Amurka ta sa wa yariman Saudiyya rigar kariya kan kisan Khashoggi

Wannan shafi yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Zanga-zangar Iran na ƙara bazuwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar matasa Iraniyaniya da aka ce jami'an tsaro sun kashe ta haddasa sabuwar zanga-zanga a Iran.

    Masu zanga-zangar da ke yayata kalamai na kisa ga jagoran kasar Ali Khamenei sun hada gangami a garin Izeh da ke kudu maso yammacin kasar a lokacin jana'izar wani yaro dan shekara tara.

    Danginsa sun ce dan sanda ne ya harbe shi, - zargin da jami'ai suka karyata, suna masu dora laifin kisan yaron kan wadanda suka kira yan ta'adda.

    Zanga-zangar ta bazu zuwa Tabriz da Mahabad da Zahedan

  2. Saudiyya ta bai wa Ghana gudumawar Dabino

    Shugaba Nana Akufo-Addo

    Asalin hoton, NANA AKUFO-ADDO/FACEBOOK

    Ƙasar Ghana ta karɓi gudumawar dabino tan 50 daga gwamnatin Saudi Arabiya.

    Lokacin da ya karɓi gudumawar dabinon a madadin gwamnatin Ghana, babban darakta na ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Ramses Cleland ya ce lamarin ya ƙara tabbatar da kyakkyawar dangantaka da haɗin kan da ke tsakanin ƙasashen biyu.

    Ya ce Saudiyya ta taka rawa sosai wajen taimaka wa Ghana a ɓangaren ilimi, da lafiya, da kuma makamashi.

  3. Amurka ta yi watsi da gwajin makamin Koriya ta Arewa

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka ta yi watsi wa watsi da barazanar Koriya ta Arewa bayan gwajin makami mai linzami na baya-bayan nan.

    Japan ta ce makamin yana da karfin da zai iya isa har Amurka.

    Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris da wasu manyan jami'ai daga kasashen Koriya ta Kudu da Japan da sauran aminnan kasar, wadanda ke halartar taron APEC, sun yi Allah wadai da gawajin makamin Pyongyang da ta yi cikin kwana biyu .

    Sai dai Amurka ta ce ba ta dauki gwajin ba a matsiyin wata babbar barazana.

  4. Ƙarancin wutar lantarki na ƙara tsanani a Afirka ta kudu

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Kamfanin samar da wutar lantarki na Afirka ta kudu, Eskom, ya gargaɗi al'ummar ƙasar da su shirya wa zama cikin duhu saboda shirin da yake yi na tsananta rarraba ƙarfin wutar tsakanin mabuƙata.

    Ƙasar na fama da ƙarancin wutar lantarki na tsawon shekaru saboda rarraba wutar da ake yi tsakanin wurare daban-daban domin tsimin wutar da ake samarwa.

    ESkom, wanda ya bayar da sanarwar a yau Juma'a, ya ce zai koma mataki na huɗu na rarraba wutar lantarki.

    Hakan na nufin za a ɗauke wutar lantarki kimanin sau 12 a cikin kwana huɗu. Kuma hakan zai ci gaba da faruwa har sai yadda hali ya yi.

    Akwai matakan rarraba wutar lantarki takwas da kamfanoni ke amfani da su.

    A mataki na twakwas, mutane za su iya kwashe awa 12 ba tare da wutar lantarki ba a rana guda.

  5. Kotu ta wanke Babachir Lawal daga zargin badaƙalar cire ciyawa

    David Babachir Lawal

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke tsohon sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Babachir Lawal da wasu mutum biyar daga zargin wata badaƙala ta kuɗi naira miliyan 544.

    Hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta Najeriya, EFCC ce ta gurfanar da mutanen, tana zargin su da almundahana kan wata kwangilar cire ciyawa, wadda kuɗinta ya kai naira miliyan 544.

    Mai sharia’a Charles Agbaza ya ce babu wani abu da zai nuna cewa Babachir yana da laifi a cikin bayanan da shaidu 11 da EFCC ta gabatar suka bayar.

    Haka nan kotun ta ce EFCC ta kasa tabbatar da cewa Babachir jami’i ne a shirin ofishin shugaban ƙasa na tallafa wa arewa maso gabas, wanda ya bayar da kwangilar aikin.

    A kan haka ne kotun ta ce ta wanke dukkanin mutane 10 da ake tuhuma a ƙarar.

  6. An halaka mutum 15 a Iraq

    Kamanin mutum 15 ne aka halaka, wasu talatin kuma suka jikkata a wata fashewa da ta faru a birnin Sulaimaniya da ke Arewacin Iraki.

