Raka gawar Sarauniya ya tuna min da mutuwar mahaifiyata Diana - Yarima William

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Bappa

  1. Rufewa

    Masu bibiyar mu a wannan shafi a nan muka kawo muku karshen labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da suka faru a yau a fadin duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, sunana Aisha Shariff Baffa, nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dakarun Rasha su fice daga tashar nukiliya ta Zaporizhia a Ukraine

    Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci dakarun Rasha da su fice daga tashar nukiliya ta Zaporizhia da ke kasar Ukraine.

    Hukumar ta bukaci hakan ne yayin wani taron shugabannin gudanarwa da ta yi, inda ta kwatanta hare-haren da Rasha ke kai wa tashar a matsayin abin da ba za a lamunta ba.

    Ana kuma nuna damuwa cewa za a iya samun hadari a tashar nukiliyar saboda luguden wuta da dakarun Rasha ke yi ba kakkautawa - duk da cewa Rashan ta na dora alhakin faruwar hakan a kan Ukraine.

    Olena Pareniuk, wata mai bincike kan makamashin nukiliya a wata jami'ar kasar Ukraine ta ce hakika Ukraine na son a kaucewa barazana ta hadarin nukiliya a kasar ta, da son kare tashar nukiliya ta Zaporizhia da kuma fatan dakarun Rasha za su fice daga tashar.

    An rufe tashar nukiliyar a yanzu saboda lalata turakan da ke bata hasken lantarki.

  3. An fitar da bayanai kan yadda za a yi jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II

    Sarauniya Elizabeth ta II
    Bayanan hoto, Sarauniya Elizabeth ta II

    Jami'an masarautar Burtaniya sun fitar da bayanai kan jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II, inda suka sanar da cewa za a yi taron addu'o'i a dakin taro na Wesminster da ke birnin Landan kafin daga bisani a binneta a fadar Windsor.

    Mutane kuma na ci gaba da bin dogayen layuka domin ganin gawar Sarauniya Elizabeth a karo na karshe, inda ake sa ran halartar shugabannin kasashen duniya daban-daban.

    Sojojin ruwa na Birtaniya ne za su ja keken da ke dauke da akwatin gawar Sarauniya Elizabeth ta II cikin titunan birnin.

    Sarki Charles na III da 'yan uwansa za su gudanar da taron addu'o'i a majalisar dokokin kasar a gobe Juma'a.

  4. 'Yan Kasashen waje 286 sun samu takarkar shaidar zama 'yan Nakeriya

    Muhammadu Buhari
    Bayanan hoto, Muhammadu Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba wa wasu 'yan kasashe waje 286 takardar shaidar zama 'yan kasa.

    Shugaban ya bukace su da su kasance 'yan kasa nagari.

    A yayin da yake mika musu takardar, ya ce" Kun sadaukar da kawunanku ga Najeriya a lokacin da kuka nuna soyayyarku da biyayyarku ga Najeriyar, a yanzu ita ma za ta saka musu."

    Shugaban ya yi bayanin cewa daga cikin mutum 286 da aka ba wa takardar shaidar zama 'yan kasar, 208 daga cikinsu sun karbi takardar da ke nuna cewa daya daga cikin iyayensu ne dan kasar shi ya sa suka zama 'yan kasa, yayin da 78 kuma aka yi musu rijistar zama 'yan kasa.

    Shugaba Buhari, ya bukace su da su rika bayar da gudunmuwa mai kyau ta yadda za a samu ci gaba a kasar, ya ce a matsayinsu na 'yan kasa dole ne su kiyaye da dokokin kasar.

  5. 'Yan bindiga sun kai hari Batagawara a jihar Katsina in da suka sace mutane fiye da 50

    'Yan bindiga
    Bayanan hoto, 'Yan bindiga

    Mazauna kauyen Bakiyawa cikin yankin Batagarawa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, sun ce suna cikin fargaba da rashin tabbas bayan 'yan fashin daji sun kai musu hari a jiya, al’amarin da ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da sace wasu fiye da 50.

    ‘Yan sanda sun ce sun aika da karin jami‘an tsaro yankin don bukutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

    Wani shaida daga garin na Bakiyawa, ya ce maharan sun je garin ne a kan Babura in da suka aikata wannan aika-aika.

    Ya ce maharan sun yi ta barin wuta a iska inda suka rika bi gida-gida suna daukar mutane.

    Shi kuwa wani mutum a garin ya shaida wa BBC cewa, ‘yan bindigar sun yi kokarin shiga gidansa amma ba su yi nasara ba, inda ya kara da cewa suna dauke da miyagun makaman da ‘yan sa kai baza su iya tunkararsu ba.

    Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, ya tabbatar da kai wannan hari a kauyen na Bakiyawa da ke karamar hukumar Batagarawa, Inda yace sun yi arangama da ‘yan fashin dajin sosai.

    Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai, na ci gaba da fama da hare-haren 'yan fashin daji duk da matakan murkushe su da hukumomi ke cewa suna ɗauka, al’amarin da ya jefa dumbin jama’a cikin halin kakanakayi.

  6. An kama mutum biyu da laifin luwaɗi a birnin Riyadh na Saudiyya

    The Public Prosecution.

    Asalin hoton, Saudi Gazette

    An kama mutum biyu da laifin tursasawa wani yin luwadi a birnin Riyadh na kasar Saudi Arabiya.

    Jami'an tsaron sun ce sun kama mutanen ne wadanda 'yan kasar ne da ake zargi da tursasawa wani mutum yin luwadin ta karfin tsiya.

    Tuni aka kama mutanen sannan an fara bincike don gano ainihin abin da ya faru.

    Mai magana da yawun jami'an tsaron, ya ce mutanen biyu sun hadu da mutumin ne ta hanyar kafar sada zumunta, sannan a hankali suka rinka tursasa masa yin luwadi da su.

    Rahotanni sun ce a yanzu an tsare mutanen kafin kammala bincike.

    Idan har aka tabbatar da laifin na su, to hukuncin da kotu ke yankewa masu irin aikata wannan laifin a kasar shi ne hukuncin kisa.

  7. Raka gawar Sarauniya ya tuna min da mutuwar mahaifiyata Diana - Yarima William

    Yarima William

    Asalin hoton, OTHER

    Bayanan hoto, Yarima William

    Yarima William ya shaida wa masu zaman makoki a wajen Fadar Sandringham cewa tafiyar da yake yi a bayan akwatin gawar Sarauniya Elizabeth a wani tattaki a jiya, ya tuna masa da mutuwar mahaifiyarsa.

    Tun da farko da yake magana da masu masa fatan alkhairi a wajen gidan masarautar, ya ce abin da ya faru a jiya abu ne mai matukar wahala.

    A watan Satumbar 1997 ne, shi da dan uwansa Harry, suka yi irin wannan tattakin a bayan akwatin gawar mahaifiyarsu Gimbiya Diana, abin da har yanzu ya zauna masa a ransa ya kasa mantawa.

    A 2017, Yarima Harry, ya gaya wa jaridar Newsweek cewa, "Ba na zaton akwai yaron da za a ce ya yi haka a kowanne irin yanayi kuwa, ba na jin hakan zai faru a yau."

  8. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum fiye da 130 cikin wata biyu a Nijar

    Ambaliyar ruwa
    Bayanan hoto, Ambaliyar ruwa

    Mahukunta a Jamhuriyar Nijar, sun ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum fiye da 130 a kasar tun daga watan Yulin shekarar da muke ciki.

    Nijar dai na fuskantar ambaliyar ruwa a duk shekara, to amma a bana adadin ya rubanya na bara.

    Kazalika ambaliyar ruwan ta kuma kashe dabbobi da dama da kuma lalata gonaki.

    Ministan ayyukan jin kai na kasar, Lawan Magaji, ya ce yankunan Maradi da Zinder da kuma Diffa ne ambaliyar ta fi shafa.

    Haka kuma ambaliyar ruwan ta tursasa wa mutane fiye da 150 barin muhallansu a wadannan yankunan.

    Ambaliyar ruwan bana dai ta shafi kasashen yammacin Afirka da dama ciki har da Najeriya.

  9. Ana ce-ce-ku-ce kan yi wa kananan yara uku fyade da kashe su a Indiya

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ta cece-ku-ce kan yadda ake yi wa wasu kananan yara mata fyade tare da kashe su a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya.

    Lamarin ya haifar da zanga-zanga, inda mazauna garin ke neman a yi wa matan adalci.

    'Yan sanda sun ce sun kama mutum shida da ke da hannu a lamarin.

  10. Jami'an Masarautar Birtaniya sun fitar bayanai kan jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II

    Queen

    Asalin hoton, PA Media

    Jami'an Masarautar Birtaniya sun fitar bayanai kan jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II, inda suka sanar da cewa za a yi taron addu'o'i a dakin taro na Wesminster Abbey da ke birnin Landan kafin daga bisani a binne ta a Fadar Windsor.

    Mutane kuma na ci gaba da shiga dogayen layuka domin ganin gawar Sarauniya Elizabeth a karo na karshe.

