Mutum goma sun rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.

    Sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kaimu.

    Kafin nan za ku iya duba kasan wannan shafi domin sake karanta labaran da muka wallafa muku.

    A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Philippines ta bukaci manyan jami'an 'yan sandan ƙasar da su yi murabus

    Gwamnatin Philippines ta bukaci manyan jami'an 'yan sandan ƙasar da su miƙa takardun murabus bisa radin kai, a wani mataki na yaki da masu safarar muggan kwayoyi.

    Sakataren harkokin cikin gida Benhur Abalos, ya bukaci masu mukaman Kanar da Janar su dauki wannan mataki, ya yin da wani kwamiti na musamman da aka kafa zai yi aikin tattara bayanansu.

    Mr Abalos ya ce wannan murabus ya jami'an da aka samu shaidar su na da hannu a cinikin wata nau'in kwaya ne kadai za amince.

    Ya kira matakin da tankaɗe da rairaya a fannin jami'an tsaron Philippines domin cire bara gurbi a cikinsu.

  3. Yakin Ukraine: Dakarun Rasha sun lalata garin Bakhmut

    Bakhmut

    Wani kwamandan sojin Ukraine a garin Bakhmut da yaki ya ɗaiɗaita, ya shaidawa BBC irin yadda aka lalata yankin da hare-hare.

    Ya ce bai taba ganin dakarun Rasha na yaki kan jiki kan karfi a ko ina ba kamar Bakhmut, inda suke kutsawa cikin wuta, da sake dannwa ko da kuwa su na ganin 'yan uwansu na faduwa kasa a mace sakamakon martanin sojin Ukraine.

    Wakiliyar BBC ta ce dakarun Rasha na amfani da makaman Tarayyar Soviet, zungureriyar bindiga ce da ke harba makaman Atilari.

  4. Kotu a Legas ta tura likita gidan yari bisa zargin yin lalata da 'yar shekara 16

    Wata kotun sauraron kararraki kan laifuka na musanman da keta mutuncin yara ƙanana ta jihar Legas, ta tura wani babban likita gidan yari, bisa zarginsa da yin lalata ta baki da wata yarinya ‘yar shekara goma sha shida.

    An gabatar da Dokta Olufemi Olaleye, manajan daraktan cibiyar gidauniyar kula da masu cutar daji, a gaban kotu; to sai dai a tsawon zaman ya musanta zargin da ake yi ma sa.

    Ku danna kasa domin sauraron rahoton wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman.

    Bayanan sautiKotu a Legas ta tura likita gidan yari bisa zargin yin lalata da 'yar shekara 16
  5. Cocin Anglika ta yi Alla-wadai da lalata kaburbura sama da 30 a Birnin Kudus

    Jerusalem Cemetary

    Archbishop na Canterbury, Justin Welby, ya bi sahun shugabannin addinai da yin allawadai da lalata kaburbura sama da 30 a wata makabarta da ke birnin Kudus kan zargin batancin addini.

    Archbishop din Angalika a Kudus,HosamNaoum, ya ce a dan tsakanin nan ana samun karuwar kai wa mabiya addinin Kirista hare-hare, da wuraren ibadarsu.

    Wakiliyar BBC ta ce hotunan tsaro na CCTV sun nuna maharan, sanye da tufafin malaman yahudawa su na ta kai kawo cikin makabartar da tsalle daga wannan kabari zuwa wancan ba tare da kowa ya zo wurin ba.

    Daga bisani suka rika cire allon da ake sanyaw kan kabari mai dauke da sunan mamaci da bayanansa. Sun kuma dinga amfani da manyan duwatsu domin ruguza wasu kaburbura a jiya Lahadi.

  6. INEC ta karbi kashin karshe na na'urorin tantance masu zaɓe

    INEC

    Asalin hoton, FACEBOOK/INEC NIGERIA

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta karbi kashin karshe na na'urorin tantance masu zabe gabanin babban zaben ƙasar da ke tafe.

