Gwamnatin Tarayya ta ba da umurnin sake bude kamfanin simintin Dangote na Obajana

Wannan shafin yana kawo maku labaran da suka shafi Najeriya da makwaftanta da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Asuba ta gari

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye da muka dauki tsawon rana muna kawo muku.

    Sai kuma gobe idan mai duka ya kaimu.

    Kafin nan, Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya

  2. Yara 10 sun mutu a Yemen bayan shan maganin cutar sankarar jini

    Hukumomi a Yemen sun ce akalla yara 10 ne suka mutu bayan sun sha maganin cutar Sankarar jini.

    An gano cewa sun sha maganin bayan ya lalace. Sanarwar yan Houthi da ke iko da babban birnin Yemen wato Sana'a ta ce lamarin ya faru ne a asibitin Kuwait.

    Houthi ta ce ta barauniyar hanya aka shigo da maganin ba da saninsu ba. Daga baya a ka gano cewa maganin ya lalace.

  3. Rasha ta ce za a dauki tsawon watanni kafin sake gyara gadar Crimea da bam ya lalata

    Crimea Bridge

    Gwamnatin Rasha ta ce aikin sake gyara gadar Crimeazai dauki har zuwa nan da watan Yulin 2023.

    Hukumomi sun ce harin bam ne ya lalata wani bangare na gadar a ranar Asabar da ta gabata, inda akalla mutum uku suka mutu.

    Rasha dai ta zargi Ukraine da kai harin, sai dai, Kyiv bata ce ko ita ce ta kai harin ba zuwa yanzu.

    Gadar mai tsawon mil 12, ita ce mafi tsawo a Turai, kuma ta kasance hanya da dakarun Rasha ke samun damar shiga Ukraine, inda a yanzu manyan motocin dakon kaya basa samun damar bi ta gadar.

    Fashewar ta kuma janyo karyewar wani bangare na tsakiyar gadar da kuma lalata layin dogo.

    An dai budewa jiragen kasa hanya wadanda suke bi ta gadar domin samun damar wucewa.

  4. Ambaliya na ci gaba da daidaita Australiya

    Flood

    Akalla gidaje 500 ne ruwa ya tafi da su, sannan mutum daya kuma ya rasa ransa yayin da ambaliya ke ci gaba da daidaita Australiya.

    Ambaliya a fadin Australiya ta kashe mutane sama da ashirin a wannan shekara.

    An bukaci al'ummomi a wasu jihohi uku na Australiya da su fice daga wurarensu yayin da mamakon ruwan sama ke janyo ambaliya a yankunan.

    An yi ta samun ruwan sama mai karfin gaske a kasar a wannan shekara, inda wasu lokuta ake shafe sa'o'i 24 ana zuba ruwa.

    Ambaliyar dai ta fi shafar jihar Victoria da ta kasance jiha ta biyu mafi yawan jama'a a Australiya.

    Ambaliyar ta kuma yashe hanyoyi tare da tilasta rufe makarantu da kuma katse wutar lantarki na gidaje da kasuwanni sama da 3,000.

  5. Gwamnatin Tarayya ta ba da umurnin sake bude kamfanin simintin Dangote na Obajana

    Obajana cement

    Asalin hoton, OTHERS

    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umurnin sake bude kamfanin simintin Dangote na Obajana da ke jihar Kogi.

    Hakan ya fito yayin taron majalisar tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau a fadarsa a Abuja.

    Ministan harkokin 'yan sanda, Mohammed Dingyadi da takwaransa na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola wadanda suka kasance a taron, sun shaida wa mana labarai cewa an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Kogi da kuma kamfanin Dangote.

    Aregbesola ya bayyana cewa bangarorin biyu sun amince na sake bude kamfanin simintin na Obajana, inda aka bukaci dukkansu da su mutunta yarjejeniyar.

    Ministan ya kuma kara da cewa majalisar ta amince cewa za a warware dukkan batutuwa da suka janyo sabani tsakanin bangarorin saboda a cewarsa gwamnati na da zummar samarwa mutane aikin yi.

