Tinubu ya ba da umarni a sake nazari kan shirin tallafin N8,000

Wannan shafi ne da yake kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and Rabiatu Kabir Runka

  1. Sai da safe

    To, masu bibiyar BBC Hausa, a nan za mu dasa aya cikin wannan shafi na kai tsaye da ke kawo muku rahotanni da labaran abubuwan da suka faru a faɗin duniya.

    Muna sa ran sake ganin ku a gobe Laraba, don ci gaba da tattaro muku muhimman labaran da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Amma yanzu kuna iya gangarawa ƙasa don karanta rahotanni da labaran da muka kawo muku.

    Aisha Babangida da Mukhtari Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya!

  2. Asibitoci na amfani da gungumen ƙanƙara ga masu fama da tsananin zafi a Amurka

    Zafi babu ƙaƙƙautawa na ci gaba da sauka a mafi yawan kudancin Amurka, abin da ya sanya Amurkawa fiye da miliyan 90 cikin gargaɗin fuskantar matsala sanadin zafin.

    A Phoenix, yanayin zafi ya kai mizanin salsiyas 43 karo na 19 a jere, abin da ya rusa tarihin zafi da birnin ya taɓa gani a baya.

    Jami'ai sun ce asibitoci na amfani da gungume-gungume na jakunkunan ƙanƙara don samar da sauƙin zafi ga wasu marasa lafiya da jikinsu ya yi zafi.

    Ana jin cewa yanayin zafi zai kai wani mizani mai hatsari a faɗin Amurka tsawon wannan mako.

    Tsananin zafin da ya sauka a mafi yawan yankunan Kudancin Amurka, ya sanya yanayin zafi ya yi matuƙar tashi kama daga jihar Florida har zuwa California.

    Fiye da sau 12,000 ana samun tsananin zafin rana bana zuwa yanzu a Amurka, a cewar Hukumar kula da Yanayi da Kimiyyar Tekuna ta Ƙasar (NOAA).

    Kamfanin samar da lantarki mafi girma a Arizona ya ce abokan hulɗarsa sun yi amfani da wutar lantarki a tare fiye da kowanne lokaci a baya, yayin da mazauna jihar suka kunna na'urorin sanyaya ɗaki don kauce wa tsananin zafi.

  3. Tinubu ya ba da umarni a sake nazari kan shirin tallafin N8,000

    ...

    Asalin hoton, BOLA TINUBU/FACEBOOK

    Bayanan hoto, ...

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya umarci da a yi duban tsanaki kan batun bai wa ‘yan kasar mutum miliyan 12 tallafin naira dubu takwas kowanne a tsawon watanni shida domin rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake ya fitar, shugaba Tinubu ya ce a sake yi wa tsarin garanbawul kasancewar gwamnatin mai sauraron koken al’umma ce bisa la’akari da yadda ‘yan kasar suka yi ca a kan al’amarin.

    Wannan ya zo ne sa'o'i bayan Babbar ƙunigyar ƙwadago sunyi watsi da matakin Shugaba Tinubu na neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage raɗaɗin ƙarin farashin man fetur.

    Ƙungiyar ƙwadagon dai sun ƙara da cewa hakan na nufin gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa 'yan Najeriya, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa.

    To sai dai Tinubu ya ce yanzu haka za a fayyace wa ‘yan kasar dukkanin abubuwan da gwamnatin ke Shirin yi wa ‘yan kasar a zuwan tallafin tunda ba batun kudin ba ne kawai.

    Shugaba Bola Ahmed ya bayar da umarnin sakin takin zamani da hatsi ga manoma da magidanta kimanin miliyan 50 a dukkanin jihohin kasar 36 da Abuja.

    Bugu da kari shugaba Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a yi amfani da naira biliyan 500 da majalisar dokokin kasar ta sahhale wa bangaren zartarwa domin rage radadin janye tallafin mai ta hanyar da ta dace.

    Inda ya kara da cewa ‘yan Najeriya za su amfana da tsarin ba tare da la’akari da addini ko kabila ko kuma siyasarsu ba.

    Daga karshe, sanarwar ta ce shugaba Tinubu mutum ne mai sauraron al’umma kuma mai kaunar cigaban ƙasar musamman bisa la’akari da wasu matakai da gwamnatinsa ta dauka a baya-bayan nan kamar batun rage yawan haraji da kafa kwamitin da zai yi kwaskwarima kan tsarin harajin da ke tarnaki ga kasuwanci da zuba jari.