    Ana sa ran dubban mutane ne za su kalli gawar Sarauniyar yayin da aka ajiye ta a dakin taro na Wesminster da ke majalisar dokokin Birtaniya.

    Za a yi mata jana'izar ban girma ta kasa baki daya a ranar Litinin.

    Sarki Charles na III na wata ziyara ta kwana daya a gidansa da ke kudancin Ingila, bayan daukar tsawon kwanaki yana ayyuka a bainar jama'a a matsayinsa na sabon sarki.

  11. An yanke wa mutum biyu hukuncin daurin shekara 50 a Saudiyya

    .

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Bayanan hoto, .

    Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam a Saudiyya sun ce wata kotun hukunta manyan laifuka a kasar ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekarar 50 a gidan yari saboda kin ficewa daga yankin da za a yi aikin gina wani katafaren birnin mai cike da fasahar zamani na duniya wanda ake yi wa lakabi da Neom project.

    Aikin na Neom project dai wani gagarumnin aiki ne da zai lakume kusan dala biliyan 500 da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ke jagoranta.

    Masu gwagwarmaya sun ce an yanke wa mutanen biyu Abd -al-Ilah al-Huwaiti da Abdullah Dakheel al-Huwaiti - wadanda 'yan uwan juna ne - hukuncin ne saboda bayar da goyon baya ga 'yan uwansu wadanda suka ki yarda su fice daga yankin.

    An kuma haramta musu tafiye-tafiye na tsawon shekara 50

    An dai ruwaito cewa mutanen biyu 'yan uwa ne ga Abd-al-Raheem al-Huwaiti, wanda jami'an tsaron kasar suka kashe saboda kin yadda ya fice daga yankin a shekarar 2020

  12. Shugaban Rwanda ya yi wa Sarki Charles lll ta'aziyya ta waya

    .
    Bayanan hoto, .

    Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya ce ya kira Sarki Charles lll na Birtaniya ta waya domin yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita shugaba Kagame ya ce ''Na samu damar kiran Sarki Charles lll a waya, domin yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa mai martaba Sarauniya Elizabeth ll''

    Ya kara da cewa ''Kasar Rwanda za ta yi aiki hannun-da-hannu tare da Sarki Charles lll domin ciyar da manufofin kungiyar Commonwealth gaba wajen yi wa al'umar kasarmu aiki''

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A watan Yunin da ya gabata ne dai shugaba Kagame ya karbi bakuncin Sarki Charles lll a taron shugabannin Kungiyar kasashe Rainon Ingila ta Commonwealth.

  13. Peter Obi ya ziyarci Goodluck Jonathan

    .

    Asalin hoton, twiter/ Peter Obi

    Bayanan hoto, .

    Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar Labour Peter Obi ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce ya ziyarci tsohon shugaban ne domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaba kasa.

    A shekarar 2015 ne dai Goodluck Jonathan ya sha kaye a zaben shugaban kasar a karkashin jam'iyyar PDP

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a Benue

    .

    Asalin hoton, others

    Bayanan hoto, .

    Ambaliyar ruwa ta janyo hasarar gidaje sama da 200 a Makurdi babban birnin jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wato SEMA, Dakta Emmanuel Shior na bayyana haka a yayin raba kayan tallafi ga wadanda lamarin ya raba da muhallansu a birnin makurdi

    Mista Shior ya ce wannan shi ne bala'in ambaliya ma fi muni da jihar ta taba fuskanta

    Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa jihar kan wannan hali da ta shiga.

  15. Sama da baki 2000 ne za su halarci jana'izar Sarauniya

    .

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, .

    Sama da baki 2000 ne daga kasashe daban-daban a fadin duniya, ake sa ran za su halarci jana'izar Sarauniyar Ingila Elizabeth ll, a yayin da za a yi shiru na minti biyu lokacin jana'izar.

    A yanzu dai an bude kofofin dakin taro na Westminster Abbey a shirye-shiryen jana'izar da za a gudanar ranar Litinin 19 ga watan Satumba.

  16. Kotu ta umarci INEC ta amince da Akpabio a matsayin dan takarar sanata a APC

    .

    Asalin hoton, Godswill Akpabio/facebook

    Bayanan hoto, .

    Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja babbar birnin Najeriya ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar da ta amince tare da wallafa sunan Godswill Akpabio a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltar yankin Akwa Ibom ta arewa maso yamma a karkashin jam'iyyar APC.