  6. Shugaban China ya yi wa Buhari ta'aziyyar mamatan hadarin kwale-kwale a Anambra

    XI and Buhari

    Asalin hoton, OTHERS

    Shugaban kasar China Xi Jinping, ya jajantawa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya kan hadarin kwale-kwale da ya faru a Jihar Anambra a baya-bayan nan.

    A cikin wata wasika zuwa ga shugaba Buhari daga takwaransa na China, ya ce ya kadu matuka da jin labarin kifewar kwale-kwalen a jihar Anambra da ya janyo asarar rayuka da dama.

    ''A madadin gwamnatin China da kuma al'ummarta, ina kara mika sakon ta'aziyyata zuwa 'yan uwan wadanda suka rasu a hadarin,'' in ji Xi Jinping.

    Sama da mutane 40 ne aka ruwaito cewa sun rasa ransu sakamakon kifewar kwale-kwalen da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba a garin Umunankwo na karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra.

  7. An sauke allunan da ke dauke da hotunan wasu sanannun mata a Iran

    Matan Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    An sauke allunan da ke dauke da hotunan wasu sanannun mata a Iran, kwana daya bayan matan sun bukaci hakan a Tehran.

    Daga cikinsu akwai Jarumar fina finai Fatemeh Motamed, wadda bidiyon da ta yi na bukatar a cire hotonta ya ja hankali a kafafen sada zumunta.

    Ana ci gaba da zanga zanga a Iran, wata daya bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun jami'an tsaro, kan zargin saka mayafi ba dai dai ba.

    Iran ta dogara ne da rundunar tsaro ta musamman wurin hana boren, a maimakon amfani da sojoji, don da lamarin ya fi haka muni. Wani hoton bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka kara tsaurara tsaro a sassan kasar.

  8. Ba za mu kara yin luguden wuta ba a Ukraine nan da wani lokaci - Putin

    Putin

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce babu bukatar yin luguden wuta a kan Ukraine ba nan da wani lokaci, kwanaki kalilan bayan ruwan bama-bamai a fadin kasar tun soma yakin.

    Ya ce sun samu damar kai hare-hare a duka wuraren da suka tsara kai wa, inda ya kara da cewa ba niyyarsu ba ce ta ruguza Ukraine.

    Kalaman Putin na zuwa ne yayin da dakarun Rasha ke samun koma baya, inda sojojin Ukraine kuma ke kara dannawa wata takwas tun fara mamayar.

    Da yake magana da manema labarai yayin wani taro na shugabanni a birnin Astana na Kazakhstan, Putin ya ce hare-hare na baya-bayan nan sun ruguza wurare 22 cikin 29 da suka yi niyyar kai wa a Ukraine.

  9. Makiya ne ke rura wutar zanga-zanga a Iran - Ali Khamenei

    Iran

    Asalin hoton, Mehr News Agency

    Shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce kada wani ya kuskura da kuma yin tunanin cewa za su samu nasara a kasar a daidai lokacin da masu zanga-zangar adawa da gwamnati ke shiga mako na biyar.

    Ali Khamenei ya ce Iran ba za ta girgiza ba kuma babu wanda ya isa ya rusa kasar ta musulunci.

    Iran

    Asalin hoton, IRNA

    Shi ma shugaban kasar, Ebraim Raisi, ya zargi makiya da kokarin kawo tarnaki a kasar.

    Ya godewa al'ummar Iran saboda goyon bayan gwamnati da suke yi musamman ma a wannan lokaci da kasar ke kokarin farfado da tattalin arzikinta, inda ya ce kasar na samun ci gaba cikin sauri.

  10. Yunwa ta kai wani mataki mai matukar muni a wasu yankunan Haiti in ji MDD

    Mace da ƴarta

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwa ta kai wani mataki mai matukar muni a wasu yankunan Haiti.

    Hukumar da ke samar da abinci ta majalisar ta bayyana yanayin a matsayin wanda duniya ta dade ba ta ga irinsa ba.