    A cikin wata sanarwa da Babban Kwamishina a Hukumar, Festus Okoye ya fitar, kwamishinan ya ce shugaban Hukumar Zaɓen ne farfesa Mahmood Yakubu tare da wasu manyan kwamishinoni a hukumar suka karɓi na'urorin a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja jiya Talata.

    Hukumar zaɓen ta samar da filayen jirage hudu a Abuja da Kano da Legas da kuma Fatakwal a matsayin wuraren rarraba na'urorin cikin sauki zuwa sauran jihohi.

    Har ila yau, sanarwar ta ce yanzu hukumar na'urorin tantance masu zaɓe da za a kai zuwa rumfunan zaɓe a fadin ƙasar .

    INEC

    Asalin hoton, FACEBOOK/INEC NIGERIA

  7. China na ɓoye ainihin alkaluman cutar korona - WHO

    China Covid

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi gargadin cewa China na ɓoye ainihin tasirin da annobar korona ta yi wa ƙasar - musamman ma alkaluman wadanda suka mutu.

    Cire yawancin takunkumai da ƙasar ta yi a watan da ya gabata, ya janyo ƙaruwar mutane masu kamuwa da cutar.

    Sai dai China ta daina wallafa alkaluman masu cutar a kowace rana, inda ta sanar da cewa mutum 22 ne kadai suka mutu sakamakon korona tun watan Disamba.

    Darektan bayar da agajin gaggawa na hukumar, Dr Michael Ryan, ya ce abin da suke gani a China kan cutar korona ba shi ne ainihin abin da yake faruwa ba musamman idan aka duba wadanda ake kwantar wa a asibiti da ke bukatar kulawar gaggawa da kuma wadanda ke mutuwa sanadin cutar.

  8. Mutum goma sun rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

    CANOE

    Asalin hoton, OTHER

    An gano gawarwakin mutum goma da suka rasu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi, inda masu aikin ceto na can suna ci gaba da kokarin lalubo wasu mutanen wani jirgin ruwa da ya kife da su a garin Samanaji na Karamar Hukumar Koko-Bese.

    Jirgin dai yana dauke da fiye da mutum dari, amma an samu nasarar ceto mafi yawa daga ciki.

    Alhaji Yahaya Bello Koko, wanda ya kasance shugaban Karamar Hukumar Koko Besi, ya tabbatar wa BBC cewa hadarin ya faru ne lokacin da mutanen ke komawa gida daga gona.

    Ya ce mutane sun cika makil cikin jirgin tare da mata da kuma yara, inda jirgin ya rabe biyu a tsakiyar ruwa kasancewar tsohon jirgi ne.

    Shugaban karamar hukumar ya ƙara da cewa an ceto mutane fiye da 80, inda aka gano gawarwaki goma, akwai kuma goma har yanzu ana neman su.

  9. 'Yan sandan Zamfara sun kashe ɗan bindiga, sun kwato makamai

    Police

    Asalin hoton, OTHER

    Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da kashe wani dan bindiga tare kuma da kwato makamai a kan hanyar Gusau bayan samun rahoton yunkurin kai hari da 'yan bindigar suka yi.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce a ranar 1 ga watan Janairu ne suka samu nasarar fatattakar 'yan bindigar zuwa cikin daji bayan artabu na tsawon lokaci, inda suka kwato bindigar AK-47 da harsasai 104 da kuma wasu abubuwan yin asiri daga hannun 'yan bindigar.

    Har ila yau, sanarwar ta ƙara da cewa wata rundunarta ta musamman ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata ta'addanci da garkuwa da mutane da kuma satar shanu, ciki har da wani mai bai wa 'yan bindiga bayanai da ke ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi na jihar.

    Kakakin 'yan sandan ya ce wadanda ake zargin na hannun 'yan sanda, inda suke bayar da bayanai da za su kai ga kamo sauran masu laifi, inda ya ce bayan haka za a tura su zuwa kotu domin yi musu hukunci bayan kammala bincike.

  10. Kenya na shirin samar wa 'yan ƙasar kwaroron roba kyauta

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Kenya, ta tabbatar da wa 'yan ƙasar cewa akwai isassun kwaroron roba da ta samar bayan ƙarancinsa na makonni.

