Ba za mu ƙara kuɗin man fetur ba a yanzu - Gwamnatin Najeriya

Wannan shafi na kawo maku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi na yau Alhamis.

    Mu haɗu da ku gobe don kawo wasu sababbi daga sassan duniya.

  2. Babu abin da zai hana mu taimaka wa Ukraine - Sifaniya

    Ministar harkokin tsaron Sifaniya Margarita Robles ta ce babu wani tashin hankali da zai hana ƙasarta taimaka wa Ukraine.

    Tana magana ne a yayin da aka gano wata takarda ƙunshe da bam a ƙasar wadda aka ƙwace a ofishin Jakadancin Amurka da ke Madrid.

    Ms Margarita ke cewa ƴan sanda suna gudanar da bincike amma abin da ya zama dole a fayyace shi ne, babu wani tashin hankali da zai sauya ƙudirin Spaniya da ƙasashen Nato da Tarayyar Turai na goyon bayan Ukraine.

    A ranar Laraba ne wata wasiƙa da aka aike wa jakadan Ukraine ta kama da wuta inda wani ma’aikaci a ofishin jakadancin ya ji rauni.

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa wataƙila an aika wasiƙar ne daga cikin ƙasar.

  3. Ba za mu ƙara kuɗin man fetur ba a yanzu - Gwamnatin Najeriya

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar ƙara kuɗin man fetur "a wannan lokaci" yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fama da dogayen layi a gidajen man.

    Wata sanarwa da hukumar kula da rarraba fetur ta NMDPA ta fitar ta ce ya zama dole su musanta jita-jitar da ake yi game da farashin man da kuma ƙarancinsa a cikin Najeriya.

    Sanarwar ta ce kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited, ya tanadi man fetur da zai isa amfanin ƙasar tsawon kwana 34.

    "Ana bai wa 'yan kasuwa da sauran jama'a shawarar su daina fargaba da kuma sayen man don karkatarwa da kuma ɓoye shi," in ji NMDPR.

    Bisa al'ada, akan fuskanci ƙarancin man fetur a duk ƙarshen shekara a Najeriya duk da cewa a baya-bayan nan ba a ga hakan ba sakamakon ƙarin kuɗin man da gwamnati ta dinga yi akai-akai.

    Sai dai wannan karon an fara ƙarancin fetur ɗin tun daga tsakiyar 2022, inda wasu gidajen mai ke sayar da lita ɗaya kan N200 zuwa N250 maimakon N185 farashin gwamnati.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. An bai wa Majalisar Kano shawarar hukunci mai tsanani wajen kafa dokar haƙƙin yara,

    Majalisar Dokokin Kano

    A yau Alhamis Majalisar Dokokin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta yi zama don sauraron ra’ayoyin jama’a a kan yunkurin kafa dokar kiyaye haƙƙin ƙananan yara.

    Mahukunta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiyaye hakkokin yara sun ba da shawarar a yi tanadin hukunci mai tsanani ga masu tauye haƙƙin yaran, ciki har da ɗaurin shekara bakwai da tara mai yawa ga masu cin zarafin su.

    Majalisar Kanon ta bayyana cewa suna yunkurin kafa dokar ne saboda a hukunta masu kuntata musu, kuma wannan ne ya sa aka yi tanadin hukunce-hukunce daban-daban.

    Mataimakin Kakakin Majalisa Kabiru Hassan Dashi - kuma shugaban kwamitin harkokin mata da walwalar jama’a - ya faɗa wa BBC Hausa cewa dokar za ta ba da dama agina wa marayu gidaje da ɗaukar nauyin karatunsu.

    Ya ƙara da cewa wannan ne zama na ƙarshe da suka yi kafin amincewa da dokar a Majalisa.

  5. 'Yan tawayen Tigray za su mika makamansu

    TPLF

    Asalin hoton, Getty Images

    Jakadan Habasha (Ethiophia) a Kenya ya ce ƙungiyar 'yan tawayen yankin Tigray Tigray People's Liberation Front (TPLF) za ta miƙa manyan makanta a ranar Asabar a shirin tsagaita wuta tsakaninsu da gwamnatin tarayyar ƙasar.

    Bacha Debele ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon bidiyo da aka wallafa a dandalin Youtube.

