'Yan sanda sun kama mutum biyar bisa zargin cire sassan jikin gawarwaki

Asalin hoton, TWITTER/@POLICENG
Rundunar 'yan sandan jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wasu mutum biyar da take zargi da kasancewa 'yan ƙungiyar asiri da suka yi shura wajen tono kaburbura domin cire sassan jikin gawarwaki don yin tsafi.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a birnin Abeokuta.
Oyeyemi ya ce an kama mutanen ne bayan da suka samu bayan sirri cewa gungun mutanen za su fita neman sassan jikin mutane a cikin Ososa.
Inda ya ce nan take jami'an 'yan sanda ƙarƙashin jagorancin Baturen 'yan sandan Odogbolu Godwin Idehai suka dirar musu tare da kama mutum biyar daga cikinsu.
“Bayan da aka fara tuhumar ne kuma mutanen suka bayyana wa 'yan sanda cewa sun daɗe suna aikata wannan laifi, inda suke tona kaburbura domin cire sassan jikin gawarwaki,'' in ji Oyeyemi.
“Sun ce sukan sayar da sassan jikin gawarwakin ga wasu mutane da ke amfani da su wajen yin tsafi domin samun kuɗi'', in ji shi.