    Wani jami’i ya ce mutane 13, wasu daga cikinsu yara, sun maƙale cikin ɓuraguzon ginin.

    Jami’an tsaro sun kashe wutar da ta tashi bayan afkuwar fashewar.

    Ƴan sanda kuma sun ce lamarin ya shafi gidaje da dama.

  7. Shugaba Buhari ya amince da yi wa ma'aikatan shari'a ƙarin albashi

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin ƙara wa ma’aikatan shari’a na ƙasar albashi.

    Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yau Juma’a a jihar Rivers, lokacin ƙaddamar da sabon ginin makarantar horas da lauyoyi da ke jihar.

    Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙasar, ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙarin inganta albashin ma’aikatan shari’ar ne domin ƙarfafa ɓangaren da kuma tabbatar da ƴancinsa.

    Ya ce yanzu haka shugaba Buhari ya umurci shugaban hukumar tarawa da raba kuɗaɗen haraji na ƙasar, da ministan sharia’a su ɗauki matakan ganin an fara aiwatar da ƙarin albashin.

  8. Wasu ƙasashen Afirka na taron nemo hanyoyin hana rikici yaɗuwa zuwa cikinsu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Jami’ai daga wasu ƙasashen yammacin Afirka na gudanar da taro a Accra, babban birnin ƙasar Ghana domin tattauna yadda za su kare yaɗuwar rikicin masu iƙirarin jihadi zuwa cikin ƙasashensu daga yankin Sahel.

    Ministan tsaron Ghana Albert Kan-Dapaah, ya ce ana buƙatar gudanar da taron ganin yadda ayyukan ‘ta’addanci’ ke yaɗuwa zuwa ƙasashe daban-daban.

    Ana gudanar da tattaunawar ne yayin da ƙasashe da dama suka ɗauki matakin fita daga shirin ƙasashen duniya na samar da zaman lafiya a Mali, wadda ke fama da rikicin masu tayar da ƙayar baya.

    Ƙasashen da ke halartar taron, wato Ghana, da Togo, da Benin, da Ivory Coast na ci fuskantar barazanar hare-hare daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi waɗanda suke dannowa kudu daga ƙasashen Sahel.

  9. Amurka ta sanya wa yariman Saudiyya rigar kariya kan shari’ar kisan Khashoggi

    Mohammed bin Salman

    Asalin hoton, EPA

    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da wata kotun ƙasar cewa yariman Saudiyya Mohammed bin Salman yana da rigar kariya saboda sabon matsayinsa na firaiministan Saudi Arabia.

    A saboda haka Amurkar ta ce ba za a iya hukunta shi a sharia’ar da budurwar ɗan jaridar nan da aka kashe Jamal Khashoggi ta shigar game da kisan saurayin nata ba.

    Khashoggi, shahararren mai sukar gidan sarautar Saudiyya, an kashe shi ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke ƙasar Turkiyya a cikin watan Oktoba na shekarar 2018.

    Jami’an tattara bayanan tsaron sirri na Amurka sun ce sun yi amannar yarima bin Salman ne ya bayar da izinin kisan.

    Budurwar Kashoggi ta ce wannan matsaya da hukumomin Amurka suka ɗauka tamkar bi-ta da ƙulli ne a kan mamacin.

    Matar, mai suna Hatiz Cengiz, tare da wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Arab World Now sun shigar da ƙara ne suna neman diyya daga yariman na Saudiyya bisa kisan Jamal Khashoggi.

  10. Hukumar Alhazai na gab da soma shirin aikin Hajjin 2023 a Najeriya

    NAHCON

    Asalin hoton, NAHCON

    Shugaban hukumar Alhazai ta kasa a Najeriya, Zikrullah Kunle Hassan, ya ce a cikin watan Disamba za su fitar da adadin mutanen da za su je aikin hajjin baɗi a faɗin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a Abuja a wani taro kan shirye-shiren hajjin baɗi.

    Ya ce ba kamar bara ba da aka fuskancin jinkiri, a wannan lokaci hukumomin Saudiyya za su tuntubesu a kan lokacin domin ba su wadatacen lokacin shirye-shirye.

    Ya kuma bayyana yadda matsalar bisa a wani lokaci ke zama kalubale ga shirye-shiryensu.

  11. MDD ta gargaɗi Najeriya kan bai wa ma'aikatanta cikakkiyar kariyar tsaro

    Antonio

    Asalin hoton, UN

    Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kare ma'aikanta daga barazanar hare-hare a faɗin kasar.