    "Game da sarandar manyan makamai, ya kamata su [TPLF] miƙa su tun a ranar 17 ga watan Nuwamba amma ba a yi hakan ba, yanzu an amince su mia su ranar 3 ga watan Disamba," in ji shi.

    Mista Bacha kwamandoji "na ganawa a kullum" don tattauna sarandar makaman sannan kuma ana tattara mayaƙan TPLF a wasu yankuna na musamman.

    "Bayanan da na samu a yau sun nuna cewa an fara shirin tattarawa [mayaƙan TPLF] a sansanoni na musamman. Suna ci gaba da aiwatar da shirin sarandar," a cewarsa.

    A farkon watan nan gwamnati da 'yan TPLF suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Afirka ta Kudu don kawo ƙarshen yaƙin da suka fara gwabzawa a yankin Tigray a 2020.

  6. Qatar 2022: Moroko ta tsallake, an fitar da Belgium

    Moroko

    Moroko ta kai zagayen gaba a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar, yayin da a ka cire Belgium bayan da ta kasa samun maki uku a hannun Croatia.

    Nasarar da Moroko ta yi 2-1 a wasanta da Kanada na nufin ta zama zakara a Rukunin F da maki bakwai, yayin da Croatia ke bin ta da maki biyar.

    Kasar ta Arewacin Afrika ta ci kwallayenta ne ta hannun Hakim Ziyech da En-Nesyri tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

    Kuma ta zama kasa ta biyu daga nahiyar Afrika bayan Senegal da ta kai zagayen kwaf ɗaya na gasar ta Qatar 2022.

    Belgium kuwa wadda ita ce ta biyu a jadawalin Fifa na ƙasashe mafiya ƙwarewa kuma ta uku a Kofin Duniya na 2018, ta fita daga gasar da maki 4.

  7. Sojojin Isra'ila sun harbe shugabannin gwagwarmayar Falasɗinawa biyu

    Israila

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra’ila sun harbe jagororin ƴan tawayen Palasɗinu biyu a wani samame da suka kai yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Lamarin ya janyo musayar wuta.

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta shiga garin Wadi Burqin kusa da Jenin domin kama wasu Palasɗinawa uku da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

    Majiyoyi sun ce sojojin sun je samamen ne cikin wasu motoci kirar 'jeep' sama da tamanin.

    A watannin baya-bayan nan, Isra’ila tana kai samame kusan kowace rana a yankin Gaɓar Yamma da Kogin na Jordan.

  8. Jiragen sama 500 ke shige da fice a Qatar a kullum

    Qatar

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun da aka soma gasar cin kofin duniya a Qatar a cikin watan Nuwamba, dubban jama'a daga kasashen duniya da dama ke tururuwa zuwa kasar domin kallon wasannin kwallo.

    Bayanai sun ce a kullum jiragen sama 500 ke tashi da sauka a Doha babban birnin kasar.

    Daga ciki kusan jirage 120 ke tasowa daga Dubai mai makwabtaka da Qatar din.

    Ana fama da karancin dakunan otal a Qatar abin da ya sa wasu 'yan kallo ke sauka a Dubai ko kuma wasu kasashen larabawa inda daga nan suke kama hanya zuwa Qatar.

    Masu rajin kare muhalli sun ce yawan zirga-zirgar jiragen na tasiri ga muhalli.

  9. Wani dan majalisar dokokin Senegal ya doki takwararsa a zauren majalisa

    Massata Samb

    Asalin hoton, Senegal National Assembly

    An samu yamutsi a zauren majalisar dokokin Senegal ranar Alhamis bayan wani dan majalisa ya doki takwararsa a ka a yayin da ake nuna zaman majalisar kai-tsaye a talabijin.

    An fuskanci tsaiko a zaman majalisar lokacin da ake gabatar da kasafin kudi, bayan dan majalisar dokoki daga jam'iyyar hamayya Massata Samb ya bar dandamali inda ya tafi wurin 'yar majalisa Amy Ndiaye Gniby ta jam'iyyar Benno Bokk Yakaar mai mulki sannan ya doke ta a ka.

    Da take mayar da martani, Ms Gniby ta jefi Mr Samb da kujera, kafin wasu 'yan majalisar su sanya baki, amma rikicin bai tsaya ba domin kuwa sun yi ta nuashin juna, lamarin da ya sa aka soke zaman majalisar.