    • Rabon kuɗin rage raɗaɗin tallafin mai ya janyo taƙaddama a Najeriya
  4. Kotu ta ƙi tsawaita umarnin hana gurfanar da Hudu Ari a gaban shari'a

    ...
    Bayanan hoto, ...

    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta ki tsawaita wa’adin wucin gadi da ta bayar a ranar 10 ga Yuli, 2023, na dakatar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), da Babban Lauyan Tarayya. (AGF) daga gurfanar da kwamishinan zabe na jihar Adamawa (REC) Hudu Yunusa Ari da aka dakatar.

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na neman a gurfanar Hudu Yunusa Ari saboda ayyana Sanata Binani, ƴar takarar gwamna na jam’iyyar APC a matsayin wadda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar 15 ga Afrilu, 2023 yayin da ake ci gaba da kidayar kuri’u.

    Kotun ta umurci bangarorin da ke da hannu a wannan lamari, wadanda suka hada da INEC, IGP, da AGF a matsayin wadanda ake tuhuma, da su ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki, har sai an yanke hukunci mai inganci.

    Kotun ta kuma bukaci wadanda ake kara da su gurfana a gabanta a ranar 18 ga watan Yuli domin nuna dalilin da ya sa ba za a tauye su na dindindin ba daga gurfanar da kwamishinan zabe na jihar Adamawa da aka dakatar.

    A yayin zaman na ranar Talata, lauyan INEC, Rotimi Jacobs (SAN), ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara bai yi wa wadanda ake tuhuma umarnin kotu ba a ranar 10 ga watan Yuli.

    Sai dai lauyan Binani, Michael Aondoaka (SAN), ya ce umarnin wucin gadi bai kare ba saboda wadanda ake tuhumar ba su nuna dalili ba kamar yadda kotu ta umarce su.

    Kotun ta ki tsawaita wa’adin wucin gadi na dakatar da gurfanar da Hudu Yunusa Ari da aka dakatar.

    • Ban yi nadamar bayyana Binani a matsayin gwamna ba - Hudu Ari
  5. Hotunan sassan duniya kan yadda suka ga rana mafi tsananin zafi

    Miliyoyin mutane a sassa da dama na duniya suna fuskantar rana mafi tsananin zafi.

    Irin waɗannan lokuta suna faruwa ne a cikin canjin yanayi ne, amma a duniya zafin na ƙara yawa saboda ɗumamar yanayi.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani matashi ya cire rigarsa yana watsa wa kansa ruwa a Phoenix, Arizona, Amurka
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata yarinya daga Koriya ta Kudu na fifita don samun saukin zafi yayin da take jiran mahaifiyarta a wajen La Sagrada Familia Basilica a Barcelona, ​​Spain.
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata tana watsa ruwa a kanta daga wani magudanar ruwa a birnin Alghero, a Sardiniya don samun saukin zafi
    ...

    Asalin hoton, Shutterstock

    Bayanan hoto, Ana fesa wa giwaye ruwa a gidan namun daji da ke Skopje, a arewacin kasar Macedonia, inda yanayin zafi ya tashi sama da 40C.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara a kusa da Prado, California don samun saukin zafin rana
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A Roma, masu yawon bude ido da mazauna suna sheka ruwa akan su don samun saukin rana a wani famfon al'umma
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A Italiya kuma, wani mutum ya hau kan keken sa da fanka lantarki
  6. An kai harin ƙunar bakin wake kusa da shingen jami'an tsaro a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, Rescue1122

    An kai wani harin kunar bakin wake kusa da wata motar jami'an tsaro a yankin Hayatabad da ke Peshawar, babban birnin lardin Khyber Pakhtunkhwa na Pakistan.

    Mutane 8 ne suka jikkata a wannan harin, inda biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

    Cantt SP Waqas Rafiq ya tabbatar da harin kunar bakin wake kusa da motar jami'an tsaro.

    An kai wadanda suka jikkata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Hayatabad.

  7. Ba mu gama sabawa da wancan ƙarin man fetur ba sai ga wani - 'Yar Najeriya

    ...

    Asalin hoton, HUW EVANS PICTURE AGENCY

    Bayanan hoto, ...

    Wani mazaunin Abuja da ya bayyana sunansa da Abubukar kawai ya shaida wa BBC Hausa cewa a shafin sada zumunta ya ga batun ƙara farashin man fetur zuwa N617 da aka yi wayewar garin Talata a Najeriya.

    Ya ce "Gaskiya ana kai talaka bango.