    Wannan na zuwa ne bayan wani sojan Najeriya ya bude wuta a wani sansanin sojoji da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar.

    Sojan ya kashe ɗan uwansa soja ɗaya da kuma wani ma'aikacin agaji, sanna ya raunata wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.

    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tana mai cewa sojojinta da ke wurin sun yi nasarar kashe sojan da ya yi ta'asar.

    Sanarwar ta ce matukin helikwaftan ba ya cikin wani garari, akwai alamun samun sauki a gareshi.

  12. Gasar cin kofin duniya na 2022: An haramta sayar da barasa a filin kwallo a Qatar

    FIFA

    Asalin hoton, FIFA

    An haramta sayar da barasa a filayen ƙwallon da Qatar za ta karɓi baƙuncin wasannin cin kofin duniya.

    Za ake rinƙa shan barasar ne a wasu keɓaɓɓun wurare da aka ware, domin taƙaita shan barasar a ƙasar da ke bin dokokin Musulunci.

    A ranar Lahadi za a fara gasar inda Qatar za ta buga wasan farko da Ecuador.

    Qatar dai na cigaba da ɗaukar matakai da bijiro da tsare-tsaren faranta ran manyan baƙinta gabanni fara wasanni.

  13. Matata da ƴaƴana Kiristoci ne, in ji Tinubu

    BOA

    Asalin hoton, BOA

    Ɗan takarar shugabancin ƙasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa shugabannin ƙungiyar Kiristoci ta kasa CAN cewa ba zai sanya batun addini a mulkinsa ba, muddin ya yi nasara a zaɓen 2023.

    Tinubu ya ce shi Musulmi ne sai dai matarsa da 'ya'yansa duk Kiristoci ne.

    Tsohon gwamnan na Legas ya yi waɗannan kalamai ne a Abuja a kokarin nuna wa ƙungiyar CAN cewa yana tare da su kuma bambanci addini ba zai yi tasiri a shugabancinsa ba.

    Batun zaɓin da Tinubu ya yi na Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ya ja hankali da haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan kasar musamman Kiristoci da ke ganin an yi masu rashin adalci.

    Sai dai Tinubu ya ce shi burinsa shi ne kafa gwamnati mai nagarta ba wai bisa addini ko kabilanci ko wani abin da mutum ya yarda da shi ba.

    Dan takarar ya ce shi mutum ne da ke neman kawo sauyi a Najeriya, shi yasa yake neman haɗin-kan kowa ba tare da nuna banbanci na addini ba, wajen kai kasar ga nasara.

    Tinubu ya tausasa zuciyar shugabanni CAN tare da masu alƙawarin cewa za su more a mulkinsa.

  14. Rundunar 'yan sanda Najeriya ta gargaɗi gwamnonin da take zargi na daukar nauyin ɓata-gari

    NPA

    Asalin hoton, NPA

    Rundunar 'yan sanda Najeriya ta gargaɗi wasu gwamoni da take zargi na daukar nauyin 'yandaba domin ingiza rikici.

    Babban sufeta janar na 'yan sanda kasar, Usman Baba, ya ce suna samun rahotanni sosai daga jihohi kan yadda wasu gwamnoni ke karfafa dabanci tsakanin matasa da kai wa 'yan hamayya hari.

    Usman Baba, ya ce za su dau mataki mai tsauri domin daƙile duk wani yunkuri yada kiyayya ko haddasa rikici bisa tanadin dokokin kasar.

    Jami'in ya kuma umarci 'yan takara musamman masu neman kujerar shugaban kasa su mutunta yarjejeniyar da suka sanyawa hannu na tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.

  15. Ana zargin Koriya Ta Arewa da harba wani katafaren makami mai linzami

    Hukumomin sojin Koriya ta Kudu sun ce makwabciyarsu Koriya ta Arewa ta harba abin da suke zargi katafaren makami mai linzami ne da ke cin dogon zango daga nahiya zuwa wata nahiyar.

    Rahotanni na cewa a jiya ministar waje ta Koriya ta Arewar, ta soki taron da aka yi tsakanin Amurka da kawayenta na yankin Koriya ta Kudu da Japan.

    A wannan lokacin kasashen uku suka yi alkawarin hada kai domin yakar duk wata barzana daga Koriya ta Arewar.

    Ministar ta yi barazanar cewa za su mayar da kakkausan martani.

    Wannan shi ne na biyu a cikin kwana biyu a jerin gwajin da take yi wanda zai iya tayar da zaune tsaye.