    Kafofin watsa labaran kasar sun rawaito cewa Mr Samb ya tuna wa zauren majalisar wasu kamalai da Ms Gniby ta yi tun da farko wadanda ya ce na "rashin da'a ne".

    Daga nan ne Ms Gniby ta mayar da martani daga kujerarta inda ta ce ba ta "damu" ba.

    Nan take Mr Samb ya daina magana ya ruga a guje inda take.

  10. 'An kashe masu iƙirarin jihadi 30 a Mozambique'

    Rundunar sojin kasashen da ke kungiyar ci gaban Kudancin Afirka, wadda aka fi sani da Samim, wadda aka aika yankin Cabo Delgado da ke arewacin Mozambique don magance hare-haren ta'addanci, ta ce ta kashe mayakan da ke ikirarin jihadi guda 30 a harin da ta kai ranar Talata.

    Ta ce ta kwato makamai da dama da mayakan suke amfani da su.

    Kazalika rundunar ta sanar cewa sojojinta biyu, daya dan kasar Botswana yayin da dayan dan kasar Tanzania, sun rasa rayukansu a harin da aka kai musu a kauyen Nkonga,da ke gundumar Nangade ta arewacin Cabo Delgado.

    Har yanzu Nangade ne yankin da mayakan da ke ikirarin jihadi suka fi karfi, inda suke kai hare-hare kan mazauna kauyuka da gonakinsu da kuma cibiyoyin soji.

    A kwanakin baya an yi kwanton-bauna ga dakarun Tanzani da ke aiki a cikin rundunar sojin kasashen da ke kungiyar ci gaban Kudancin Afirka, inda aka jikkata sojoji biyar.

  11. Wasu ma'aikatan CBN da NPA sun fi Buhari albashi - RMAFC

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tarawa da rarraba kuɗin haraji ta Najeriya - RMAFC ta ce wasu ma'aikatan gwamnati suna karɓar albashin da ya zarta na shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.

    Shugaban hukumar Mohammed Shehu ya ce "albashin shugaban ƙasa bai kai naira miliyan 1,300,000 ba a wata...kuma ana saka alawus-alawus ɗin shugaban ƙasar ne a cikin albashin nasa."

    Ya ƙara da cewa "a yanzu akwai ma'aikata a ɓangaren gwamnati da masu zaman kansu waɗanda suke karɓar irin wannan albashi nunki biyu, ko uku, ko huɗu."

    A wani shiri na gidan talabijin na Channels, Shehu ya ce akwai masu karɓar irin wannan albashi a ma'aikatu kamar Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya (NIMASA), da Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC), da Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa (NPA), da kuma Babban bankin Najeriya (CBN) da ma wasu da dama.

    Shugaban hukumar ta RMAFC ya kuma ce wasu jami'an gwamnati suna karɓar kuɗin sallama har naira miliyan 500 yayin da shi kuwa shugaban ƙasa yake samun miliyan 10 a ƙarshen wa'adin mulkinsa.

    Mohammed Shehu ya ce akwai tsarin biyan albashi guda 17 a ma'aikatu daban-daban a Najeriya.

    Daga nan sai ya nuna buƙatar daidaita tsarin yadda ake biyan albashin ma'aikata, inda ya ce bai kamata a samu wani ma'aikaci da ya fi shugaban ƙasa albashi ba.

  12. Tsohon shugaban jami’ar Gusau zai sha ɗaurin shekara 35

    VC Gusau

    Asalin hoton, EFCC

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta yanke wa tsohon shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba hukuncin ɗauri na shekara 35.

    Mai shari’a Maryam Hassan Aliyu, wadda ta yanke hukuncin ta ce an samu farfesa Garba ne da laifuka biyar da suka jiɓanci amfani da ƙarya wajen karɓar kuɗi da kuma zamba.

    Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gaban kotu a ranar 12 ga watan Oktoba tana zargin sa da tatsar kuɗi daga wani mutum bisa alƙawarin ba shi kwangilar katange jami’ar, wadda kuɗinta ya kai naira biliyan uku.

    A lokacin da ta yanke hukunci, mai shari’ar ta ce ta gamsu da bayanan da EFCC ta gabatar, sannan ta yanke masa hukuncin jimillar shekaru 35 a gidan maza.

  13. Aisha Buhari: Dole ne a saki Aminu - Amnesty

    ..