    "Yau za ka tashi da wannan, in an jima ka saya. Ba ka san kuma gobe me za ka je ka tarar ba".

    Ya ce kamata ya yi gwamnati ta duba halin da talakawan Najeriya ke ciki.

    Ita ma wata mazauniyar Abuja ta ce abin takaici ne yadda aka wayi gari da ƙarin kuɗin man fetur ba zato ba tsammani.

    "Babu wani bayani na cewa za a yi ƙarin (kuɗin man). Nawa ne albashin mutum da har za a yi ƙarin man fetur da tsada haka?" Ta tambaya.

    Ta ce da tsakar rana ne kawai ta ga ana maganar ƙarin man fetur ɗin a shafin Tuwita.

    "Kuma ga shi ina buƙatar na sha man a yau. Farashin da na gani ya kai N617, wannan abu ya wuce hankali. Ba mu gama sabawa da wancan ƙarin man fetur ba, sai ga wani. Ni, ban san yadda zan yi ba!"

    An samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai cikin wasu sassan Najeriya, bayan rahotannin ƙara farashin man fetur zuwa sama da N600 a kan lita ɗaya. Tun farko, an wayi gari ne da ƙarin kashi 22% a kan farashin N540 da ake sayar da man fetur ɗin a baya.

    BBC ta fahimci cewa layukan ababen hawan sun faru a gidajen man da ba su kai ga ƙara farashinsu ba. Matakin na zuwa ne yayin da hukumar kayyade farashin man fetur ta kasar ta ce an samu raguwar man da ake sha a kasar daga lita miliyan 65 a kullum zuwa lita miliyan 35 a kullum.

    • Kamfanin NNPC ya ƙara farashin man fetur a Najeriya
  8. Gobarar daji ta ɓarke a lardin Valais na Switzerland

    Wutar daji

    Asalin hoton, Reuters

    Gobarar daji na ci gaba da ɓarna a kudancin ƙasar Switzerland, inda masu kashe wuta sama da 100 ke can suna kokarin shawo kan ta.

    Gobarar ta ɓarke ne jiya da rana kusa da wani ƙauye mai suna Bitsch da ke lardin Valais, inda ta ci gaba da yaɗuwa cikin dare.

    An kwashe mutane sama da 200 da ke zama a ƙauyukan da ke kusa domin tseratar da su.

    Gobarar a yanzu tana ci a wani wuri mai girman kadada 100, wanda ke bai wa ababen wahalar kai wa.

    Ana amfani da jirage masu saukar ungulu mallakin rundunar sojin ƙasar ta Switzerland wajen fesa ruwa kan wutar. Amma iska da hayaki na kawo tarnaki a aikin kashe gobarar.

  9. Sojoji sun ce sun kashe ƴan IPOB biyu

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Army

    Hadin gwiwar dakarun Bataliya ta rundunar sojin Najeriya, 'yan sandan Najeriya da kuma jami'an tsaro na farin kaya sun kashe mayakan IPOB/ESN guda biyu tare da kama wasu biyar bayan wata mumunar arangama da suka yi a ranar Litinin 17 ga watan Yuli 2023 a unguwar Fuji Junction,Asaba, Delta state.

    Ganawar ta biyo bayan kiraye-kirayen al'ummar garin suka yi da kai ƙaran ‘yan ta’adda sun kai wa garin hari, inda dakarun hadin gwiwa suka mayar da martani cikin gaggawa.

    ‘Yan ta’addan sun kasa jurewa hadin gwiwar dakarun da karfin wutar da sukayi ta sakewa inda wasu mutane biyu daga cikin su suka mutu cikin harbe-harben sojojin, yayin da wasu kuma suka tsere zuwa maboyarsu da ke kusa da kogin Okpanam.

    Amma dakarun da ke fafatawa da ‘yan ta’addan sun yi nasarar bibiyar su a wani gida da ke kusa da kogin Okpanam, inda suka kama su.

    Sojojin sun kuma kwato makamai da dama daga ƴan ta'addan.

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Army

    Muna rokon jama'a da su ci gaba da ba jami'an tsaro hadin kai ta hanyar samar da bayanan da suka dace don tallafa wa ayyukansu na tunkarar kalubalen tsaro.

    Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya yaba wa rundunar da hadin gwiwar da suka yi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yin hakan, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

    • Sojojin Najeriya sun kama babbar mota maƙare da makamai
  10. 'Yan ci-rani sun makale a hamada ana tsaka da zafin rana a Tunisia

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Ana sa ran wasu yanayi mafi zafi a yau a Tunisiya, wanda kusan kashi daya bisa uku na cikin hamadar Sahara ya rufe.

