Zelensky ya yaba wa Yariman Saudiyya saboda shiga tsakani a yakin Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Jabir Mustapha Sambo and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu dawo domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan za ku iya ziyartar shafinmu na BBCHausa.com domin karanta sabbin labarai da muke wallafawa a kowanne lokaci.

    Haka kuma za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara a kan labaran da muke wallafawa.

    A madadin sauran abokan aiki Abdullahi BelloDiginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. CNN ta soke hira da shugaban Iran saboda an bukaci 'yar jaridar ta daura dankwali

    .

    Asalin hoton, CHRISTIANE AMANPOUR

    Bayanan hoto, Christiane Amanpour ta ce a baya babu wani shugaban Iran da ya taba bukatar ta daura dankwali kafin hira da shi a wajen kasar

    Fitacciyar 'yar jaridar nan ta CNN Christiane Amanpour ta soke wata hira da ta shirya yi da shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, bayan da aka bukaci cewa sai ta daura dankwali kafin hirar da aka shirya yi a birnin New York na kasar Amurka.

    Amanpour ta ce babu ko daya daga cikin tsoffin shugabannin Iran da ya taba bukatar ta yi hakan a duka hirarrakin da ta yi da su a wajen kasar.

    Ta kara da cewa wani hadimin shugaban kasar ya sanar da ita cewa an bukaci ta yi hakan ne sakamakon 'halin da kasar ke ciki a halin yanzu'.

    Mutuwar wata matashiya da aka tsare a hannun 'yan sandan kasar sakamakon karya dokar sanya dankwali ya janyo zazzafar zanga-zanga a kasar.

    Matashiyar mai suna Mahsa Amini mai shekara 22, ta mutu ne a ranar Juma'a, kwanaki uku bayan an tsare ta a kan rashin sanya dankwali yadda ya dace

  3. Shugaban Kenya ya nemi kasashen duniya su yafe wa Afirka tarin basussuka

    ;

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wannan ne dai karonsa na farko a taron na Mnajalisar Dinkin Duniya a matsayin shugaban kasar

    Sabon shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi kira ga kasashe masu arziki da shugabannin duniya da su saukaka wa kasashen Afirka dangane da tarin basussukan da suke binsu.

    Yayin da yake magana a zauren taron Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban ya ce dimbin bashin da ake bin kasashen na yi wa ci-gaban kasashen tarnaki.

    Ya kara da cewa a halin da ake ciki kasashen na fama da rikice-rikice da kuma matsalar sauyin yanayi.

    Mista Ruto ya ce ''Yankinmu na gabashi da kusurwar Afirka, na fama da yake-yake da kuma matsalar sauyin yanayi, abin da ke yi wa ci gaban yankin barazana''.

    Kiran nasa na zuwa ne a daidai lokacin da mafiya yawan kasashen Afirka ke kokawa dangane da yawaitar basukan da suke biya.

    A shekarar da ta gabata ma'aikatar baitul-malin kasar kenya ta ce kasar ta biya bashin dala biliyan 6.5, abin da ya zarta rabin kudin shiga da kasar samu.

  4. Dole ne a dora wa Rasha alhakin mamayar da take yi mana - Ukraine

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, ..

    Ministan harkokin wajen Ukraine ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa dole a dora wa Rasha laifin mamayar da ta ke yi wa kasarsa.

    Dmytry Kuleba ya ce Rasha ta karya wasu dokokin Majalisar Dinkin Duniya abin da zai sa babu wata kasa da za ta ji tamkar tana da kariya matukar ba a hukuntata ba.

    Tun da farko Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya yi kiran da a sake duba batun kuri'ar raba-gardamar da za a yi kan hadewar wasu yankuna da Rasha.

    Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce mambobin kwamitin sulhun na kokarin sauya abubuwan da ke faruwa a Ukraine don su dorawa Rasha laifi.

  5. An gano gawarwaki 28 kusa da gabar tekun Siriya

    Mahukunta a Siriya sun bayyana cewa an gano gawarwaki 28 tare da ceto wasu 13, a kusa da gabar tekun kasar wanda wani kwale kwale ya kwaso su daga arewacin kasar Lebanon.

    Hukumomin sun bayyana cewa kwale-kwalen nasu ya taso ne daga Lebanon ne dauke da mutane da dama daga mabambantan kasashe.