    Asalin hoton, OTHER

    Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su saki matashin nan da ake zargi da cin mutuncin uwargidar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari tare da yin watsi da duk zarge-zargen da ake yi masa.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an azabtar da matashin bayan kama shi.

    Ta ce "babban abin kunya ne a ce hukumomin Najeriya sun kama tare da azabtar da Aminu Adamu kawai saboda ya wallafa bayanai a shafin tuwita wanda ya shafi uwargidar shugaban ƙasar."

    Bayanin ya ƙara da cewa wannan lamari karan-tsaye ne ga ƴancin bil'adama.

    Haka nan hukumar ta ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su mayar da hankali a kai shi ne tsarewar da aka yi wa matashin ba bisa ƙa'ida ba da kuma azabtar da shi da aka yi.

    Bayanai dai sun tabbatar da cewa kotu ta tura matashin mai suna Aminu gidan gyara hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin sa da cin mutuncin mai-ɗakin shugaban ƙasa, A'isha Buhari a shafinsa na tuwita.

  14. Akwai isasshen man fetur a rumbu – NNPC

    Mele Kyari

    Asalin hoton, TWITTER

    Kamfanin man fetur na Najeriya ya ce yana da man fetur wanda yawansa ya kai lita biliyan biyu maƙare a rumbuna.

    A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce yawan man fetur ɗin zai wadaci Najeriya na tsawon kwana talatin.

    NNPC ya ce ya ajiye jiragen ruwa da tankokin safarar mai a cibiyoyi daban-daban, kuma yana sanya ido sosai kan yadda ake maƙare su da man fetur ɗin domin kai wa jihohi daban-daban ta yadda za a magance ƙarancin mai.

    Sanarwar ta ce ƙarancin mai da ake fuskanta a Legas ya samo asali ne daga aikin gyaran hanyar Apapa, yayin hakan kuma ya shafi man fetur ɗin da ake samar wa Abuja.

    Sai dai kamfanin ya ce yanzu ya ƙara azama wajen loda man fetur ɗin a motocin dakon mai zuwa sassan ƙasar.

  15. Najeriya ba ta talauce ba – Ministar kuɗi

    Zainab Ahmed

    Asalin hoton, TWITTER/ ZAINAB AHMED

    Ministar kasafin kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta ce Najeriya ba ta talauce ba.

    Ta bayyana hakan ne a wurin taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.

    Hajiya Zainab ta ce har gobe gwamnatin ƙasar na ci gaba da raba kuɗaɗe daga asusun tarawa da rarraba kuɗaɗe na gwamnati.

    Ta ce daga shekarar 2015 zuwa yau gwamnatin tarayya ta bai wa na jihohi kuɗi naira tiriliyan 5.04.

    Ta ƙara da cewa har yanzu Najeriyar ba ta gaza wajen biyan basussukan da ake bin ta ba, a ciki da wajen ƙasar.

    Ministar ta kuma ce yawan man fetur da ƙasar ke haƙowa na ƙara yawa, inda ta ce a watan Oktoba yawan man ya kai ganga miliyan 1.4 a kowace rana.

  16. Zulum ya bayar da umurnin kama ƴan bangan siyasa

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/@bornogov

    Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana takaicinsa kan yawan tashin hakula da ake samu tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihar.

    Wata sanarwa ta hannun mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labaru, Isa Gusau, ta ce an fi samun rikicin ne tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma na PDP mai hamayya.

    Gwamnan ya buƙaci kwamishinan ƴan sanda na jihar ya gudanar da bincike kan rikice-rikice da aka samu na baya-bayan nan tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

    Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki, da ƴan takara su tabbatar sun kauce wa rigingimu a lokutan yaƙin neman zaɓe domin kauce wa shiga hannun hukuma.

  17. Kotu ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa na Najeriya

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/NIGERIAN ARMY

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Minna, jihar Neja, ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya bisa laifin rashin grimama kotu.

    Mai shari’a Halima Abdulmalik, wadda ta yanke hukuncin ta kuma bukaci da a kulle Janar Yahaya a gidan gyara hali na Minna saboda saba ma wani umurnin kotu na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022.

    Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata babbar kotun da ke zamn ta a Abuja ta yanke wa sifeta-janar na ’yan sandan Najeriya hukuncin dauri na wata uku saboda kin martaba hukuncin kotu.

  18. Mutanen Kenya na rububin cin bashi daga gwamnati

    ...