    Sahara wuri ne wanda ba shi da dadin rauwa ga ɗan'adam, amma duk da haka bakin haure kan tsallaka shi da fatan isa tekun Mediterranean da kuma Turai.

    Biyo bayan tashe-tashen hankula na nuna wariyar launin fata a birnin Sfax na kasar Tunisiya, wasu 'yan Afirka kudu da hamadar Sahara sun yi gudun hijira zuwa wani yanki mai cike da sojoji da makamai da ke kan iyaka da Libya.

    Jami'ai a Libya sun kuma zargi Tunisia da jefar da daruruwan bakin haure kan iyaka a cikin hamada - ba tare da abinci ko ruwa ko kuma matsuguni ba.

    Libya da Majalisar Dinkin Duniya sun ce sun ceto bakin haure daga kan iyaka.

    Tunisiya - wacce a baya-bayan nan ta sa hannu kan wata yarjejeniya ta bakin haure da kungiyar tarayyar Turai - ba ta ce komai ba kan zargin Libya.

    • Baƙin-Haure: Tunisiya ta ƙulla yarjejeniyar tsaron kan iyaka da Tarayyar Turai
  11. Tsananin ƙaranci wutar lantarki a Gaza ya haifar da zanga-zanga

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Ƙarancin wutar lantarki, sakamakon zafin rana a Zirin Gaza, ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna yankin tare da haifar da wani gangami ta intanet game da tashar wutar lantarki ɗaya tilo da ake da ita a yankin.

    Yanayin zafin ya zarce salsiyas 38 a yankin da ke da iyaka da Tekun Bahar Rum da Isra'ila da kuma Masar, inda mutane sama da miliyan biyu ke rayuwa.

    Gaza na samun wutar lantarki kusan megawatt 120 a rana daga Isra'ila, kuma tashar lantarki guda ɗaya ta yankin ce ke samar da karin megawat 60. Amma hukumomin yankin sun ce Gaza na bukatar kusan megawatt 500 a lokacin watannin zafi.

    Wasu fusatattun mazauna yankin sun yi korafi a kafofin sada zumunta kan yadda ake ci gaba da katse lantarkin, wanda zai iya kai wa tsawon sa'a 12 a rana, sannan sun yi kira a fara gudanar da aikin ba da wuta ta yadda ya kamata.

    Har ila yau, suna nuna bacin rai ga Ƙungiyar Hamas da ke rike da ragamar mulkin yankin - tare da karfafa gwiwar jama'a su fito su ɗaga murya ga mahukunta.

  12. NLC ta yi watsi da shirin Tinubu na biyan 'yan Najeriya N8,000

    ...

    Asalin hoton, OTHER

    Bayanan hoto, ...

    Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi Allah-wadai da matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman amincewar majalisar dokoki don karbar rancen naira biliyan 500 daga Bankin Duniya da nufin aiwatar da shirin da ta kira na bogi don rage raɗaɗin ƙarin farashin man fetur da aka yi babu lissafi.

    Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya fitar ranar Talata.

    Sanarwar ta ce, "Shawarar biyan naira 8,000 ga magidanta miliyan 12 mafiya talauci a Najeriya tsawon wata shida cin mutunci ne da kuma ba'a ga haƙuri da imani da muke da shi a kan tattaunawa da gwamnati."

    "Rashin tunani ne gwamnatin da ta haddasa tsananin wahala a kan mutane cikin ƙasa da wata biyu da hawanta mulki, sannan ta zo ta kawo wani ƙuduri wanda ƙarara zai saka wa masu kuɗi da ke riƙe da muƙaman gwamnati, ba tare da duba halin da talakawa ke ciki ba."

    "Abin da hakan ke nufi shi ne gwamnati na neman hanyoyin da za ta sace dukiyar talakawa 'yan Najeriya, su kuma masu kuɗi su ƙara kuɗancewa."

    NLC ta ce ba za a lamunci waɗannan ƙudurori ga ma'aikatan Najeriya ba kuma matakin ya fi kama da kama-karya don haka ya saɓa da tsarin dimokraɗiyya.

    "Muna nanata cewa ba mu da ƙwarin gwiwa kan hanyar da aka bi aka tattara bayanan da ba sa canzawa na gidajen mutanen da suka fi talauci su miliyan 12, sannan ba mu da ƙwarin gwiwa a kan tsare-tsare da za su bi wajen raba wannan kuɗi."

