a yayin da gwajin da hukumomin Indiya suka yi, ya nuna cewa maganin bai gurɓace ba.
Kawo yanzu ba a san wane tasiri wannan matakin zai yi ba kan rikicin da ke tsakanin gwamnatin ƙasar da kuma kamfanin Atlantic Pharmaceuticals da ya shigar da maganin da kuma kamfanin Maiden Pharmaceuticals mai sarrafa maganin.
Wata ƙungiyar iyayen yaran da suka mutun ne suka shigar da ƙara suna bukatar diyyar dala miliyan 4.7, tare da bukatar ma'aikatar lafiyar Gambiya da hukumar kula da magunguna ta kasar da su yadda sun kasa tantace magungunan da ake shiga kasar da su.
Adadin mutanen da aka sani sun mutu a sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a Koriya ta Kudu ya kai 47.
Bayan da masu aikin ceto suka gano gawar wani dattijo da ruwan ya yi gaba da shi a birnin Yochoon.
Jami'ai sun ce a ranar Asabar din da ta gabata mutane uku ne suka ɓace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yawancin kasar a 'yan kwanakin nan.
Lamarin da ya janyo zabtarewar kasa da ambaliya a yankuna da dama a ƙasar.
A halin da ake ciki hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa ana sa ran za a sake samun ruwan sama mai dimbin yawa a ƙasar cikin ƙarshen wannan mako
Hukumar Lafiya da Duniya WHO ta ce mutane na ɗaukar cututtuka fiye da 200 ta hanyar cin abincin da ya gurɓata da wasu ƙwayoyin cuta.
A sakamakon hakan mutum ɗaya cikin kowanne 10 na kamuwa da rashin lafiya a duk shekara sakamakon cin abincin da ya gurɓace.
WHO ta ce abinci kan gurɓata ne a lokacin da ake sarrafa shi ko ake jigilarsa daga wani wuri zuwa wuri, ko ma a yayin da ake cinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Cutar Mashaƙo ta halaka ƙananan yara uku tare da kwantar da bakwai a asibiti, bayan ɓarkewarta a ƙaramar hukumar Maƙarfi da ke jihar Kaduna.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ambato sakataren lafiya na ƙaramar hukumar Makarfi Malam Aliyu Alassan na tabbatar da haka a lokacin zantawa da shi.
Ya ce an samu ɓullar cutar a garin Tashar Na Kawu da ke mazaɓar Gubuchi a ƙaramar hukumar.
Alassan ya ce mafiya yawan waɗanda cutar ta kama ƙananan yara ne, ya ci gaba da cewa tuni aka ɗauki samfurin jininsu tare da aika shi Abuja babban birnin ƙasar domin yin gwaji don tantance cutar .
“An kai waɗanda ake zargi sun kamu da cutar zuwa asibiti, tare da killace su domin ba su kulawar da ta dace'', in ji shi.
Ma'aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da ɓullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema'a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan
Cikin wata sanarwa da ya fitar gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya umarci ma'aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci zuwa garin na Kafancan domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace kan ɓullar cutar.
A baya-bayan nan cutar mashaƙo na ci gaba da ɓulla a wasu jihohin ƙasar, tare da rahotonnin rasa rayuka masu yawa a wasu jihohin.
Alamomin cutar sun haɗar da wahalar numfashi, da zazzaɓi mai zafi, da tari, da kasala, da zafin maƙogoro da kuma kumburin wuya.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Tarayyar Najeriya FEMA ta yi gargaɗin samun ruwan sama mai karfi gaske da zai iya haifar da ambaliya a babbar birnin ƙasar Abuja da wasu jihohin ƙasar a ranakun Asabar da Lahadi.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma'a mai ɗauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar Nkechi Isa, ya ce hukumar na gargaɗin ne bayan da hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun ruwan sama mai ƙarfin gaske haɗe da iska da ambaliya da zaizayewar ƙasa a wasu sassan jihohin Katsina da Kano da Bauci da Plateau da Taraba da kuma Abujan
Hukumar kula da yanayi ta kasar NiMET ta yi hasashen cewa za a samu ambaliya ruwa tare da batsewar koguna da iska mai ƙarfi, da zaizaiyewar ƙasa da walkiya da kuma tsawa.
Hukumar ta NiMET ta yi kira a sauya matsugunai ga al'umomin da suke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar, wadda za ta iya lalata dukiyoyi tare da haifar da cutattuka.
Babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Abuja Dakta Abbas Idriss ya ce hukumar ta sanya jami'anta cikin shirin ko-ta-kwana don fuskantar matsalar.
Haka kuma ya yi kira ga mazauna birnin da su riƙa la'akari da gargadin da hukumar ta fitar, tare da kaucewa yin tuƙi ko tafiya a ƙafa a lokacin da ake tsaka da ruwan sama, tare da kauce wa titunan da ruwan zai iya mamayewa.
Ya kuma nemi jama'a da su yi gaggawar tuntuɓar hukumar idan suna buƙatar taimakon gaggawa daga gareta.