    Haiti na bukatar agaji daga kasashen duniya, kuma ko a farkon makon nan shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa za a aike da taimakon da ake bukata.

    Shugaban hukumar ta WFP Jean Martin Bauer ya ce a duka fadin Haiti kusan mutum miliyan biyar ke fama da tamowa, ga kuma rikicin kungiyoyin tada kayar baya, da hauhauwar farashi da amai da gudawa.

    Ya ce irin wahalar da manoma ke yi kafin kawo abinci kasuwa na ta'zzara matsalar karancin abinci a Haiti.

  11. Taliban za ta soke dokokin da ba na Musulunci ba a Afghanistan

    Taliban

    Asalin hoton, Reuters

    Taliban ta ce za a soke duk wata dokar da ba ta musulunci ba a Afghanistan .

    Taliban ta ce za a dawo tsantsar tsarin Shari'ar musulunci a ƙasar.

    Shugaban ƙungiyar Hibatullah Akhundzada ya ce sun shirya hulda da ƙasashen duniya irin yadda shari'ar musulunci ta buƙata.

    Tun bayan da Taliban ta dawo kan mulki a 2021, ƙugiyar ta ƙi amince wa ɗalibai mata komawa makarantun sakandare, batun da ya jawo Allah-wadai a faɗin duniya.

  12. Kotu ta soke zaɓen Aisha Binani

    Sanata A'isha Binani

    Asalin hoton, FACEBOOK/AISHA BINANI

    Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yola ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, wanda Sanata A'isha Binani ta lashe.

    A hukuncin da ta yanke, mai shari’a A.M Anka ya buƙaci Aisha Binani ta daina bayyana kanta a matsayin ƴar takarar gwamna a zaɓen gwamna na shekara ta 2023.

    Kotun ta ce zaɓen ya zama haramtacce saboda aringizon ƙuri’a da kuma kawo wakilai daga ƙaramar hukumar Lamurde, inda ba a gudanar da zaɓen cikin gida na jam’iyyar ba.

    Tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa (EFCC) Mallam Nuhu Ribadu ne ya shigar da ƙarar, inda ya buƙaci kotu ta soke zaɓen, wanda aka gudanar a watan Maris.

    Inda ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u, da sayen ƙuri’a da kuma bai wa daliget cin hanci.

    Yanzu haka kotun ta ce jam’iyyar All Progressive Party ba ta da ɗan takarar gwamna a jihar ta Adamawa a zaben shekara ta 2023.

  13. An sauke Ministan kuɗin Birtaniya daga muƙaminsa

    Kwasi Kwateng

    Firaministar Burtaniya Liz Truss ta sauke ministan kuɗin ƙasar Kwasi Kwarteng daga muƙaminsa, makonni bayan naɗa shi.

    Ana kallon wannan lamari a matsayin ɗaya daga cikin mataki mafi wahala da sabuwar firaministar ta ɗauka.

    Wannan na nufin Kwarteng ya zama ministan kuɗi na biyu mafi ƙanƙantar wa’adi a kan matsayin, inda ya riƙe na tsawon kwana 38.

    Korar Mr Kwateng ta ƙara tabbatar da shakkun da al’umma ke nunawa kan ƙaramin kasafin kuɗin da ministan ya gabatar.

    Kasafin ya ƙunshi shirin zabtare haraji mai yawa da kuma ƙari a kuɗin da ƙasar za ta ranto.

    Wani lamari da ya yi sanadiyyar faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, kasancewar ana faragabar shirin zai ingiza tashin farashi kaya, wanda yanzu haka yake a matsayi mafi muni cikin shekara 40.

    Dama dai babban bankin ƙasar ya yi gargaɗin cewa za a yi fama da rashin tabbas a ɓangaren kuɗi na ƙasar sanadiyyar kasafin kuɗin.

    A sanarwar da ya fitar bayan sallamar tasa, Kwateng ya ce zai ci gaba da mara wa Truss baya wajen aiwatar da manufofin gwamnatinta.