    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur

    Sanarwar ta ƙara da cewa matuƙar gwamnati ba ta son dakatar da irin waɗannan matakai da suna rage raɗaɗi, za su tilasta mu sae nazarin matakinmu na tattaunawa da gwamnati a kan wannan batu mai cike da ɓacin rai kuma za mu yi gaban kanmu.

  13. Koriya ta Arewa ta kama jami’in sojan Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sojan Amurka ya ƙetara iyaka zuwa cikin Koriya ta arewa, inda ake da yaƙinin cewar hukumomin ƙasar na tsare da shi.

    Bayanai sun ce sojan ya ƙetara zuwa Koriya ta Arewar daga Koriya ta Kudu ne ba tare da izini ba.

    Jami’in yana rangadi ne a yankin ‘tudun-mun-tsira’ da ke tsakanin ƙasashen biyu, kafin ya ƙetara iyakar.

    Kafar labarai ta CBS ta ce tun asali ana yunƙurin mayar da sojan gida Amurka ne domin fuskantar hukunci kan wani laifi da ya aikata, inda ya sulale daga filin jirgi tare da tafiya yankin na kan iyaka.

  14. Ana sa ran yanayin zafi zai kai maki 46 a Turai

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Zafin yanayi da ke tsananta har zuwa maki 40 a ma’aunin salshiyas lamari ne da ba a taɓa ganin irin sa ba a manyan birane na kudancin Turai.

    Amma hakan ba sabon abu ba ne a wurare kamar Gabas ta tsakiya da Asiya, inda akan ga irin wannan yanayi a kai – a kai.

    Misali, a Bagadaza, babban birnin Iraki, matsakaicin zafin yanayi kan kai maki 44 a ma’aunin salshiyas a watan Yuni da Agusta.

    Haka nan a Delhi na ƙasar Indiya, inda a wasu lokutan yanayin zafi kan kai maki 45 a ma’aunin salshiyas.

    To amma ta yaya mutanen irin wannan yankuna ke jure wa yanayin?

    A kusan kowane gida a waɗannan birane za ka ga cewa akwai na’urar sanyaya ɗaki kala-kala.

    Wasu kuma kan sha abubuwa masu sanyi, kamar askirin da kuma yin wanka a kai-a kai.

    Sai dai waɗanda ba su samun wutar lantarki sosai na fama a lokutan zafi.

    Sai dai mutane da dama a irin waɗannan yankuna ba su cika fita da rana ba a lokutan zafi, sai idan ya zama dolen dole.

  15. Najeriya na shirin yi wa dabbobi riga-kafin cutar Anthrax, Daga Ibrahim Isa

    Riga-kafin dabbobi

    Asalin hoton, AFP

    Najeriya na shirin yi wa dabbobin ƙasar huji ko riga-kafin cutar Anthrax bayan ɓullar cutar a wata gona da ke Suleja a jihar Niger.

    Ma'aikatar noma a Najeriya ta ce ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile cutar da hana yaɗuwarta, kuma gonar da ake magana, wadda ake kiwon shanu da tumaki da Awaki, har ta ɗauki matakan keɓe ta tare da sa'ido a kan ta.

    Tun a watan Yunin da ya wuce, gwmanatin Najeriyar ta ankarar da al`ummar ƙasar game da ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo. Wannan ne ma ya sa mahukunta suka gargaɗi al`umma da suke dinga ɗaukar matakan kariya.

    Wani kwararren likitan dabbobi a Najeriya, Dakta Abubakar Sulaiman, ya ce duk da cewa cutar ba ta da saurin yaɗuwa, amma bil`adama ma kan harbu da ita idan ya ci nama ko gogayya da jikin dabbar da ta harbu.

    Ya ce ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kariya daga cutar, ita ce yi wa dabbobi huji kamar yadda mahukunta a Najeriyar suka yi aniya.

    A ƴan makwannin da suka wuce ne aka samu labarin ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo.

  16. Ba zan sake buga wa kungiyar Turai wasa ba - Ronaldo

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Cristiano Ronaldo ya ce ba zai sake komawa nahiyar Turai buga tamaula ba, ya kuma kara da cewar gasar kwallon kafar Saudi Arabia ta dara ta Amurka daraja nesa ba kusa ba..

    Lionel Messi ya koma taka leda a Inter Milami mai buga gasar Amurka, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St Germain a karshen kakar 2022/23.