    Sakatariyar lafiyar ƙasar, Susan Nakhumicha, ta sanar a yau Laraba cewa an samar da kwaroron roba miliyan 38 domin raba wa mutane,

    “Muna aiki don tabbatar da cewa sun kai ga mutane a cikin ƙankanin lokaci,'' in ji Ms Nakhumicha.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    'Yan gwagwarmaya sun soki gwamnatin ƙasar bisa jinkiri wajen samar da kwaroron roban, inda suka ce hakan na sanya rayukan mutane cikin hadari.

  11. Mozambique ta samu kujera a kwamitin tsaro na MDD

    Mozambique

    Asalin hoton, Getty Images

    Mozambique ta maye gurbin ƙasar Kenya a kwamitin tsaro na MDD, inda ta alƙawarta bayar da haɗin kai wajen yaƙi da ta'addanci.

    Ƙasar za ta kwashe shekara biyu a kan kujerar wadda ba ta dindin ba ce a kwamitin tsaron na MDD.

    Jakadan ƙasar na Majalisar Ɗinkin Duniya Pedro Comissário ya ce: "Za mu yi ƙoƙari wajen yaƙar ta'addanci a duniya"

    Ƙasar dai ta kwashe shekara biyar tana yaƙi da masu iƙirarin jihadi a lardin Cabo Delgado da ke arewacin ƙasar.

    Yaƙin da ya yi sanadin kashe kusan mutum 4,000 tare da raba sama da mutum miliyan ɗaya da muhallansu.

    Mista Comissário ya ce ƙasar za ta yi ƙoƙari wajen kawo sauyi a kwamitin tsaron ta yadda za a magance ''matsalolin Afirka''

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na da mambobin dindin guda biyar - waɗanda suka haɗar da Amurka da Rasha da Faransa da Birtaniya da kuma China - sai kuma mambobi 10 waɗanda ake sauya su lokaci zuwa lokaci.

  12. China za ta aike da magunguna zuwa asibitocin karkara a ƙasar

    China

    Asalin hoton, others

    Hukumomi a China sun ce za su aike da kayan aiki da magunguna zuwa asibitocin da ke yankunan karkara a ƙasar, a daidai lokacin da ake fargabar za a samu ƙaruwar cutar korona a kasar.

    Hukumar lafiyar ƙasar ta ce yawancin mazauna karkara ba a yi musu riga-kafin cutar korona ba.

    Tuni wasu ƙasashe suka fara ɗaukar mataki mai tsauri kan waɗanda suka shigo ƙasar daga China.

    Mai magana da ma'aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta ce bai kamata a siyasantar da batun ba.

    Ta ce ''a kodayaushe China ta amince ƙasashe su ɗauki matakin kariya daga korona amma ta fannin kimiyya, ta amfanin da hanyoyin da suka dace, kada abin ya zama makarkashiyar siyasa''.

    Wasu rahotanni na cewa yawancin biranen da attajiran ƙasar ke ciki, ba su daɗe da farfaɗowa daga zagayen farko na ɓarkewar korona a China ba.

  13. Gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur a ƙarshen watan Yuni

    ZAINAB AHMED

    Asalin hoton, TWITTER/ ZAINAB AHMED

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga ƙarshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a ƙasar.

    Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuɗin shekarar 2023.

    Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur ɗin a cikin wata shida na farkon shekarar 2023.

    Ministar ta ƙara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.

  14. Amfani da wayar hannu ne ya yi sanadin kashe sojojinmu 89 - Rasha

    Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta ce harin da aka kai kan dakarunta a ranar sabuwar shekara, ya faru ne sakamakon amfani da wayar hannu da sojojin nata ke yi.

    Jamai'an Rasha sun ce harin wanda ya yi sanadin mutuwar dakarun Rasha 89, ya faru ne saboda saɓa wa dokar amfani da wayar ta hannu, kamar yadda Rashar ta bayyana.