    A 'yan shekarun nan ana yawan samun 'yan ci-rani a kasar Lebanon - wadda tattalin arzikinta ke kara tabarbarewa - in da suke guduwa wasu kasashe don samun ingantacciyar rayuwa.

  6. Mutum shida sun mutu bayan kifewar kwale-kwale a Benue

    n

    Asalin hoton, others

    Bayanan hoto, .

    Rahotonni daga jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya na cewa mutum shida sun mutu, yayin da wasu takwas suka bace sakamakon kifewar wani kwale-kwale a kusa da kauyen Fada da ke karamar hukumar Guma a jihar.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito jami'ar hulda da jama'a ta rundunan 'yan sandan jihar SP. Catherine Anene, na tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00pm na ranar Talata.

    Ta kara da cewa kwale-kwalen na dauke da fasinjoji 40, wadanda aka dauko daga karamar hukumar Guma zuwa karamar hukumar Buruku domin halartar kasuwa, lokacin da kwale-kwalen ya kife a daidai kauyen Fada.

    Yunkurin hadin gwiwwa tsakanin jami'an 'yan sanda da masinta ya taimaka wajen kubutar da fasinjoji 26, wadanda aka garzaya da su asibiti.

  7. Zelensky ya yaba wa Yariman Saudiyya saboda shiga tsakani a yakin Rasha

    b

    Asalin hoton, Saudi gazzet

    Bayanan hoto, Shugaban Ukraine tare da Yariman Saudiyya

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yaba wa Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman, saboda kokarin da ya yi na shiga tsakani wajen sakin wasu fursunoninta daga Rasha, tare da taimakawa wajen mayar da su kasar.

    Kafar yada labaran Saudiyya ta Saudi Press Agency ta ruwaito cewa Yarima Mohammed bin Salman ya shaida wa Zelensky ta waya cewa kasar Saudiyya a shirye take wajen shiga tsakani domin sasanta kasashen biyu game da rikicin da ke wakana yanzu haka.

    Yarima Mohammed bin Salman ya jaddada aniyar kasarsa na ci gaba da taimaka wa wadanda yakin ya daidaita.

  8. Gwamnatin mulkin sojin Guinea ta zargi shugaban ECOWAS da yin ‘karya’

    b

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, A 2021 sojoji suka kwace mulki daga hannun Alpha Condé

    Shugaban Gwamnatin mulkin soji a Guinea ya zargi shugaban Ecowas da ‘karya’ saboda kiran kakaba wa kasar takunkumi muddin sojojin kasar suka tsawaita lokacin mika Mulki zuwa shekara uku.

    Wani babban jami’in sojin kasar Colonel Amara Camara, ya shaida wa kamfanin dillancin labari na AFP ranar Alhamis cewa ‘’tsagwaron karya da tsangwamar kasar’ na neman rage wa shugaban Ecowas martaba’’

    A ranar Laraba ne dai shugaban na Ecowas Umaro Sissoco Embaló yace Ecowas ba za ta lamunci kudurin sojojin kasar ba, na ci gaba da Mulki har tsawon shekara uku kafin mika shi ga fara hula.

    A yau Alhamis ne dai kungiyar ta ECOWAS din ke gudanar da wani taro, jim kadan bayan kamala taron majalisar dinkin duniya da aka gudanar a birnin New York na Amurka.

    Tun a watan Satumban 2021 ne dai sojojin suka kwace Mulkin kasar daga hannun Alpha Condé, wanda ke mulkin kasar tun shekarar 2010.

  9. Mutum biyar sun nutse a ruwa a kokarin tsere wa ƴan bindiga a Abuja

    Bandits

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu mutum biyar sun rasa rayukansu yayin da suke kokarin tsere wa masu garkuwa da mutane a kauyen Chakumi na karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

    Cikin wadanda suka rasa rayukan nasu akwai maza biyu da mata uku, a wannan kauye da ke daura da kauyen Daku na karamar hukumar Gwagwalada.

    Tabarbarewar matsalar tsaro ta kai ga wasu mazauna kauyukan da ke kananan hukumomin Abaji da Gwagwalada na yin kaura, suna barin gonakinsu babu masu kula da su.