    Asalin hoton, OTHER

    Sama da mutum miliyan daya ne suka yi rajista da shirin gwamnati na bai wa matasan kasar da kananan yan kasuwa bashi, kwana daya bayan kaddamar da shi.

    A jiya Laraba ne shugaban kasar William Ruto ya kaddamar da shirin, wanda ya zuwa yanzu aka bai wa wadanda za su ci gajiya bashin kudin kasar shilling miliyan 400 (kimanin dala 3.3).

    Kafafen yada labarun kasar sun ambato ministan tallafin kudi na kasar na cewa mutum 600 ne suka rika nuna sha'awar neman bashin a cikin kowace dakika daya a farkon kaddamar da shirin.

    Masu son karbar bashin za su iya samu ta hanyar danna wasu lambobin daga wayoyinsu na hannu.

    Ana bayar da bashin da ya kama daga dalar Amurka hudu zuwa dala 408 ga daidaikun mutane.

    Bashin, daya ne daga cikin manyan alkawurran da shugaban kasar ya yi lokacin yakin neman zabe.

    Ana sa ran shirin zai tallafa wa 'yan kasar miliyan takwas.

  19. Kasashe 10 da suka kai zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya

    'Yan Ingila na murnar kai wa mataki na gaba

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Juma'a za a kammala buga wasannin zagayen farko na gasar cin kofin duniya da ake fafatawa a Qatar.

    Kawo yanzu wasu kasashen sun tsallake zuwa zagaye na biyu wasu kuma an fitar da su.

    A yayin da akwai wasu karin kasashen da suma za su iya kaiwa mataki na gaba.

    Rukunin A

    A wannan rukunin kasashen Netherlands da Senegal su ne za su buga wasanni a zagaye na biyu.

    A yayin da mai masaukin baki Qatar da Ecuador kuma aka fitar da su.

    Rukunin B

    Ingila da Amurka su ne suka haye zuwa mataki na gaba a yayin da Iran da Wales kuma aka fitar da su.

    Rukunin C

    Argentina da Poland su ne kasashen da suka yi nasarar tsallakewa zuwa mataki na gaba a gasar.

    A yayin da Saudi Arabiya da kuma Mexico suka fita daga cikin gasar.

    Rukunin D

    Faransa da Australiya su ne kasashe biyu da suka fito daga wannan rukunin duk da cewa Tunisia ta doke Faransar a wasansu na karshe.

    Denmark da Tunisia su ne suka gamu da rashin sa'a a wannan rukunin.

    Rukunin E

    Spaniya da Costa Rica da Japan da kuma Jamus su ne a wannan rukunin. Amma kawo yanzu babu wacce ta tsallake zuwa zagaye na biyu. Sai a wasanninsu na yau za a sani.

    Spaniya za ta kara da Japan sai kuma Jamus ta hadu da Costa Rica.

    Rukunin F

    Croatia da Belgium da Canada da Morocco su ne a wannan rukunin.

    Canada ta riga ta san makomarta saboda an doke ta a wasanni biyu na farko saboda haka ba za ta kai zagaye na gaba ba.

    Rukunin G

    Brazil ta tsallake zuwa zagaye na biyu.

    Sai dai a ranar Juma'a za a san tsakanin Switzerland da Kamaru da Serbiya kasar da za ta kai mataki na gaba.

    Rukunin H

    Portugal ta kai matakin zagaye na biyu a gasar bayan ta samu nasara a wasanni biyu a jere.

    Ghana da Koriya ta Kudu da Uruguay su ne sauran kasashen da ke a rukunin kuma a cikinsu kasa daya ce za ta iya kai wa mataki na gaba.

    Kasashe 16 ne za su kai mataki na biyu a gasar cin kofin duniya

    'Yan Mexico sun sha kuka

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Wata uwa ta fille kan danta dan wata 11

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama wata mai suna Blessing bisa zargin ta da kashe danta dan wata 11 a kauyen Ugep, da ke karamar hukumar Yakurr na jihar Cross River.

    Jaridar PUNCH ta ce jami'an 'yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru ne daidai lokacin da matasa ke kokarin lakada wa matar duka.

    Lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce yanzu haka matar tana hannun hukuma.

    Ugbo ya kara da cewa "ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ta yanka yaron, amma labarin da muka samu shi ne tana da tabin hankali."