Ganduje ya ƙai ƙarar gwamnan Kano wurin Tinubu kan rusau - Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya bayyana wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu halin da ake ciki kan maganar rushe-rushe a jihar Kano.
Ya kuma ce ya miƙa koke kan lamarin ga sifeta-janar na ƴan sandan ƙasar domin ganin an ɗauki mataki.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da manema labaru bayan wata tattaunawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana abin da gwamnatin sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ke yi ta hanyar rushe gine-gine da abin da ya saɓa wa doka.
Ya kuma nuna matuƙar ɓacin ransa ga tsohon gwamnan jihar Rabi'u Musa Kwankwaso inda ya yi barazanar marin sa.
Ya ce "inda na haɗu da shi da na mare shi.
Dangantaka dai ta yi matuƙar tsami tsakanin Ganduje da Kwankwaso tun bayan da suka raba gari a shekarun baya bisa saɓanin fahimta.
Tun bayan kama aiki, gwamna Abba Kabir ya bayar da umurnin rushe wasu gine-gine waɗanda ya zargi tsohuwar gwamnatin ta Abdullahi Ganduje da assasawa ba bisa ƙa'ida ba.



