    Kamar dai yadda suka saba a wannan lokaci na damina, mutanen kauyen Chakumi da ke karamar hukumar Abaji ta babban birnin Najeriya Abuja, sun fita zuwa gonakinsu da sanyin safiyar ranar Laraba.

    Sai dai bayan sun isa gonakin, sun hango masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai, lamarin da ya tilasta musu komawa gida.

    Amma duk da sun koma gida - ba su tsira ba, domin masu garkuwa da mutanen sun bisu har kauyen nasu.

    Cikin wadanda wannan al'amari ya rutsa da su akwai wata matar aure, baya ga wasu mutum biyu.

    Abubakar Abdullahi, wanda tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji ne, ya shaida wa BBC cewa 'yan uwansa biyu sun halaka a sanadiyyar kokarin tserewa masu garkuwa da mutanen.

    Kuma Mallam Abdullahi ya shaida min cewa duk da kusancinsu da babban birnin tarayyar Najeriya, babu wani dauki da suka samu daga hukumimin birnin ko kuma jami'an tsaro.

    Ya kuma ce har zuwa yau da rana ba a ga gawar wadanda ruwan kogin Gurara ya ci ba.

    DSP Josephine Adeh, kakakin rundunar 'yan sanda na babban birnin tarayya Abuja ta ce ba ta da cikakken bayani game da wanann harin da masu garkuwa suka kai, amma ta ce za ta bincika kuma za ta sanar da BBC abin da ta gano daga baya.

    Matsalar tsaro a wannan yankin da ke kusa da kan iyakar Abuja da JIhar Kogi da kuma karamar hukumar Gwagawalada na kara tabarbarewa, har ya kai ga mazauna kauyukan na yin kaura zuwa wasu yankunan, inda manoma suka bar gonakinsu babu mai kulawa da su.

  10. Mutum 17 sun mutu a zanga-zangar adawa da hijabi a Iran

    Iran Women

    Asalin hoton, Getty Images

    Zanga-zangar da ake yi a Iran ta fantsama zuwa birane fiye da takwas da kuma wasu garuruwa a yayin da aka shiga rana ta shida da fara ta, bayan mutuwar wata matashiya a wajen 'yan sanda a lokacin da take tsare.

    Kafar talbijin din kasar ta ce mutum 17 sun mutu ciki har da jami'an tsaro uku ne suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar.

    A Mashhad, birni mai tsarki a Iran din, wata mata ta tsaya gaban motar 'yan sanda tana ihu tana cewa ba ma son Jamhuriyyar Musulunci.

    Rundunar juyin juya halin kasar ta yi kira ga ma'aikatar shari'a a kan ta hukunta duk masu yaɗa jita-jitar karya, sannan kuma mahukunta na kokarin rufe intanet a kasar.

    Matashiyar Mahsa Amini mai kimanin shekara 22 a duniya, ta mutu ne a ranar Juma'a, kwanaki uku bayan an tsare ta a kan rashin sanya dankali yadda ya dace.

  11. An gano wani mutum a raye kwanaki 17 bayan girgizar kasa a China

    China

    Asalin hoton, Getty Images

    An ceto wani mutum a raye, kwanaki 17 bayan girgizar kasa a China.

    A ranar 5 ga watan Satumba ne aka samu girgizar kasa a gundumar Sichuan, da ta kashe mutum 93 tare da jikkata wasu 400.

    Gan Yu na kokarin ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su ne, a lokacin da ya makale a wata tashar wutar lantarki.

    Gidan rediyon China na China National Radio ya ruwaito cewa, Mr Yu ya bace hanya ne bayan ya gama taimaka wa abokan aikinsa da suka samu rauni, kasancewar ya rasa gilashin idonsa da ke taimaka masa gane inda hanya take.

    Wani manomi ne da ke aiki da masu aikin ceto ya jiyo kukan Gan Yu a karkashin itace.

    Daga nan ne aka samu nasarar fito dashi aka kuma garzaya da shi asibiti, inda aka yi masa dauri a kariyar da ya samu.

  12. Cutar Ebola na kara bazuwa a Uganda

    .

    Asalin hoton, AFP

    Ma'aikatar lafiya a Uganda ta tabbatar da samun karin mutum shida da suka harbu da cutar Ebola.

    A farkon mako ne aka sanar da barkewar annobar a kasar.

