An samu ɓarkewar amai da gudawa a Gabashi da Kudancin Afirka – UNICEF

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya damu matuƙa game da ɓarkewar cutar amai da gudawa a sassan gabashi da kudancin Afirka.
Lamarin kuma ya shafi fiye da mutane dubu sittin tare da halaka mutum dubu ɗaya da ɗari bakwai.
Malawi da Mozambique ne ƙasashen da lamarin ya fi yin muni.
Wani babban jami'in UNICEF ya faɗa wa BBC cewa cibiyoyin kula da lafiya da ke farfadowa daga mummunan tasirin anobar korona a yanzu suna fafutukar daƙile yaɗuwar cutar.
Ya faɗa wa BBC cewa sauyin yanayi na haifar da ƙaruwar cutar saboda yawan fari da ambaliyar ruwa da ke shafar muhalli da ruwa.
Ministoci daga ƙasashe 11 suna ganawa a Malawi domin samar da dabarun tunkarar cutar da ke yaɗuwa.

