  14. ‘Yunwa za ta kashe ɗaruruwan mutane a kullum a Somalia’

    Somalia

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar bayar da agaji ta Oxfam ta ce akwai yiwuwar yunwa za ta rinƙa hallaka mutum ɗaya a cikin kowane daƙiƙa 36 a Somalia daga yanzu zuwa ƙarshen wannan shekara.

    Ƙungiyar ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar fari da ke addabar yankin.

    Yanzu haka yanki mai fadi na ƙasar Kenya, da Somalia da kuma Habasha na gab da fuskantar hari a karo na biyar a jere.

    Wannan ya sanya miliyoyin mutane na baro ƙauyuka suna komawa sansanonin da ake samarwa a kusa da birane.

    Oxfam ta ce yawan waɗanda tsananin yunwa ya tagayyara a Somalia yanzu haka ya zarta waɗanda lamarin ya shafa shekara 2011 lokacin da aka yi fama da yunwar da ta kashe mutum 250,000.

    Yakin da ake yi a Ukraine ya ƙara ta’azzara matsalar, inda farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron-zabi.

  15. Gwamnatin Kenya za ta rufe layukan waya miliyan 12.5

    William Ruto

    Gwamnati a ƙasar Kenya ta ce za ta rufe layukan waya 12.5 cikin wannan wata saboda ƙarewar wa’adin rajistar layukan.

    Miliyoyin mutane za su wayi gari a ranar Lahadi ba tare da damar kira ko amsa waya, ko turawa da karɓar saƙo, ko ma shiga shafukan intanet ta wayoyin nasu ba.

    Hukumar lura da harkokin sadarwa ta ƙasar ce za ta datse layukan, bayan da aka kwashe wata guda ana aikin tabbatar da bayanan masu layukan waya a faɗin ƙasar.

    A watan Afrilu ne hukumar ta tsawaita wa’adin rajistar layukan da wata shida.

    Sai dai ya zuwa yanzu layuka miliyan 53 ne aka tabbatar da rajistar su.

    Gwamnatin Kenya ta bijiro da batun rajistan layukan ne a ƙoƙarinta na kakkaɓe matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

  16. Gwamnatin Zamfara ta garƙame ƙananan hukumomi uku

    Bello Matawalle

    Asalin hoton, TWITTER/@BELLOMATAWALLE

    Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ɗauki matakin dakatar da kowace irin hada-hada a wasu yankunanta da ke fama da matsalar tsaro.

    A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Juma’a, ta ce ta lura da yadda ake samun taɓarɓarewar tsaro ta hanyar sace-sacen al'umma a kauyuka da kuma kan wasu hanyoyin jihar.

    A saboda haka sanarwar ta ce gwamnati ta kulle, ɗungurungum, ƙananan hukumomin Anka da Bukuyum da kuma Gummi.

    Sauran kauyukan da kullewar ta shafa su ne Ƴarkofoji, da Birnin Tudu, da Rini, da Gora Namaye, da Janbako, da Faru, da Boko da kuma Mada.

    Sanarwar ta kuma ce daga yau an rufe kasuwannin Danjibga da Bagega.

    Bugu da ƙari an dakatar da zirga-zirga kan hanyoyi kamar haka:

    - Colony zuwa Lambar Boko

    - Bakura zuwa Lambar Damri

    - Mayanchi zuwa Daki Takwas zuwa Gummi

    - Daki Takwas zuwa Zuru

    - Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke

    - Magami zuwa Dangulbi

    - Gusau zuwa Magami

    Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu ba tare da wani cikas ba.

    Ta kuma ce ta bai wa jami’an tsaro umurnin ɗaukan mummunan mataki kan duk wanda aka samu da laifin karya dokar.

    Zamfara na cikin jihohin da matsalar tsaro ta ƴanfashin daji ta fi tagayyarawa a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

  17. 'Gwamnati za ta daukaka ƙara kan Nnamdi Kanu'

    Nnamdi Kanu

    Asalin hoton, bbc

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba hukuncin da kotu ta yanke na yin watsi da ƙarar da gwamnati ta shigar kan shugaban kungiyar IPOB, mai rajin ƴantar da yankin Biafra.