    Sabbin alkaluman sun fito ne daga gundumar Mubende, inda aka tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 24 ranar Talata, bayan ya nuna alamun kamuwa da cutar.

    Wannan ne karo na uku da aka bayyana barkewar annobar Ebolar, nau'in Sudan.

    Ana kuma kan bibiyar sama da mutum 40 da suka yi hulda da mutanen, inda tuni aka killace wasunsu.

    Kazalika makwabtan kasashe sun ce suna ankare da lamarin akan iyakokinsu.

    Sai dai masana sun ce nau'in Sudan na cutar ba shi da hadari sosai ta fuskar yaduwa da kuma kisa, idan aka kwatanta da na Zaire.

    Hukumomin Uganda na ci gaba da bai wa yan kasar da ma duniya baki daya tabbacin shawo kan cutar ta Ebola.

  13. Za a rage sadaki da kudin da ake kashewa wurin biki a China

    China

    Gwamnatin China ta kaddamar da wani gangami na rage yawan kudin da ake kashewa a yayin biki da kuma rage sadaki.

    Gwamnatin ta yi hakan ne a wani bangare na yunkurin dakatar da raguwar da ake samu a yawan masu aure abin da kuma ya janyo raguwar haihuwa.

    Kungiyoyi da dama ne suka shiga gangamin, da nufin janyo hankalin mutane a kan rage almubazzaranci yayin biki.

    Gwamnatin ta ce idan an rage yawan kudin da ake kashewa a lokacin biki za a samu karuwar masu yin aure a kasar.

    To sai dai kuma masu sharhi sun ce da wuya wannan yunkuri ya yi tasiri, saboda raguwar da al'ummar kasar ke yi ya sa mutane kalilan ne zasu kai shekarun aure.

  14. An kama farfesar da ta ci zarafin 'yar sanda a Abuja

    Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya yi tir da cin zarafin wata 'yar sanda da uwargidanta ta yi.

    An zargi Farfesa Zainab Duke Abiola da cin zarafin sifeta Teju Moses, saboda ta ki amincewa ta yi mata ayyukan da ba su shafi wadanda aka dauke ta aiki ta yi ba daga hukumar 'yan sanda.

    Teju na aiki ne da Farfesa Zainab, wadda ma'aikaciyar shari'a ce kuma mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya, a matsayin odali.

    Kuma lamarin ya faru ne a gidan Farfesar da ke anguwar Garki da ke Abuja ranar 20 ga watan Satumba.

    Yanzu haka Farfesa Zainab da wasu yaran gidanta da ake zargi da hannu a cin zarafin na hannun rundunar 'yan sanda inda ake ci gaba da bincike.

    Kazalika IGP Usman Alkali ya umurci a janye duka yan sandan da ke aiki da Farfesar.

    Ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda matar da ke ikirarin kare hakkin bil adama za ta ci zarafin wani mutum, musamman wadda aka nada don ta ba ta kariya.

    Kwanan nan ne rundunar yan sandan Najeriyar ta ba da sanarwar daukar matakin doka, ga duk wanda ya ci zarafin dan sanda ta ko wace siga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Ba mu taba sayar wa da Rasha makamai ba- Kim Jong-un

    Kim Jong un

    Asalin hoton, Reuters

    Koriya ta Arewa ta ce bata taba sayar wa da Rasha makamai ba, kuma ba tada shirin yin haka a nan gaba.

    Gwamnati a Pyonyang na martani ne ga zargin Amurka na cewa Rasha na mayar da hankali ne Koriya ta Arewa wurin sayen makamai.

    Pyonyang kuma a martanin ta zargi Amurka da ire-irenta da yada jita-jita ''don cimma farfagandar siyasa da ta sojinta''.

    A farkon watan Satumba ne ofishin harkokin wajen Amurka ya zargi Koriya ta Arewa da amincewa ta sayar wa Rasha makamai, da suka hada da rokoki da sauran makamai masu linzami.

    To amma ta ce ba bu shaidar cewa za a yi amfani da su ne a yakin Ukraine.

  16. 'Yan damfarar intanet sun sace sama da N500m daga asusun wani mutum a Najeriya

    Internet Fraud

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu da ake zargin cewa masu damfara ne ta intanet sun wawushe naira miliyan 523,337,100, daga asusun wani kwastoma, zuwa asusuna daban-daban har goma 18.