  16. Gwamnonin da EFCC ke bincike kan rashawa a Najeriya sun ƙaru, in ji Abdulrasheed Bawa

    EFCC

    Asalin hoton, EFCC

    Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya ce bijiro da batun sauya fasalin kuɗi a Najeriya na taimaka musu wajen yaƙi da rashawa, kuma hanya ce ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

    Bawa ya kuma shaida cewa adadin gwamonin da ake bincike kan zargi haramta kuɗaɗen haramu sun karu daga mutum uku da suka bayyana a baya.

    Sai dai kuma Bawa yaƙi bayyana su waye gwamnonin da kuma yawansu.

    Ya kuma shaida cewa hukumar ICPC ta kuma kwato naira biliyan 117 tsakanin Janairu zuwa Agustan 2022.

    Sannan ya kuma ce akwai kuɗaɗen ƙasar da CBN har yanzu ba ta san inda suka shiga ba, don haka wannan wata dama ce ta kwato kudaden kasar da kuma karya wadanda suka wawushe dukiyar kasar.

  17. Gwamnatin Najeriya ta tsaurara matakan tsaro a ofisohin INEC da ke faɗin ƙasar

    INEC

    Asalin hoton, INEC

    Gwamnatin Najeriya ta tura jami'an tsaro na DSS da sojoji da jami'an hukumar kashe gobara ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC domin tsaurara tsaro gabannin zaɓen 2023.

    Ta kuma umarci jami'an su inganta tattara bayanan sirri domin daƙile duk wani yunƙuri na rikici ko ɓata gari a makonni masu zuwa gaba.

    Babban Sufeta Janar na 'yan sanda kasar, Usman Baba ne ya shaida hakan bayan tattaunawa da shugabanni jam'iyyun siyasa a hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja.

    Rundunar ta ce a cikin mako shida, an samu rigingimu aƙalla 52 a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da Ogun da Osun.

    Akwai kuma harin da aka kai wa magoya-baya a gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi irinsu Borno da Kaduna da Zamfara da dai sauransu.

    Rundunar ta ce tana tsare da wasu da ake zargi na da hannu a waɗannan rikice-rikice, kuma za a gurfanar da su domin fuskantar hukunci.

  18. 'Yan Lebanon na ficewa daga kasar domin shiga ƙungiyar IS

    Shugabannin al'umma a Lebanon sun ce kusan matasa maza dari daya ne suka fice daga kasar domin shiga kungiyar IS ta masu ikirarin jihadi a bara.

    Ana ganin sun sulale ne zuwa kasar Iraqi.

    An ce sun shiga kungiyar ne ba don an yi musu wa'azi na tsattsaurar akidar kungiyar ba, sai dai kawai a matsayin wata hanya ta tsere wa matsalar tattalin arziki da kuncin rayuwa da ake fama da su a Lebanon din.

    Sai dai kuma hukumomin Iraqi sun gargadi mazajen na Lebanon da cewa a kul suka bari IS ta yi amfani da su, za su fuskanci kamu ko ma kisa idan aka same su suna yaki a Iraqin.

    Rahotanni na cewa sojin Iraqi sun ce hare-harensu na sama sun kashe 'yan bindiga da yawa da suka je can daga Lebanon a shekarar da ta wuce.

    Tun a 2019 Lebanon take fama da matsalar tattalin arziki da ba ta taba fuskanta ba, wadda ta jefa sama da kashi tamanin cikin dari na al'ummar kasar cikin talauci.

  19. Elon Musk ya umarci ma'aikatansa su rufe ofisoshinsu

    Elon Musk

    Asalin hoton, ELONMUSK

    Kamfanin Twitter ya gaya wa ma'aikatansa cewa zai rufe dukkanin ofisoshinsa tun daga yanzu har zuwa ranar Litinin.

    Sai dai a sakon da ya aika musu bai bayyana dalilin rufewar ba.

    Ana dai ganin daruruwan ma'aikatan kamfanin da ya shiga wani hali na ajiye aikinsu da shi ko kuma suna shirin yin hakan.

    Tun bayan da ya saye shi a kan dala miliyan dubu hudu sabon mai kamfanin Elon Musk ya sallami kusan rabin gaba dayan ma'aikatansa, manya da kanana.

    Haka kuma ya bai wa sauran wadanda suke nan wa'adin su sanya hannu a yarjejeniyar aiki tukuru na karin sa'o'i ko kuma su san inda dare ya yi musu.

  20. Maraba

    Umaymah Sani Abdulmumin ke muku maraba a wannan shafi da ke kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.