    ''Komawa kan wayoyin hannu tare da yawaitar amfani da su zai bai wa maƙiya damar gano inda kake'', kamar yadda jami'an na Rasha suka bayyana.

    Wannan dai shi ne adadi mafi girma da Rasha ta taɓa amincewa da yin asarsu tun bayan mamayar a farkon shekarar da ta gabata.

    To sai dai Ukraine ta ce sojojin Rasha 400 ta kashe tare da raunata 300, a harin da ta kai kan sansanin sojin na Rasha da ke garin Makiivka, da ke yanzkin Donetsk.

  15. Majalisar wakilai ta gargaɗi EFCC kan sayar wa masu laifi kadarori

    majalisa

    Asalin hoton, others

    Kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke kula da kadarorin da hukumomin gwamnatin ƙasar suka ƙwato daga hannun masu laifi ya gargaɗi hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC da kada ta sayar wa masu laifin kadarorin da a yanzu take gwanjonsu.

    Shugaban kwamitin Adejoro Adeogun ya ce kwamitinsa ya gano cewa akwai yiyuwar waɗanda aka ƙwace wa kadarorin su biyo ta bayan fage domin sake mallakar kadarorin.

    Mista Adeogun ya ce kwamitin nasa zai ci gaba da sanya ido domin sanin waɗanda ake sayar wa da kadarorin.

    Cikin watan Disamban da ya gabata ne hukumar EFCC ta fara gwanjon ababen hawa 649 a jihohin ƙasar tara da birnin tarayya.

    Sauran kadadrorin da hukumar ta bayyana yin gwanjon su sun haɗar da ƙananan jiragen ruwa 15, da wani babban jirgin ruwa na dakon kaya a jihohin Rivers da Delta da kuma Legas.

    Haka kuma a watan na Disamba ne hukumar ta bayyana yin gwanjon manyan gidaje masu alfarma 144, tare da filaye da ta ce ta ƙwace daga hannun 'yan siyasa, da masu riƙe da madafun iko, da kuma masu zamba ta intanet a sakamaon laifukan almundahana da zamba cikin aminci da aka same su da aikatawa.

  16. Ronaldo ya yi saɓul-da-baka a Saudiyya

    Ronaldo

    Asalin hoton, GOAL

    Shahararren ɗan ƙwallon ƙafar duniya Cristiano Ronaldo ya yi tuntuɓen harshe a lokacin da ake gabatar da shi ga sabuwar ƙungiyar da ya koma ta Al Nassr ranar Talata,

    Ronaldo ya yi suɓul-da-baka a gaban magoya bayan ƙungiyar inda ya ce 'South Afirka' a maimakon 'Saudi Arabiya'.

    Ɗan wasan ya koma Al Nassr ranar Juma'a bayan da ya raba-gari da tsohuwar ƙungiyarsa Manchester United.

    Ronaldo ya ce: "Wasan ƙwallon ƙafa wani abu ne na daban, dan haka zuwana 'South Afrika' ba shi ne ke nuna cewa ta-ƙare min ba''

    ''Wannan shi ne dalilin da ya sa nake son samun sauyi, haƙiƙa ban damu da abin da mutane ke cewa ba'', kamar yadda Ronaldo ya bayyana wa manema labarai a lokacin da aka gabatar da shi a birnin Riyadh.

    Ya ƙara da cewa: "Na samu komai, na yi wasa a manyan ƙungiyoyi a Turai, a yanzu kuma lokacin buɗe sabon babi ne a Asiya''.

    Bayan taron manema labaran, ɗan wasan ya sanya sabuwar rigar wasansa ta ƙungiyar a filin wasan a gaban dubban magoya bayanta.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Mutum tara sun mutu a tagwayen harin bom a Somaliya

    Magadishu

    Asalin hoton, Reuters

    Akalla mutum tara ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata a wasu tagwayen hare-haren bom da aka kai tsakiyar Somaliya.

    Rahotonni sun ce an kai harin ne da ƙananan motoci da sanyin safiyar ranar Laraba a garin Mahas.

    To sai dai an samu rahotonni masu cin karo da juna game da inda aka nufa da harin.