    Mai magana da yawun sashe na musamman kan ayyukan damfara na rundunar 'yan sanda a jihar Legas, SP Eyitayo Johnson, ya ce daga baya 'yan damfarar na intanet sun aike da kudin zuwa sama da asussa 200 a bankuna daban daban.

    Ya kuma kara da cewa sun yi hakan ne tsakanin ranakun 23 ga watan Afrilu zuwa 25 ga watan na Afrilu, kuma tuni sun kama mutum biyu da suke tuhuma da hannu a mummunan aikin.

    Kawo yanzu an iya kwato sama da naira miliyan 160, yayin da ake ci gaba da neman mambobin wannan kungiya.

    SP Eyitayo ya ce za su gurfanar da wadanda suka fara shiga hannu gaban kotu da zarar sun kammala nasu binciken.

  17. Fasto ya amsa laifin kisan ma'aikaciyar lafiya a Ghana

    Georgina

    Asalin hoton, Girlfriendmorrison

    An kama wani fasto bayan ya amsa cewa yana da hannu a kisan wata daliba da ke karatun nas a tsakiyar Ghana.

    Georgina Asor Botchwey, mai shekaru 22, ta bata ne a makon jiya kuma daga bisani an gano gawarta a wurin da aka binne ta.

    An gano gawar Georgina ne a gidan wani hakimi da aka kira Nana Clarke a Mankessim, ta hanyar faston da aka kama.

    Kazalika an gano jaka da takalmi da sauran kayayyakin matashiyar a gidan.

    Yanzu haka jami'an tsaro na neman hakimin ruwa a jallo.

  18. Zan tabbatar an gudanar da sahihin zabe a 2023 - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, OTHER

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nanata kudurinsa na tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a kasar a 2023.

    Shugaban ya fadi hakan ne a jawabin bankwana da ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi birnin New York na Amurka.

    ''A matsayina na Shugaba, daya daga cikin tarihin da nake son bari shi ne na ga cewa an gudanar da sahihi kuma tsabtataccen zabe. Ta hakan ne 'yan Najeriya za su zabi shugabannin da suke so,'' in ji Buhari.

    Ya kara da cewa wanda duk zai gaje shi zai gudanar da jawabi a madadin Najeriya a taron majalisar na gaba.

    ''A yanzu muna shirin gudanar da babban zabe a Najeriya a watan Fabrairun badi. Saboda haka a taron Majalisar Dinkin Duniya na 78, za ku ga sabuwar fuska ne a kan wannan munbari'', a cewar Shugaba Buhari.

    Ya kuma yi magana a kan rawar da kasarsa ta taka wurin ganin an mika mulki salun alun a wata gwamnatin dimokradiyya a Gambia.

    Shugaban zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu a watan Mayun badi, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnati.

  19. Bidiyon yadda mata suke kona hijabansu don bijire wa 'yan Hisbah a Iran

    Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda mata suke kona hijabansu don bijire wa 'yan Hisbah a Iran

    Mutuwar Mahsa Amini a hannun 'yan hisba Iran ta janyo zanga-zanga a fadin kasar.

    'Yan Hisbah sun kama matashiyar mai shekara 24 saboda ba ta sanya kallabinta yadda ya kamata ba.

    Sai dai mutuwar tata ta janwo kakkausan suka daga wasu 'yan kasar.

  20. Ya zama dole a hukunta Rasha kan barnar da ta yi a Ukraine - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce dole Rasha ta fuskanci hukunci kan mamayar da ta yi wa Ukraine.

    Shugaban ya yi kiran ne a jawabin da ya gabatar ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a birnin New York.

    Ya bukaci a kafa kotun hukunta laifukan yaki ta musamman domin hukunta Rasha, da kuma biyansu diyya kan irin asarar da ta haddasa a Ukraine.

    Mista Zelensky ya ce akwai kuma bukatar a tsaurara takunkumai kan daidaikun mutane, lura da cewa suna tsoron rasa dukiyarsu.

    Yakin Ukraine ya sake mamaye manyan batutuwa da aka rika tafka muhawara kan a taron.

    Firaministar Birtaniya, Liz Truss, ta yi alkawarin ci gaba da bai wa Ukraine taimakon soji har sai yadda hali ya yi.