    Ronaldo, tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus ya koma Al Nassr cikin watan Disamba kan kwantiragin kaka biyu da rabi daga Manchester United.

    Dan kwallon tawagar Portugal ya ce ya buge hanyar da fitattun 'yan kwallo ke komawa buga gasar Saudi Arabia - yana sa ran 'yan wasa da dama nan gaba za su koma can da taka leda.

  17. Tsohon shugaban Kongo ya musanta bai wa ƴan tawaye mafaka

    Kongo

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, A zargi ƴan tawayen ADF da kai hare-hare a baya-bayan nan kan wata makaranta a yammacin Uganda da ke iyaka da Kongo

    Tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Joseph Kabila, ya yi watsi da zargin da makwaɓciyarta Uganda ta yi masa na bai wa kungiyar 'yan tawayen Islama mafaka tare da ba ta damar wawure albarkatun ƙasar.

    A makon da ya gabata shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya ce Mista Kabila ya bai wa kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) damar kafa manyan sansanoni da hakar zinare da kuma sayar da katako.

    An kafa kungiyar ta ADF ne a shekarun 1990 kuma ta ɗauki maƙamai don yakar shugaba Museveni, bisa zargin zaluncin da ake yi wa musulmi.

    Museveni

    Asalin hoton, AFP

    Kabila ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa "zargin karya na rashin adalci da shugaba Museveni ke yi, wanda ɗaya ne daga cikin masu tayar da zaune tsaye a yankin, abin dariya ne kawai da nufin raba hankalin al'ummar Kongo tare da raba kawunansu."

    A bara ne wata babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta umarci Uganda da ta biya gwamnatin Kinshasa ɗaruruwan miliyoyin daloli a matsayin diyya ga ta’asar da aka yi a lokacin yakin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

    Rikicin baya-bayan nan ya zo ne wata guda bayan da aka zargi 'yan tawayen ADF da kashe ɗalibai sama da 42 a wata makaranta a yammacin Uganda.

  18. Matashi ya shaƙe mahaifiyarsa har ta mutu a Ogun

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Wani matashi ɗan shekara 32, mai suna Samson Sikiru,ya shaƙe mahaifiyarsa har ta mutu a garin Ijebu Ode da ke jihar Ogun.

    Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Omotola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin.

    Ana dai zargin matashin da tu'ammali da ƙwayoyi.

    Kanin wanda ake zargi da kashe mahaifiyar tasu, wanda yake aikin gadi, shi ya sanarwa makwaɓtansu abin da ke faruwa lokacin da ya dawo ya samu gawar mahaifiyarsu a kwance.

    Samson wanda ya kasance ba ya gida na tsawon shekaru, ya dawo ne domin yin bikin babbar Sallah tare da mahaifiyarsa makonni biyu da suka wuce.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an kama matashin ne bayan da makwaɓtansu suka gano cewa shi ya kashe mahaifiyar tasa, inda daga nan aka miƙa shi hannun ƴan sanda.

    Kakakin ƴan sandan jihar ta Ogun, Omotola Odutola ta ce matashin yana da lalura ta kwakwalwa.

    Ta kuma ce an kasance ana ɗaure lokuta da dama domin kada ya ji wa kansa ko mutane ciwo.

  19. Laraba ce 1 ga watan Muharram

    Watan Musulunci

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da cewa ranar Laraba ita ce ɗaya ga watan Muharram, abin da ke alamta shiga sabon watan Musulunci.

    Cikin wata sanarwa da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce bayan gaza ganin watan a yau Talata.

    Hakan na nufin cewa yau Talata 18 ga watan Yuli ta zama 30 ga watan Zul Hijjah.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Farashin man fetur ya tashi a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin litar man fetur ya tashi a sassa daban-daban na Najeriya a safiyar yau Talata.

    Masu ababen hawa a arewaci da kudancin ƙasar duk sun bayyana yadda farashin ya tashi daga yadda aka saba gani.

    Haka nan an ga dogayen layukan ababen hawa a Abuja, babban birnin ƙasar.

    A Abuja, babban birnin ƙasar wani gidan mai na kamfanin NNPC tsakiyar birnin ya ƙara farashin litar man zuwa naira 617 haka nan ma wasu gidajen man na ƴan kasuwa.

    Hakan ya yi sama idan aka kwatanta da naira 539 da ake sayarwa a baya.

    Wani mazaunin Jos, babban birnin jihar Filato ya ce ya sayi litar mai ɗaya a kan naira 617 a safiyar Talata, sama da naira 537 da aka saba saye gabanin hakan.