    Wani shafin intanet da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Shabab ya ce sojojin Somaliya aka nufa da harin, inda wani shafin intanet mai zaman kansa ke cewa an kai harin ne kan wani gidan abinci, a yayin da kafar yaɗa labaran gwamnati ke cewa an kai harin ne kan shagunan fararen hula.

    Jami'an tsaro na gudanar da bincike game da lamarin.

  18. An tsinci gawar wani mutum kwana uku bayan kashe iyayensa

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwanaki uku bayan kashe wasu ma'aurata a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, an gano gawar ɗansu a cikin wani kogi a jihar.

    Wasu mutane ne da ba a san ko su wane ne ba suka kashe ma'auratan masu suna Kehinde da Bukola Fatinoye a birnin Abeokuta na jihar a ranar sabuwar shekara bayan da suka dawo daga addu'o'in shiga sabuwar shekara.

    Haka kuma rahotonni sun ce maharan sun ƙona gawarwakinsu da gidansu da ke birnin na Abeokuta, tare kuma da sace ɗan nasu inda kuma suka jefa shi cikin kogin.

    An ce Kehinde ma'aikacin babban bankin Najeriya ne CBN, yayin da matar tasa ke aiki a jami'ar koyar da harkokin noma ta tarayya da ke Abeokuta.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Abimbola Oyeyemi, rundunar na gudanar da bincike kan lamarin domin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aika-aika.

  19. Sama da mutum miliyan shida ba su karɓi katin zaɓensu ba - INEC

    Katin zaɓe

    Asalin hoton, INEC

    A yayin da ya rage ƙasa da mako takwas a gudanar da babban zaɓe a Najeriya , Hukumar zaɓen ƙasar ta ce akwai aƙalla mutum miliyan 6.7 da ba su karɓi katunan zaɓensu ba.

    Wani rahoto da ya fito daga ofisoshin INEC a jihohin ƙasar ranar Talata ya nuna cewa akwai katuna kusan miliyan 6.7 da ke ƙunshe cikin ofisohin INEC a jihohin ƙasar 17 da kuma babban birnin tarayyar ƙasar Abuja.

    Tun da farko dai Hukumar Zaɓen mai Zaman ƙanta a Najeriya ta bayyana cewa za ta fara rabar da katunan zaɓen daga watan Disamban da ya gabata zuwa ranar 22 ga watan Janairun da muke ciki.

    Babban kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri'a, Festu Okoye ya faɗa a wata sanarwa da ya fitar cewa daga ranar 6 zuwa 15 ga watan Janairu za a mayar da katunan zuwa mazaɓu domin sauƙaƙa wa jama'a karɓar katin.

  20. Ana zargin fararen hula da shirya juyin mulki a Gambiya

    Gambiya

    Asalin hoton, AFP

    'Yan sandan Gambiya na tuhumar wasu fararen hula biyu tare da jami'in ɗan sanda ɗaya da hannu cikin zargin yunƙurin juyin mulki da aka yi cikin watan da ya gabata.

    Ana zargin mutanen uku da haɗin baki da cin amanar ƙasa da rashin bayar da bayanai game shirin yunƙurin juyin mulkin domin tunɓuke shugaban ƙasar Adama Barrow daga kan mulki a watannin Oktoba da Disamba.

    Wannan dai babban laifi ne da ka iya janyo musu ɗaurin shekaru a gidan yari.

    Sai dai duka mutanen uku sun musanta zargin.

    A makon da ya gabata, babban mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro ya ce ana zargin fararen hular da bayar da taimakon kuɗi ga masu yunƙurin shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba.

    A watan Disamba gwamnatin ƙasar ta ce ta samu nasarar daƙile yunƙurin juyin mulki tare da kama sojojin da ake zargi da hannu a ciki.

    Wannan dai shi ne karo na farko da aka gurfanar da waɗanda ake zargi da juyin mulki a gaban kotu a ƙasar.

    Su kuma jami'an sojin da ake zargi da hannu za a kai su kotun soji ne domin yi musu shari'a.