    Jam'iyyar APC dai ta wallafa sunayen Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da tsohon ministan Niger Delta Godswill Akpabio, da kuma gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, a matsayin 'yan takarar majalisar dattawa a karkashin jam'iyyar

    To sai dai hukumar zaben kasar ta cire sunayensu daga cikin jerin sunayen 'yan takara da ta wallafa

  17. Harin makami mai linzami ya fada dab da garin su Zelensky

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Madatsar ruwan da ta haddasa ambaliyar

    Wani harin makami mai linzami da Rasha ta harba ya fada kan wata madatsar ruwa da ke kusa da birnin Kryvyi Rih a kudancin kasar Ukraine.

    Shugaban yankin ya ce tuni suka bayar da umarni ga mazauna yankin da su fice daga gidajensu, a yayin da ya ce ana kokarin shawo kan matsalar.

    Ukraine ta ce harin wani martani ne da Rasha ta yi game da sabbin hare-hare da Ukraine din ke kaddamarwa a 'yan kwanakin nan.

    Shugaban kasar Volodymyr Zelensky - wanda haifaffen birnin ne - ya bayyana Rasha a matsayin 'kasar 'yan ta'adda' bayan harin kan madatsar ruwan Karachunivske.

    Harin ya shafi hanyoyin samar da ruwan sha ga mazauna birnin fiye da 600,000.

    Jami'ai sun ce ruwan ya fasa madatsar abin da ya janyo ambaliya tare da cinye wasu gidaje da dama a yankin

    Kawo yanzu dai Rasha ba ta ce komai ba game da wannan hari.

  18. ICPC ta bankado almundanar naira biliyan 2.8 na ayyukan mazabu cikin shekara uku

    .

    Asalin hoton, Website/ICPC

    Bayanan hoto, .

    Hukumar da ke yaki da cin hanci da almundahanar kudade ta ICPC a Najeriya ta ce ta gano ayyukan mazabu da aka karkatar a fadin kasar da kudinsu ya kai Naira biliyan 2.8

    Hukumar ta ce ta gano hakan ne ta hanyar wani kwamiti da ta kafa don bin diddigin ayyukan mazabu a fadin kasar.

    Wanda ya gano ayyukan mazabu kusan 2,444 da aka karkatar da kudinsu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.

    Yayin da yake yake gabatar da takaitaccen kundin binciken hukumar a birnin Legas, daraktan gudanarwa na hukumar Akeem Lawal, ya ce a karon farko an gano ayyukan mazabu 524 a jihohi 12 da babban birnin tarayya a shekarar 2019.

    Sannan kuma a karo na biyu, kwamitin bin diddigin ya gano ayyukan mazabu 822 a jihohi 16 a shekarar 2020,

    Haka kuma a karo na uku na bin diddigin an zakulo ayyukan mazabu 1,098 a jihohi 17 hade da Abuja babban birnin kasar.

  19. Man fetur a Kenya ya yi tashin gwauron zabi bayan cire tallafi

    Kenya ta cire wani bangare na tallafin man fetur

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Kenya ta cire wani bangare na tallafin man fetur

    Farashin man fetur ya kai matsayin da bai taba kai wa ba a kasar Kenya bayan da kasar ta fara aiwatar da matakin cire masa tallafi.

    A ranar Laraba hukumar kula da makashin kasar ta ce ta cire tallafi a kan man fetur, yayin da za ta ci gaba da bayar da karamin tallafi kan gas da kalanzir

    A yanzu farashin litar man fetur a kasar ya kai Shilin 179, a maimakon shilin 160 da ake sayar da shi a baya.

    Matakin na zuwa ne bayan da sabon shugaban kasar William Ruto a jawabin rantsuwar kama aikinsa, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cire tallafin mai da na kayan abinci a kasar.

    To sai dai akwai fargaba game da cewa cire tallafin kacokan zai haifar wa da tattalin arzikin kasar koma baya, yayin da farashin man fetur din zai shafi tsadar rayuwa kai tseye.

  20. Armeniya ta ce dakarunta 105 ne suka rasa rayukansu a yakin da ake yi a kan iyakar Azerbaijan

    Firaministan Armeniya Nikol Pashinyan ya ce fiye da sojojin kasar 100 ne aka kashe a rigingimun kan iyaka da Azerbaijan da ya barke tun ranar Litinin.

    A nata bangaren kasar Azerbaijan ta ce dakarunta 50 ne suka rasa rayukansa a sanadiyyar rikicin da kasashen biyu ke dora alhakinsa a kan juna.

    Yayin da yake jawabi ga majalisar dokokin kasar Mista Nikol Pashinyan ya ce dakarun kasar 105 ne suka rasa rayukansu tun ranar Litinin da daddare a wasu hare-hare da dora alhakinsu kan kasar Azerbaijan.

    Tuni dai kasashen Rasha da Amurka suka yi kira ga kasashen biyu da su tsagaita wuta.