    Kotu a ranar Alhamis ne ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da ake yi wa Mr Kanu, inda ta bayar da hujjar cewa yadda aka dawo da shi Najeriya ya saɓa wa doka.

    Sai dai a sanarwar da ofishin ministan shari’a na ƙasar ya fitar ta ce kotun ta yi watsi ne da ƙarar kawai, amma ba ta wanke shi daga laifukan da ake tuhumarsa ba.

    Hakan na nufin cewar da yiwuwar ba za a saki Nnamdi Kanu nan take ba, sai dai lauyoyinsa na iƙirarin cewar wajibi ne gwamnati ta saki Kanu kasancewar kotu ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi masa kafin ta ɗauki duk wani mataki na gaba.

    A ranar 29 ga watan Yuni na shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta dawo da Nnamdi Kanu Najeriya ta gurfanar da shi a gaban kotu, inda bayanai ke cewa an kama shi ne a ƙasar Kenya.

    Sannan hukumar tsaron ciki ta DSS ta samu izinin ci gaba da tsare shi a hannunta.

    Nnamdi Kanu dai shi ne jagorar ƙungiyar ƴanta yankin Biafra, wadda gwamnatin Najeriya ta haramta.

  18. Trump ya yi watsi da buƙatar majalisar dokokin Amurka

    Donald Trump

    Asalin hoton, AFP

    Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da umurnin da kwamitin majalisar dokokin ƙasar ya ba shi na cewa ya bayar da hujjoji kan batun yin kutse ga Majalisar Dokokin ƙasar da aka yi a Janairun 2021.

    Mista Trump ya ƙalubalanci kwamitin kan dalilin da ya sa bai buƙaci ya bayar da waɗannan hujjoji ba a watan da ya gabata.

    A jiya Alhamis ne kwamitin ya yi ƙuri'a inda ya amince Trump ya je ya bayar da hujjoji kan tarzomar da magoya bayansa suka tayar a majalisar.

    Shugaban kwamitin Bennie Thompson ya bayyana cewa babu shakka tsohon shugaban ƙasar ya jagoranci wani yunƙuri da aka yi na yi wa dimokraɗiyyar ƙasar hawan ƙawara domin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasar.

    A halin yanzu kwamitin zai sake duba yiwuwar tuhumar waɗanda ke da hannu da aikata laifuka watakila har da tsohon shugaban ƙasar

  19. Ana luguden wuta a birnin da ke da cibiyar nukiliya ta Ukraine

    Zaporizhzhia

    Asalin hoton, ENERGOATOM/REUTERS

    Rahotanni daga Ukraine na cewa an wayi garin ranar Juma'a ana luguden wuta a Zaporizhzhia, garin da ke kunshe da cibiyar nukiliya mafi girma a nahiyar Turai.

    Gwmannan yankin Oleksandr Starukh ya bayyana cewa Rasha ta harba wasu makamai masu linzami uku samfarin S-300.

    Ya bayyana cewa makaman sun lalata wurare amma rahotannin farko-farko da ake samu na cewa babu wanda ya ji rauni.

  20. An tsinci gawar ƴan ci-rani 15 a gaɓar ruwa

    Dakarun tabbatar da tsaro na gaɓar teku a ƙasar Tunisia sun ce sun tsinci gawa 15 waɗanda ruwa ya hakaɗo zuwa gaɓar ruwan birnin Mahdia.

    Jami’an suka ce gawarwakin sun zugwanye, wani abu da ke nuna cewar sun daɗe a cikin teku.

    Yanzu haka hukumomin na cewa suna ci gaba da ƙoƙarin tantance su, sai dai sun tabbatar da cewa mutanen sun fito ne daga ƙasashen Afirka.

    Dubban matasa daga Afirka ne kan yi yunƙurin tsallake tekun Mediterranean a ƙoƙarinsu na tsallakawa Turai.

    Ƴan ci-rani

    Asalin hoton, IFRC MENA